BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

             Gefe ɗaya kuma Usman shima ya koma aikin sa, sai dai be taɓa neman Ɗahira domin ya ganta ba, tunda sosai zuciyar sa ke addabar shi da son ganin ta, ba kaɗan ba tunanin ta ya gallabi ruhin sa, tun yana ganin abin da sauƙi, har kuma dai ya kasa jure wa yau ya yanke shawaran zuwa Office ɗin ta ya same ta, ko da ganin waɗannan idanuwan nata ne masu firgitar dashi domin yaji sanyi a ranshi, a lokacin da yake tunanin yana zaune ne a Office ɗin sa yana ta faman murmusawa. Sai kuma ya tashi ya fito ya nufi Office ɗin ta

Nocking yayi

Sai ta ba shi iznin shiga

Ya buɗe ya shiga yana bin ta da kallo

Ɗahira da kanta ke kan files tana duba wa, ƙamshin turaren sa kawai ya ziyarci hancin ta sai taji wani muguwar faɗuwar gaba ta ziyarce ta, da sauri ta ɗago don tabbatar da shi ɗin ne wanda take hasashe

Ilai kuwa shi ne yana tsaye a bakin ƙofan, shi be shigo ba kuma be fita ba idanun shi a kanta

Sai ta ɗauke idanun ta tana jin zuciyarta na ci gaba da bugawan sauri kamar zata faso ƙirjin ta, take a nan yanayin jikin ta ya sauya lokaci ɗaya taji yayi mugun sanyi har tana jin yanda hannayen ta suka soma rawa

“I want to talk to you”. Yayi maganar har yanzu yana tsaye a bakin ƙofan be ɗauke ido a kanta ba

Bata motsa ba bare ta sake kallon sa, illa ɗaure fuskar ta da tayi tana me jin baƙin cikin sa da tsanar sa me girma a zuciya

Takowa kawai yayi ya zauna ganin bata kula shi ba, sai da kamar soconni uku suka shuɗe kafin ya buɗi baki yace, “wani alfarma nazo nema wajen ki, na san zaki yi mamaki sosai but ki ɗauka tamkar zan yi hakan ne domin faranta ran iyayen mu, ki amince muci gaba da zama a matsayin mata da miji domin yiwa iyayen mu biyayya kamar yanda suka so tun Farko..”

Be ƙare maganar ba ta ɗago tana kallon sa da idanuwan ta da suka cika fal da hawaye, cikin rawan murya da za’a gane ƙiris take jira ta saki kuka, ba wai don komi ba sai don ƙuncin da kalaman sa suka saka ta, tace dashi, “kai har kana da bakin da zaka zo waje na kace in koma ɗakin ka domin muyi wa iyayen mu biyayya? Kar ka manta tsanar da nake maka ya zarce tunanin ka, kai ka koya min tun ban san kaina ba. har gobe bazan taɓa manta azaba da wahalan da ka bani ba, idanun ka sun rufe saboda tsantsan tsanar da kake min, ka manta cewa Ni ƙanwar ka ce kuma jinin ka, ka gallaza min uƙuban da na gummaci mutuwa ta da rayuwa ta, taya ya kake tunanin zan iya yafe wa har in koma in Yi rayuwar aure da kai? Never wlh. Har abada bazan taɓa manta abinda kayi min ba, yana nan daram a cikin zuciya ta wanda kullum ƙara jin tsanar ka nake yi a cikin ta, I hate you Usman I will never go back to your house .. “

Tsawa ya daka mata saboda jin maganganun ta da suke ƙona masa zuciya da ya kasa jure wa. Sai kawai yaga ta fashe mishi da dariya ga kuma hawaye suna ɗiga a fuskar ta, sai ya saki baki yana kallon ta cike da mamakin ta

Ido cikin ido take kallon sa bayan ta tsayar da dariyan nata lokaci ɗaya tace, “Hi Guy gate out of my office baza ka zo kayi min iko a nan ba”.

“Ni kike kora?”

“Eh kai. WHO ARE YOU?”

A fusace ya tashi yana nuna ta da yatsa yace, “zan nuna miki kuwa Ni wane ne, kuma zan tabbatar miki da cewa baki isa kici galaba a kaina ba”. Sai ya saki guntun murmushi yace, “gida na ne dai baza ki koma ba har kike furta min munanan kalaman nan ko? To zan ga yanda zaki yi kiyi auren da igiyar aure na, muddin ba gida na kika koma ba baza ki taɓa aure ba wlh, sai dai ki mutu da aure na a kan ki babu wanda ya isa ya saka Ni na sake ki, ba wai don ina son ki ba sai dan in sauke miki wannan iskancin da yake kanki, dole ki koma gida na kuma dole ki amsa sunan mata ta”.

Fashe wa tayi da kuka cikin ƙunan zuciya tace, “wlh ƙarya kake yi mugu azzalumi, Ni ba matar ka bace, dole ne sai ka sake Ni”.

Dariya ya saki lokaci ɗaya saboda ganin yaci galaba da saka ta baƙin ciki kamar yadda ta saka shi

Lokaci ɗaya ta tsayar da kukan nata ganin dariya a fuskar sa wanda tunda take bata taɓa ganin shi yayi ko da murmushi ne ba. Sai gani kawai tayi ya zagayo ta gefen ta har yana ranƙwafo wa saitin kunnen ta

Yace, “Mata ta ce ke wlh, kuma dole sai kin amsa sunan nan, babu wanda ya isa ya raba aure na dake ko waye..”

Da sauri ta tashi saboda jin tsigan jikin ta ya tashi gaba ɗaya ta rasa sukunin ta, hakan yasa suka yi karo da juna kansu ya bugu, sai duk suka riƙe goshin suna kallon idanun junan su, nata idanun sun yi luhu-luhu suna zubar da hawaye kamar wanda aka kunna famfo.

Hannu ya saka ya…

kai na gaji mu haɗu next page sai ku ji ya za’a kaya. Amma ku bi Ni bashi zuwa jibi.
????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

        EPISODE Sixty One

       Hannu ya saka ya janyo ta jikin sa yana kallon ta

Wanda ita lokaci ɗaya ta rufe idanun ta jikin ta ya soma rawa ta soma ƙoƙarin ƙwace kanta

Murmushin mugunta ya saki yana sake manna ta a jikin sa, a hankali ya furta. “Na san baki manta abinda ya faru ba a ƙauyen Baba Jaure. So Kar ki tunzura Ni in sake maimaita wa wlh, ki kama kanki ba na son rashin kunya, ba wai na sauya bane daga hali na bane, sai dai na sassauto ne wanda Ni kaina ban san meyasa tsanar da nake miki na dena ji ba”. Sai yayi shiru yana saka hannun sa ya shafi fuskar ta yace, “kina burge Ni yanzu shiyasa. Ki kula”. Ya sake ta ya fice abin sa.

       Wani irin kuka me ƙara ta saki tana zame wa a ƙasan wajen jikin ta na ci gaba da rawa. “Allah ya isa tsakani na da kai Usman, ka gama dani wlh ka cuce Ni! bazan taɓa yafe maka ba mugu azzalumi kawai!”.

Kuka sosai take yi ta kasa tashi a wurin, ji take yi da zata iya da sai ta faffalla mishi mari ko zata samu sukunin ƙuncin da yake ƙunsa mata.

        Bata tashi a durƙushe a wurin ba sai da taji ana mata Nocking, a tunanin ta ko Usman ɗin ne ya sake dawowa shiyasa ta ɗauke kukan nata cak tana jiran shigowar sa tayi masa rashin mutunci, tana ga hakan kaɗai zai saka ya fita harkan ta, domin ta tsane shi ko kaɗan ba ta son ma wata magana ta sake shiga tsakanin su. But sai taji shiru ba’a shigo ba illa Nocking ɗin da aka ci gaba da yi, dole ta tashi tana share fuskar ta tare da daidaita nutsuwar ta, ta ba da iznin shigo wa tana zama a kan kujera

Ayush da Safra ne suka shigo Office ɗin idanun su a kan Ɗahira da itama ta ɗago rinannun idanuwan ta tana bin su da kallo

Kallo ɗaya da tayi musu ta gane Ayush, sai ta saki fuskan ta kaɗan tayi musu Bismillah

Zama suka yi suna murmushi duk kan su

Ayush tace, “na san baki gane Ni ba ko? Ni ce Dr. Ayush Abdulkarim friend ɗin Dr. Baffa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button