BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

“Haba dai, tunda Ɗana yake so yasha ai babu damuwa, sai in saka ma yanzu a ƙaro miki idan kika shanye”.

Shiru tayi kawai bata ce komi ba taci gaba da ɓare lemon da hannu

Shi kuma Kaka sai yayi ta mata surutu duk a kan cikin nata, da idan ta haihu in dai na miji ne sunan sa za’a saka

“Kawai ina jin ka ne Kaka, amma ba daɗin zancen nake ji ba, kayi shiru don Allah”.

“Yo ko laifin Baban shi zai shafe shi ne?”

Ɓata fuska tayi tana tashi tsaye tace, “Ni dai na tafi. Sai anjima”. Bata jira cewar sa ba ta fice abun ta

Shi kuma sai kwaɗa mata kira yake yi yana faɗin “ta dawo”.

Dawowa tayi ta leƙo daga bakin ƙofan tace, “Kakus bazan sake zuwa ba yanzu sai kana ajiye min abun daɗi, tunda Babyn naka abun da yake so kenan”.

Dariya yake yi yace, “to shikenan, ai kuwa zan riƙa ajiye miki kar ki damu”.

“To byee na tafi zan dawo anjima ai”. Tayi maganar tana dariya ta fice

      Shima still dariyan yake yi zuciyar sa cike da farin ciki. “Usman da baka yi wannan abun tsiyan ba ai da farin ciki na sai yafi haka, amma kuma ka rigada ka ruguza komi, duk da haka dai ina da rabon ganin ɗan ku tare, ko ba komi dole wata rana ku dena nuna wa junan ku ƙiyayya tunda kuna da ɗa a tsakani”.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

          Tunda yaje Office ya kasa sukuni, duk abinda yake yi tunanin sa na gare ta, babu abinda ke dawo masa a rai sai abinda ya faru tsakanin su ɗazu, shiyasa abu kaɗan sai murmushi kamar wani zautacce, sosai yake kewar ta tabbas yana buƙatar matar sa a halin yanzu, meyasa baza ta yafe mishi komi ya wuce ba tunda ya bata haƙuri? Tun sanda abun nan ya faru a ƙauyen Baba Jaure yake dana-sanin furucin da yake mata na ɓatanci, da kuma kallon ta da yake yi a matsayin mazinaciya, haƙiƙa yayi dana-sani mara misaltuwa, wanda har ya ɗau alƙawarin duk wanda ya kawo mishi pictures ɗin nan da ya sake dagula mishi lissafi a kanta dole ne sai ya fuskanci wulaƙanci me muni, bazai taɓa barin ko waye bane sai ya ɗau mata fansa, idan da ba shi ne aka ba wa hotunan ba shikenan za’a riƙa tunanin tabbas ita ce.

        Shiyasa sai da yabi diddigin inda aka yi hoton, a can ne ya samu bayani a kan mutumin da ya zo aka yi mishi hoton, dayake sananne ne tunda ya saba zuwa wajen ana mishi, da ya kamo shi yaci uban sa kwanan sa biyu a rufe yana gana mishi azaba, inda kuma yayi mishi barazana a kan sai ya danƙa shi wajen hukuma muddin be nemo mishi waɗanda suka saka shi aikin ba. Wannan dalilin ne da yasa aka kamo su Ayush. Shi mutumin yayi musu wayau ne ya jawo su hotel ɗin a kan “baya ta haihu..” da suka zo kuma sai ya bugar da su daga ƙarshe ya ɗaure su….

                 Ajiyan numfashi Usman ɗin ya sauke yana ɗaukan wayan shi ya soma laluben numbobi, yana son jin muryan ta ko zai samu sukuni amma be san wa zai kira ba, be da Numban ta bare na Maman ta da zai iya kira, nan dai ya tuna dana Fadil sai ya danna mishi kira

Koda ya ɗauka sai yace mishi, “ya je ya kai wa Nafeesa wayan”.

Jiki na rawa Fadil ya soma inda-inda don be gane da wacce yake nufi ba

To abun ne ai yazo musu da sabon salo tunda dai kowa da Ɗahira yake kiran ta, babu wani me kiran ta da sunan ta, shiyasa wani lokacin ma suke manta sunan ta, amma shi da iyayi irin nasa dole sai ya bambanta kanshi da kowa

“Ka kai mata wayan ka tsaya kana min shirme”. Yayi maganar cike da ɗan tsawa

“Yaya ai ban gane wacce kake nufi ba”.

Tsaki yaja yace, “stupid.. Ɗahira”.

“Ai Ina school ban dawo ba..”

Be jira sake jin wani zancen nashi ba ya katse wayan yana ajiye wa cike da takaici, ba don ya so ba yaci gaba da aikin da yake yi, sai kuma ya tashi ya fice ya tafi duba patiens ɗin da yake da su.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

        Da dare Kaka ya sanya a tara mishi jama’an gidan, bayan kowa ya hallara sai yayi musu magana a kan “sakin da Usman zai yiwa Ɗahira ne, yanzu ya kamata ace ya bata takardan ta kowa ya huta”.

Big Dady yace, “nima nayi mishi maganar jiya, amma dayake shi fitsararre ne yake faɗa min maganar ma da bazai yiwu ba, wai “bazai sake ta ba a bar shi da matar shi”.

Kaka kallon Usman ɗin yayi da kanshi ke ƙasa. yace, “ai sakin ta ya zama dole kuwa Fodio tunda mu baza mu sake mata tilas ba, tunda ita take buƙatar a raba auren nan babu me matsa mata ta zauna da kai a wannan karon, tun farko abun da muka hango muku kenan sha’awar zaman ku tare har muka haɗa ku, amma kuma sai kayi watsi da umarnin da muka baka kaƙi mana biyayya, hakan yasa ka je ka gallaza mata son ranka, sai ga shi Allah ba azzalumin bawan sa bane kaima yanzu kana son zama da ita, to, ai ita ba jaka bace da zamu sake baka kaje ka sake maimaita mana abinda kayi a baya, maganin kar ayi kar a fara Allah ya haɗa kowa da rabon shi kaji ko? Yanzu ga ta nan ba sai ma ka sha wahalan rubuta wa ba sai ka sake ta kowa yaji, yaron ka kuma idan Allah ya sa ta haifa maka zata raina har zuwa yayen shi kafin ta baka kayan ka”.

“Kaka kuyi haƙuri da abinda nayi muku a baya wlh nayi nadama bazan sake ba, bazan iya sakin ta ba saboda ina son zama da ita, ko don abin dake cikin ta be kamata a raba mu ba..”

“Abun cikin ta ɗin uwaka? Usman kar ka ja mu kai maganar nan kotu wlh, idan har Daughter Bata yarda zata koma ba rashin sakin ta bazai hana mu baka ita ba, sai dai mu je kotu a raba”. Cewar Big Dady kenan cike da haushin Usman ɗin

Tashi Usman ɗin yayi yana faɗin, “Allah na rantse bazan sake ta ba, duk abinda za’a yi sai dai ayi baza a mayar min da ɗana Maraya ba”. Daga haka ya fice da sauri daga parlour’n ranshi a ɓace

Su kansu maganar Usman ɗin ta ba su dariya, wai Maraya

Abba ne yace, “abi komi a sannu babu maganar zuwa kotu, saki ne dai dole ya bata idan ya gaji bata koma ba”.

“To amma ai ita daughter za’a cuta zata yi ta zama da auren shi a kanta”.

Kaka yace, “kowa ya tashi ya tafi in yaso sai muci gaba da tattaunawa da ku ko?”.

Duk fita suka yi suka bar su Big Dady.

            ⚫⚫⚫⚫⚫

     “Ba dai kuka kike yi ba Ɗahira?”

Ɗago kai tayi tana kallon Maman nata, sai ta saka hannu ta soma share hawayen ba tare da ta iya magana ba

Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta saki tana zama kana tace, “Ɗahira ba na son kina saka damuwa a ranki, Ni abinda nake gani kiyi haƙuri ki koma gidan Usman tunda ya nuna yayi nadama yanzu, har ga Allah ina ganin soyayyar ki a idanun shi, tunda kuma ga abinda yace kiyi haƙuri ki yafe mishi ki koma ki zauna a ɗakin ki, hakan zai fi miki sutura ke da abinda ke cikin ki, Allah ma ana mishi laifi ya yafe bare ɗan Adam”.

“Mama ko na yafe mishi ni bazan iya zama dashi ba wlh, har yanzu ina ganin abubuwan da yayi min na kasa manta wa, shiyasa nake jin bazan iya sake zama a ƙarƙashin sa ba, idan har na koma gidan shi bazan taɓa jin daɗin zama dashi ba domin zuciya ta cike take da tsanar shi”. Ta ƙare maganar cikin kuka

“To ki yi shiru ai ba na ce ki koma bane tilas, babu wanda zai tilasta miki Ɗahira sai da yardan ki, Kinga ga Abbun ki can na Kira na bari inje, ki dena fa kukan nan na faɗa miki”.

“To”. Ta amsa ta tana koma wa ta kwanta

Ita kuma Aunty Amarya fita tayi, ganin babu shi a Parlour sai ta wuce ɗakin ta, a nan ta ganshi zaune a kujera, ta ƙarisa ta zauna tana cewa, “Ga Ni Abbun Zulaiha. Ina ɗakin Ɗahira ne muna magana”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button