FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Sai da ya gama ƙare musu kallon wulaƙanci fuskar sa babu alamar rahama, sarai ya gane fuskar Ayush tunda ba yau ba ya rigada yayi making ɗin ta, kai komo ya riƙa yi yana sake bin su da kallo, sai da ya mula kafin yace, “wato ku ne sheɗanun da har ƙananan ƙwaƙwalan ku ya saka muku tunanin ku shiga gona ta ko?” Sai ya ci je baki yana saka hannayen sa cikin aljihun wandon sa kana yaci gaba da faɗin, “har kuna iya ɗaukar picture ɗin ƴar uwan ku mace ku yi mata wannan ƙazafin saboda cikan burin ku? To yau zan maida sharrin ya koma kanku, ku sani da kyau Ni Usman ba na yafiya ko misƙala zarratan ga ire-iren ku…” Sai ya datse haƙoran sa be ƙarisa abinda yake son faɗa ɗin ba, ɗan jan numfashi yayi kana ya kalli mutumin yace, “ka tuɓe kayan su gaba ɗaya ba na son ganin komi a jikin su, sannan ka ɗaukar min su hoto kowacce kuma da fuskar ta a ciki. Ko wacce sai na kaima uwarta ta gani, idan kuma babu me uwa a cikin ku na san kuna da uba da dangi…” Sai ya sake yin shiru yana bin su da kallo da idanun sa da suka soma canza kala. “Common kayi min abinda na sa ka ka tsaya kana kallo na, saura kaima zan dawo kanka”. Yayi maganar cikin tsawa
Da sauri jiki na rawa mutumin ya nufe su ya soma cire musu kayan
Ko waccen su na tsiyayar da hawaye kamar ƙasa ta tsage su shige ganin cin mutuncin da yau za’a musu. Har Ayush da zuciyar ta ke cike da ƙaunar Usman ɗin amma yau sai da taji dama bata san shi a rayuwar ta ba, da wani ido zata kalli dangin ta muddin abinda ya faɗa ɗin ya aikata musu? Wayyo.. wayyo kaico da wannan ranan a wurin su
Usman na wurin be jirga ba har aka gama cire musu kayan su kaf, kana ya miƙa wayan shi mutumin ya amsa ya soma ɗaukan su hotuna
Haka suke kuka amma babu halin roƙo sabida bakin su dake rufe
Sai da ya gama tass kafin ya amshi wayan shi ya tura wa mutumin a tashi wayan
Kallon shi yayi yace, “ka tabbatar kayi min aikin da na saka ka nan da gobe, ina son hotunan su fi na yarinyan muni haka nake son gani, kuma kayi zaman tsare su nan da kwana biyu kafin ka sake su, ko abinci ba na buƙatar ka basu illa ruwa, wannan aikin kawai zaka yi min na yafe maka, idan ba haka ba ka san sauran zancen…” Daga haka ya juya ya fice abin sa
Yana shiga motan shi yaja yayi gaba, agogon hannun sa ya duba yaga ƙarfe 09:20am. Ne, duk da yanzu ba time ɗin shiga Office ɗin sa bane, kuma yana da wurin da zai je amma yana buƙatar ya sanya Ɗahira a idanun sa, don haka can Hospital ɗin ya nufa. Yana yin parcking ya fito ya shige, kai tsaye Office ɗin ta ya wuce ba tare da yayi Nocking ba ya buɗe ya shige
Da sauri ta ɗago kanta tana zuba mishi idanun nan nata masu saka shi a wani mawuyacin hali
Ɗan lumshe nashi idanun yayi yana buɗe wa a kanta
A lokacin tuni ta ɗaure fuska tamau tana jiran taji me yazo mata a Office
Sai ya ɗan sosa kansa yana kawar da ƙwayan idanun sa a kanta, domin yanda ta kafe sa da kallo kamar zata haɗiye shi ɗanye, hakan yasa yaji gaba ɗaya natsuwar sa ya gushe wanda ya saukar masa da kasala nan take, ɗan ƙasa-ƙasa yake kallon ta cike da isa da sanyin murya can ƙasa yace, “ina son zamu yi magana ne Nafeesa, ki bani aron hankalin ki, na san…” Dole ya tsayar da maganar ganin ta tashi ta nufi Toilet zata shige, sai yayi saurin taka wa ya isa wajen ta, tana buɗe ƙofan caraf ya riƙe mata hannu
Lokaci ɗaya ta juyo tana kallon sa hawaye na cika mata ido, cike da haushin sa tace, “Please Yaya Usman ina ganin girman ka kar ka saka nayi maka abinda baka zata ba, wlh wlh idan har baka fita harka na nayi rayuwa ta Ni kaɗai ba duk abinda nayi maka kai kaja”.
Murmushi yayi memakon yaji haushi, sai ya sake riƙe mata hannun gam yana haɗa shi da nashi ta cikin yatsun ta, a hankali yace, “common Babe ba hayaniya ne ya kawo Ni wajen ki ba, neman sulhu ne… Kuma kin san an ce sulhu alkhairi… Anyway ki manta komi Nafeesa ki yafe min, haƙuri nazo baki dama ba wani abu ba, na san nayi miki ba dai-dai ba wanda yasa nake ta faɗan abubuwan da na san ba haka bane”. Sai yaja numfashi a hankali yana kallon fuskar ta sannan yace, “ki amince ki koma ɗaki na mu rufa wa junan mu asiri kinji?”
Hannun ta tayi ƙoƙarin janye wa amma yaƙi saki, cike da yanayin fusata a muryan ta tace, “to Ni na ce ba na ƙaunar ka! ba na ƙaunar zama da kai ko dole ne? Ko kana tunanin don ka san wace ce Ni a yanzu wani abun alfahari ne a wuri na? Da sanin ka da rashin sa duk ɗaya ne a wuri na. Usman bazan taɓa zama da kai ba domin na tsane ka fiye da yanda kake zato..”
Hannu ya saka ya rufe mata bakin ta sabida ya gaji da jin waɗannan munanan kalaman nata, sosai zuciyar sa ke tafarfasa da jin ɗaci a cikin ta wanda tuni har idanun sa sun soma yin ja suna ƙyallin ruwa
Hannu ta sanya zata janye nashi hannun
Sai kawai ya janyo ta ya haɗe bakin su wuri ɗaya
Lokaci ɗaya gaba ɗayan su suka ji su a wani irin yanayin da basu taɓa shigan shi ba, wanda har ita tsaban tsuma tuni jikin ta ya fara rawa, sai kuma tashin zuciya da nan da nan sai ga amai ta guntso shi ta bakin ta ya shige nashi
Ai sai yayi saurin sakin ta yana tare aman ba tare da ya shige can cikin shi ba
Ita kuma tuni ta shige Toilet ɗin da gudu ta dinga kwarara shi kamar zata amayar da kayan cikin ta
Da gudu yabi bayan ta ba tare da ya damu da abinda tayi masa ba, domin ko kaɗan be ji ƙazantan hakan ba, illa ma son duba halin da take ciki da yake yi. Da kallo kawai yake bin ta da ya shiga ciki yanda yaga tana kwarara aman sai duk tausayin ta ya shige sa, yana son taɓa ta amma kuma ya kasa ƙarisawa wajen ta
Sai da tayi har ta gama sannan ta samu ta kuskure bakin ta
Shima sai a lokacin ya samu ya isa wajen ta yana mata sannu
Bata ce komi ba ta juya zata fice da sauri
Sai da yaga fitar ta kafin shima ya samu ya wanke bakin shi, ya ɗauki tissue Yana goge hannun sa ya fice
Ashe tana bakin ƙofan ta kasa jirga wa saboda jirin dake son kwasan ta ƙasa
Yana buɗe ƙofan ta faɗo mishi a jiki. Yayi saurin tare ta yana tambayar ta. “Lafiya me ke damun ta?”
Wani kallo ta watsa mishi cike da baƙin cikin abinda yayi mata, kana ta janye jikin ta ta nufi table ɗin ta a hankali ta soma haɗa kayan ta cikin jaka, tana gama wa ta juya ta fice ta bar shi nan tsaye yana bin ta da kallo
Ya jima a Office ɗin be iya ko motsi ba, sai daga baya jiki a sanyaye ya fito ya rufe mata Office ɗin ya wuce nashi ranshi duk babu daɗi.
Kai tsaye gida ta wuce, tana shiga parlour’n su da sallama, babu kowa ciki, sai ta wuce ɗakin Maman ta
Lokacin tana sallah
Sai ta fito ta wuce ɗakin su, a kan gadon ta ta zauna tana me zame jakan ta daga kafaɗan ta, shiru tayi tana riƙe da kanta, gaba ɗaya ba ta jin daɗin jikin ta, musamman idan ta tuna abinda Usman yayi mata sai ta fara jin aman na taso mata, ga kuma jirin da take ji kaɗan-kaɗan. Tsaki taja kawai tana tashi ta wuce Toilet, wanka tayi kafin ta ɗaura alwala ta fito, sai ta shirya cikin riga da wando na Pakistan blue da ratsin ruwan goro, sallan azahar ta gabatar sannan ta tashi ta sake komawa ɗakin Maman
Aunty Amarya lokacin tana tsaye tana ninke sallayan ta amsa mata sallaman tare da gaisuwar da tayi mata, sannan itama tace, “har kin dawo haka da wuri yau?”
Zama tayi a kan kujeran ɗakin kana ta amsa ta da cewa, “eh Mama, ba na jin daɗin jiki na ne shiyasa”.