BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

“Maganar me kuma?”

“Ka san bazai wuce na abinda ya faru ba, ta koma ɗaki tana ta kuka tunda abun kuka ba ya mata kaɗan ita”.

“Allah Sarki Mama na. Ni a gani na gwara ta bar abun nan ya wuce ta koma ɗakin ta hakan zai fi ai, tunda ɗan Adam ajizi ne Allah ma muna mishi laifi ya yafe bare mu Mutane, yanzu maganar da muka gama kenan da su Baba, Amma shi sam Yaya Noor yaƙi yarda”.

“Haka ne. nima abinda nake sanar mata kenan, tunda ka ga Usman ya furta hakan tabbas yana ƙaunar ta yanzu, kuma na tabbata duk abinda yayi mata a baya bazai sake aikata wa ba”.

Murmushi Abbu yayi yace, “ai maganar ƙauna ma bata taso ba yanzu tunda ga rabon jika mun samu, dama mata da miji sai Allah tunda ga shi a faɗan nasu ne suka sama mana jikalle”. Ya ƙare maganar yana dariya

“Kai Abbun su har da kaima?” Aunty amarya tafaɗa tana dariyan itama

“Eh mana. To ai gaskiya ce, kawai dai abinda zamu yi muyi ta tausan ta har ta amince ta koma, kin san ɗiyar taki halin ki ta biyo, wlh kuna da sauƙin kai, tunda ke kika manta abubuwan da ya yiwa ɗiyar ki kike son ta koma, itama na tabbata da ace zamu bata umarnin koma wa baza ta taɓa mana musu ba, sai dai na san hakan da cutarwa gwara mu lallaɓa ta har sanda taji don kanta zata iya koma wa, idan kuma mijin nata shi yayi ƙoƙarin shawo kanta shikenan, amma kar mu goyi da bayan ta wajen raba auren nan tunda be da wani amfani, Allah shi yaga abinda ya gani har ya kawo wannan cikin a tsakanin su, ni ina ga shi zai zame musu alkhairi”.

“Haka ne Abbun su, to Allah yasa mu dace”.

“Amin ya Allah. Yanzu ki kira min ita in tambaye ta kan wayan da tace take so”.

“Ka bari sai gobe mana tunda naga yanzu kamar ta kwanta ai”.

“To Allah ya kai mu, bari in duba Bilkisu ina dawowa”. Yayi maganar yana tashi ya fice.
????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

        EPISODE Sixty Five

        Usman dai tunda ya fita gidan shi ya wuce kai tsaye, gaba ɗaya duniyar tayi mishi zafi ransa duk ya gama ɓaci, shi a ganin shi don yace “bazai sake ta ba ne”. Suke mishi haka, to su riƙe ta kar su barta ta dawo, shi kuma wlh bazai sake ta ba har sai sun gaji sun kawo ta da ƙafafuwan su, barin ma ƙasar zai yi tunda don suna ganin shi ne shiyasa suke mishi haka, tunda ya basu haƙuri ya ce zai zauna da ita meye kuma laifin shi a nan? Ko albarkacin cikin shi ai be kamata su raba auren ba. Wani zuciyar tashi tace, “amma ai kaima baka kyauta ba, ko kai ne a madadin ta zaka guje wannan auren, tabbas ka bata wahalan da in dai tana da hankali dole ta guje ka gaba ɗaya”.

“Amma to ai na bata haƙuri, kuma na gane kuskure na bazan sake ba”. Yayi maganar a fili yana hawaye. Sai ya mirgina kwanciyar sa yaci gaba da tunanin zucin shi dake ƙara mishi ƙunci da raɗaɗi, duk tunanin Ɗahira ya addabe shi ya rasa ya zai yi

Yau dai rana ɗaya ya tashi domin neman agaji a wurin Allah, abin da be taɓa yi ba, domin idan har ka ga Usman ya tashi da dare yana Sallah to tabbas yana cikin ƙunci ne sosai, yau dai ga shi haka ya tashi yayi ta jero salloli yana neman biyan buƙata wajen Allah, da kuma neman ya yaye mishi duk damuwar shi, Allah ya gani yanzu yana ƙaunar Ɗahira, yana jin son ta kamar ya kashe shi yanzu, be san ya aka yi ya faɗa wannan mugun son nata ba,  shiyasa gaba ɗaya sallan duk a kanta yayi

Be dena ba sai da kusan uku tayi, sai ya jira har aka yi sallan asuba yayi a wurin don bazai iya zuwa Masallaci ba, yanzu ɗin barci yake ji sosai, shiyasa yana gama wa ya kwanta.

        Be tashi ba sai wajen goma na safe, wanka yayi ya shiga kichen daga shi sai gajeren wando ya haɗa tea ya zauna a Parlour Yana sha, duk gaba ɗaya tunanin sa ya tafi ga hukuncin da zai yanke

Bayan ya gama ya tashi ya mayar da kofin kichen, ya wanke kafin ya koma ɗaki, kayan shi ya soma haɗa wa a Trolly har ya gama, sannan ya shirya cikin ƙananan kaya farar riga me wuyan V da gajeren hannu, sai wando jeans blue colour crazy, gaban mirror yaje ya gyara gashin kansa kafin ya feshe ko ina na jikin sa da turare, ya ɗauki agogo ya ɗaura a hannun sa sannan ya zira takalman sa sandal da ya zaro su daga ƙasan gadon shi, ya ɗan share kasancewar da akwai ƙura yaja Trolly ɗin sa ya fito, sai da ya kashe komi kafin ya fice, kai tsaye wajen motan shi ya nufa yana shirin saka wa a Boot

Hajiya da ta fito ta ƙaramin ƙofan gidan su ta hange shi, kwaɗa mishi kira tayi tana nufo shi

Sai ya juyo yana kallon ta fuska babu fara’a, gajeren tsaki yaja yana ƙarisa tusa Trollyn cikin Boot ɗin sannan ya rufe, ya nufe ta ba tare da ya amsa kiran nata ba

“Ina zaka je haka da kaya? Ba dai tafiya zaka yi ba a kan maganar nan?”

Sai da ya ƙumshe baki ya saki iska kaɗan tare da sake haɗe fuska yace, “tafiya zan yi Mom, idan sun gaji da jira na sai su aiko min ita”.

“To a tunanin ka kana ganin hakan shi ne maslaha a wurin ka? Kar ka manta ita yarinyan nan ba ƙaunar ka take yi ba, memakon ka zauna ka gyara alaƙar ku a wajen ta shi ne kake son sake jagula lissafin ko? Kai a tunanin ka su Dadyn naka za su aiko maka da ita? to, ka dawo hankalin ka tun wuri ka sauya tunani ba na son shashanci kaji ko. Ka je Dadyn ka na kiran ka”. Daga haka ta juya ta wuce ba tare da ta jira jin ta bakin shi ba

Shi kuma yana tsaye ƙiƙam yaƙi jirga wa sai bin bayan ta da yake yi da kallo, har ta ƙule wa ganin shi be motsa ba, sai ma ya saka hannayen sa cikin aljihu yaci gaba da tsayuwar sa a wurin. Sai da ya mula dan kanshi kafin ya taka ya nufi hanyar da ta biyo, kai tsaye Part ɗin su ya wuce ya shiga da sallama

Big Dady na zaune a kujera yana kallon labarai a t.v, dayake yau Saturday ne basu da aiki, duk da ba hutu suke ɗauka ba amma ba sa zuwa Hospital ɗin sai yamma ko kuma duk sanda suke so, idan kuma ana buƙatan su suna zuwa su duba mara sa lafiya su dawo, sun dai ɗauki weekend ranan hutun su ne sai an buƙace su tunda akwai likitoci kala-kala.

       Amsa mishi sallaman yayi ba tare da ya kalle shi ba

Shi kuma ya tako ya zauna a ƙasa jikin kujeran dake kallon wanda Big Dady ya zauna, be ce komi ba ya sadda kansa ƙasa

“Ina zaka je da Mom ɗin ka ta ganka kana saka akwati a mota?”

Shiru yayi ya kasa magana

“Da kai nake magana”.

“I’m traveling”.

“Ok to bani takardan nata tunda dai baza ka tafi da auren ta a kanka ba. I spoke and remained silent”.

“Dady don Allah kuyi haƙuri ku yafe min don Allah Dady, wlh ina ƙaunar ta yanzu bazan iya rabuwa da ita ba, ku sake bani dama Please zan je in nemi afuwar ta, na yarda idan har ba ta ƙauna ta zan rabu da ita dan girman Allah Dady kaji?” Ya ƙare maganar da rarrafo wa gaban Dadyn yana me riƙe mishi ƙafa hawaye na tsiyayan mishi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button