FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Tuni ta tusa kanta a pilow ta saki wani kuka me cike da ƙunci da baƙin cikin abinda yayi mata
Kallon ta yake yi kawai be iya cewa komi ba, ba don dai ya san a part ɗin su yake ba babu abinda zai hana shi maimaita abinda yayi mata a baya, sai dai sosai ya daure ya zamo ta jikin ta har yana sakin mata nauyin sa ya sauka kan gadon. Sai da ya ɗan gyara gashin sa da rigan sa kafin daƙyar yace, “kiyi haƙuri kinji? Dama ganin baby na nazo Yi na kasa haƙura, tashi zaune mu gaisa”.
Ko motsi taƙi yi illa sautin kukan ta dake ƙara yawa
Ganin haka sai ya saka hannu kawai yana ɗaga rigan ta zai saka hannun sa ya shafa cikin ta yana faɗin, “to Ni bari in duba lafiyan Bab…”
Be ƙarisa ba da sauri ta tashi tana janyo hannun shi ta kama ta gantsara mishi cizo da ƙarfin ta
Ihu ya saki da ƙaramin murya yana ware ido, da sauri ya fizge hannun yana yarfe wa
“Mugu azzalumi ka fita a nan ɗakin ko in maka abinda ba ka zato”. Tayi maganar cikin ihu da hayagaga wanda ita kanta bata san cewa tana da irin wannan fushin ba
Sai ya saki baki kawai yana kallon ta
“Ka fita nace”.
“Ashe kin iya faɗa haka? To babu inda zan je tunda ke matata ce”.
Fashe wa da wani sabon kukan tayi da gudu ta tashi ta shige Toilet ta garƙame ƙofan
Duk yanda yaso ta buɗe ƙofan amma taƙi sauraron sa, illa kukan ta da yake jiyo wa kawai, sai ya wuce ya fice
Umma ce kaɗai a parlour’n, don tuni Aunty Amarya ta shige nata ɗakin saboda baza ta iya ganin abin kunyan nan da Usman yake shirin musu ba, tunda duk wani maganar su suna jiyo wa, sai dai basu fahimci me suke cewa ba illa hayaniyar su
Umman na ganin ya fice ta tashi ta shigo ɗakin Ɗahiran, ganin bata a ciki sai kukan ta da take ji a Toilet, sai ta taɓe baki tana bin gadon da kallo. “Oh dama wannan yaron haka kake ba ka da kunya?” Sai ta nufi kuma bakin ƙofan ta soma buga wa tana kiran sunan Ɗahira
But tana jin ta taƙi amsa wa
Dole ta fice ganin ta ƙi buɗe wa, a ranta tana faɗin, “muna-fukai zaku yi bayani ne daga ke har shi ɗin, ƴan iska kuna so kuna kaiwa kasuwa”.
Barka da sallah FAN’S. Da fatan an yi sallah Lafiya? Allah ya maimaita mana. Amma dai ban san cewa gaskiya baku so na ba sai yanzu, Ko ɗan cin-cin ɗin nan babu wanda yace “Ummu Ɗahirah ga naki”. Babu komo ai ????
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
بسم الله الرحمن الرحيم
⚖
FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
JIKAR LAWALI CE✍️
Wattapad: UmmuDahirah????
\F.W.A????/
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY
EPISODE Sixty Four
Sai da tasha kukan ta son ranta kafin ta wanke idanuwan ta ta fito, a hankali ta taka ta isa kan gadon ta hannayen ta a saman fuskar ta, kwanciya tayi tana sake cusa kanta a jikin gadon, gaba ɗaya ta rasa me ke mata daɗi, Usman yana son zame mata matsala a Rayuwa, shin me yake nema da ita ne yanzu? Ada ba ya ƙaunar ta amma yanzu yana nuna wa duniya yana son zama da ita? Shin ko dai wani abun ne yake son sake aikata mata? Shi ne ta kasa gane wa
“Allah ya fi ka Usman baza ka taɓa cin nasara a kaina ba, duk yanda zan yi sai na bi domin rabuwa da kai”. Tayi maganar a fili tana share hawayen da suka soma sintiri a fuskar ta.
Tana nan kwance sai ga Aunty Amarya ta shigo jin ta shiru da tayi
“Lafiyan ki kuwa Ɗahira?”
Ɗago kai tayi tana kallon ta, sai ta gyaɗa mata kai tana cewa, “eh Mama”.
Ɗan ƙura mata ido tayi ganin yanda fuskar ta duk ta sauya idanun ta suka kumbura, kowa ya ganta ya san tayi kuka, amma ta san cewa hakan na da alaƙa da zuwan Usman ɗin, ba dai tace mata komi game dashi ɗin ba, sai cewa tayi, “ta fito ta yi Breakfast”. Sannan ta fice
Itama tashi tayi tabi bayan ta, saman dainning ta zauna ta zuba arish da egg ɗin dake wajen a cikin Plate, sai dai gaba ɗaya ta gaza kaiwa baki saboda kawai ƙamshin be mata ba, gajeren tsaki taja tana miƙe wa
A lokacin Aunty Amarya ta fito ɗaki tana kallon ta tace, “ina kuma zaki je baki ci ba kin zuba zaki tafi?”
“Mama bazan iya cin komi a wurin ba”.
“Saboda me? Ko tea ɗin baza ki haɗa ki sha ba?”
“Mama bazan iya sha ba wlh, na san ina sha zai saka Ni amai”.
Da kallo kawai Aunty Amaryan take bin ta, sai kuma tace, “to me zaki ci sai na dafa miki tunda baza ki zauna da yunwa ba?”
“A’a Mama bari zan yi da kaina”.
“To ki kula”. Tayi maganar tana juya wa ɗaki
Ita kuma Ɗahiran ta wuce kichen, kai tsaye inda suke ajiye ƙullun koko ta wuce ta ɗiba kaɗan, sai ta ɗaura ruwan zafi. Wake ta samu ta sirfe ta zuba kayan miya ta markaɗa a blender, lokacin har ta dama kokon ta ta sake a jug sannan ta gama haɗa ƙullun ƙosan ta, sai ta ɗaura mai a wuta ta soma soya ƙosan, tun a wutan tana tsame wa take haɗiye shi da zafi-zafin shi. Kafin ma ta gama ta cinye sai ɗan kaɗan da ta bari, ta zuba kokon a Cup ta zauna nan ta cinye sauran da kokon
Umma ce ta shigo ta same ta a kichen ɗin, sai ta dube ta tana murmushi tace, “a’a yau kuma kwaɗayin koko da ƙosai ake ne babu tayi?”
Murmushi Ɗahiran itama tayi tace, “eyya ai ban san zaki ci bane shiyasa na cinye, amma akwai raguwan kokon”.
“A’a wasa nake miki, ci abin ki ai ke ce me lalura”.
Duƙar da kanta Ɗahiran tayi bata ce mata komi ba, ta ƙarishe shanye kokon tana miƙe wa ta fice ta bar ta a kichen ɗin.
Ɗaki ta koma ta sanya Hijab ƙarami a jikin ta ta fito ta wuce ɗakin Maman ta, ce mata tayi “zata je wajen Kaka”.
“To ke da baki da lafiya kuma meye na yawo?” Inji Aunty Amarya
“Don Allah Mama bazan daɗe ba wlh, zamu yi magana da shi ne”.
“Ok sai kin dawo”.
Fita tayi ta wuce wajen Kaka. Tana shiga da sallama
Ya amsa mata cike da fara’a
Sai da taje har gaban sa ta ja mishi Gemu kafin ta zauna a gefen gadon shi tana faɗin, “My Kakus Ina kwana. Ya kuma tsufan?”
Dariya yayi yace, “ai na bar miki Mata ta, ke ce kike fama dashi, Ni kuwa kin ganni sumul ba kamar ke ba da kullum kina rashin lafiya. Ya jikin naki to? Iyayen ki ɗazu suke faɗa min abun farin ciki”.
Kwaɓe fuska tayi tace, “Ni Kaka ba wannan ba, Ni don Allah yaushe za’a raba aure na da Yaya Usman? Ka ga har yanzu ina ta zaune da auren shi yaƙi saki na”.
“Abinda kike so yanzu kenan?” Yayi maganar yana kallon ta
“Eh Kaka”.
“Shikenan kar ki damu zuwa anjima zan tara ku mu yi maganar”.
“Yauwa Kaka na, na gode”. Tayi maganar tana sakar masa kiss a hannun sa
Murmushi kawai yayi mata yana shafa kanta be ce komi ba
Sai ta ɗago ta kalle shi tace, “Kakus baka da wani abun motsa baki ne a ɗakin?”.
Dariya yayi yace, “ina dashi mana, Jiyan nan Dadyn ku ya kawo min kayan marmari suna nan a Fridge ki ɗauka”.
“To bari in duba in gani ko akwai abinda zan iya sha”. Tayi maganar tana tashi tsaye tayi wajen Fridge ɗin, lemo ɗaya kawai ta ɗauko ta dawo ta zauna
“Shikenan abinda zaki sha?”.
“Eh. Ya ishe Ni wannan kar in shanye maka”.