FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Kaka duk ya ɗaga musu hankali, abu kaɗan yace, “har yanzu Matata bata neme Ni ba?”.. “Shin matata ta kira kuwa? Ko kuma Fodio be kira ba?”.. ga shi a lokacin jikin sa duk ya ƙi daɗi, shiyasa suke dangana wa ga zafin ciwo ne, saboda yanda ya matuƙar damuwa akan “yana son jin halin da Ɗahira take ciki”
Babu yanda za su iya su Big Dady, sai dai kwantar masa da hankali da suke yi, suna ƙara ba sa haƙuri a kan “za su kira, ƙila wani abun ne ya dakatar da su”.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
TURKEY
Fitowar sa kenan daga ɗaki cikin shirin sa na kamar kullum, idanun sa akan ta suka faɗa, hakan yasa ya tsayar da saka link ɗin rigan sa da yake yi yana sake kallon ta, lokaci ɗaya sai ya ɗauke kai yana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki na shigan sa, tare da wani tashin zuciya na taso masa, sakamakon ganin ta cikin amai da yayi. Rasa me ma zai yi yayi, sai kuma ya taka ya nufe ta tamkar zai haɗiya zuciya ya mutu tsaban baƙin ciki, yana zuwa inda take ya sanya ƙafa ya tokare ta yana faɗin “Keeeee” cikin tsawa
Sai dai bata san ma yana yi ba, domin tuni ta sume ba ta ko numfashi
Ganin bata motsa ba, sai ya mayar da idanun sa kanta yana noƙe hanci har da saka hannu ya toshe hancin nasa, sake tokarin ta yayi, sai ya ga alamun ba ta numfashi, tsaki yaja me ƙarfi yana juya wa ya shiga Toilet ɗin parlour’n, ruwa ya ciko cikin bucket, yana fito wa ya sheƙa mata a jiki
Lokaci ɗaya ta kawo wani irin numfashi a matuƙar firgice tana kiran sunan Maman ta
Ƙafa ya saka ya taka nata ƙafan Yana murzawa
Wannan dalilin ne yasa ta dakata daga kiran sunan Maman ta da take yi; sakamakon zafin da ya ziyarce ta, nan ta buɗe idanun ta da suka gama rine wa suka yi wani irin kore tamkar dai ba na ɗan adam ba, saboda yanda ƙwayan idanun nata suka kasance ba baƙi ba, ta zuba masa su kamar zata cinye sa
Hakan yasa lokaci ɗaya tsoron da ya saba ji ya tsarga masa fiye da yanda yake ji a ko wani lokaci idan ya kalle ta, nan ya janye idon sa tare da ƙafan sa ƙirjin sa na faman dukan uku-uku
Ita kuwa kuka ta fashe da shi da ɗan sautin muryan ta da ya rage mata, sosai take kuka wanda ke fita a hankali yana yi yana ɗauke wa
While shi kuma yana jin kamar ana sake tsaga zuciyar sa ne ana ƙara masa wutar tsanar ta, kukan nata na shigan kunnen sa kamar wuta, yana sake jin wani tuƙuƙi a zuciyar sa tare da wani nauyi, ji yake yi tamkar idan be mata dukan tsiya ya ɗaiɗaita ta a lokacin ba, bazai samu sukunin zuciya ba, sai dai kuma ko kaɗan ba ya son sake kallon inda take, hakan yasa ya juya ya nufi ɗakin sa da sassarfa yana kame kansa da ya soma sara masa
Lumshe idanun ta tayi tana jin wani irin zafi dake ruruwa a ko ina na sassan jikin ta da zuciyar ta, yayinda take jin numfashin ta na son ɗauke wa, hakan yasa ta buɗe ido tare da ƙwalalo su waje tana sakin nishi da sauri da sauri, tamkar wacce tayi tseren gudu ko me athma, yanda take fizgar numfashin kamar zata shiɗe, lokaci ɗaya kuma ya fizge mata ta sake sume wa gauu…
****
Shi kuwa yana shiga ɗakin sa ya zauna bakin gado yana riƙe da kansa, abinda yake ji a zuciyar sa baki ma bazai iya misalta shi ba, gaba ɗaya ya yamutsa gashin kansa ya rasa sukuni, idanun sa kuwa duk sun yi jazur kamar an yi masa duka, lokaci ɗaya ya saki kan nasa ya miƙe a firgice ya nufi ƙofa zai fice…
babu yawa. Manage Please.
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
بسم الله الرحمن الرحيم
⚖
FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
JIKAR LAWALI CE✍️
Wattapad: UmmuDahirah????
\F.W.A????/
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY
.
EPISODE Forty Four
Yana sake koma wa wajen ta ya ga alamun ta sake sume wa, juya wa kawai yayi ya sake ɗibo ruwa ya watsa mata
Hakan yasa ta farfaɗo numfashin ta ya dawo, sai dai idanun ta suna rufe ta kasa buɗe wa, illa kuka da take yi ƙasa-ƙasa tana riƙe da kanta, sai faman rawan sanyi take yi haƙoran ta na karkarwa
Ko kaɗan ba ya jin zai iya taimaka mata saboda zallan tsanar ta da yake ji a ransa, juya wa ya sake yi ya koma ɗakin sa, magani ya ɗauko mata ya zo ya jefa mata, cikin kausashshiyar murya da zaka gane yana a cikin ɓacin rai, wanda daƙyar ma maganar take fita yace da ita, “ki gaggauta tashi ki gyara min gida. Kar in dawo na ga baki gyara nan wajen ba, kar na dawo baki cire min ƙazantar nan naki ba na maimaita miki.. “sai yayi shiru yana juya wa ya yi waje ya fice
Ɗahira bata motsa ba tana nan yanda ya bar ta, illa kuka da take tayi, sosai take kukan har da su shashsheƙa, ta rasa meyasa Usman ya tsane ta, mene ne tayi masa a rayuwa da yake nuna mata wannan zazzafan tsanar? Tana a cikin halin mutuwa ko rayuwa amma shi ko kaɗan ba ya tausayin ta, shin yaushe ne zai tausaya mata? Har yaushe ne zata fita a cikin wannan uƙuban nashi? Me yake nufi da ita ne? Idan so yake yi ya kashe ta meyasa bazai kashe ta a lokaci ɗaya ba sai ya gana mata azaba haka? Ba ta jin zata iya yafe wa Bawan Allan nan, har ABADA! Baza ta taɓa yafe mishi ba domin ya cutar da ita.
Ta shafe fiye da awanni uku bata iya motsa wa daga inda take ba, sabida ko kaɗan bata da ƙwarin jiki, ga tsananin ciwon da take fama dashi, amma don kar ya dawo ta fuskanci wulaƙancin sa, tana kuka ta yunƙura ta tashi daƙyar, jikin ta gaba ɗaya ya tsume sai karo da haƙori take yi tana ƙanƙame jiki, hawayen nata ma sun kafe illa kukan zuci kawai da take yi, daƙyar da jan jiki ta isa Fridge ta sanya hannu ta buɗe ta ɗauki ruwa, maganin da ya ajiye mata ta ɗauka tasha ko don wai zata samu sauƙin ciwon da take fama dashi, sai ta sake rarrafa wa ta isa inda gaba ɗaya ruwa ne sharkaf da aman ta a wajen, kallon wajen take yi tana tunanin ta ina zata fara, baza ta taɓa iya wa ba saboda zazzaɓin da take fama dashi, daga ƙarshe zube wa tayi nan ta dinga sheƙa wani aman, ga tsananin yunwa dake addabar ta, jikin ta sai faman rawa yake yi, majinu na tsiyaya ta hancin ta
Sake rarrafa wa tayi ta kwaɓe kayan jikin ta gaba ɗaya, ta sauya wani rigan daƙyar, rufe kanta tayi ta ƙudundune tana ci gaba da rawan sanyi, gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi ta rasa inda zata saka kanta, addu’a kawai take yi a ranta Allah ya kawo mata mafita, tunda take bata taɓa shan wahala makamanciyar irin ta yau ba. Runtse idanun ta tayi tare da tamke bakin ta zuciyar ta na ƙuna, duk second ɗaya tsanar Usman na sake ruruwa a ranta, tana jin har abada baza ta taɓa yafe masa ba, sai Allah ya saka mata.
Wasa-wasa har dare Ɗahira tana cikin wannan mawuyacin halin, ta kasa taɓuka komi, a haka ta wuni zurr komi bata saka a cikin ta ba, ta kasa ma tashi bare ta samu abinda zata saka a cikin ta, tana jin sai dai ya kashe ta domin baza ta iya yin komi ba.