FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Duk ya kashe mishi jiki shiyasa yayi shiru kawai yana kallon shi, har ga Allah yana ƙaunar su ci gaba da zama a tare amma kuma shi yana yin hakan ne domin amsar mata haƙƙin ta, Usman ya zalunta mata be kamata ayi shiru a bar shi haka ba, sai dai tunda ya ce haka; zai ba shi dama ya je ya nemi amincewar Ɗahiran, idan har ita taga zata iya zama da shi shikenan, idan kuma tace a’a dole ne sai ya amsar mata takardan sakin ta
“Ya isa haka”. Yace dashi ganin yanda yake ta mishi magiya
Shiru Usman ɗin yayi kanshi a ƙasa amma hawaye be dena fita a idanun sa ba
Numfashi Big Dady yaja kafin yace, “tun farko Usman ba ka jin magana, mu iyayen ka mu zaɓa maka abinda muke ganin ya dace da kai amma ka nuna mana bamu isa ba, yanzu wa gari ya waya? Wlh Allah ne ya saka mata tun yanzu domin ka gane ɗan Adam ba abun wulaƙanta wa bane, a matsayin ta na ƙanwar ka jinin ka amma ka gallaza mata wannan azabar. Dama ɗaya tak zan iya baka kaje ka nemi amincewar ta, idan har ta yarda zata koma wajen ka falillahil hamdu, idan kuma tace a’a ka san baza mu taɓa mata tilas ba, ka tashi kaje”.
Lumshe idanun sa yayi jin abinda Dadyn yace, zuciyar sa cike da murnan da be san iyaka ba yace, “thanks Dad”. Sannan ya miƙe zai fice
“A haka zaka fita baka share hawayen naka ba?”
Ɗan juyo wa yayi yana murmushi ya saka hannu ya share hawayen, yana cire hannun sa suka haɗa ido da Hajiya dake bakin ƙofan ɗakin ta tana mishi murmushi, still shima murmushin yayi zai juya ya fice
Sai Big Dady ya sake cewa, “ina kuma zaka je baka yi Breakfast ba? Dawo ka karya zan aike ka Office ka ɗauko min saƙo dana manta da shi”.
Usman ɗin be ce komi ba ya juya ya nufi dainning ɗin, bakin sa bazai iya faɗin “a ƙoshe yake ba” shiyasa kawai yabi umarnin sa ya zauna don yaci abinda zai iya
Hajiya ƙarisa wa tayi ta zauna tana haɗa mishi Breakfast ɗin tana tsokanar shi
Shi kuma murmushi kawai yayi, da yaga zata haɗa mishi da tea yace, “ta bar shi ya sha”.
Big Dady dai na jin su be ce komi ba yaci gaba da kallon shi.
Har sanda Usman ɗin ya gama ya dawo wurin shi ya amshi keey ɗin office ɗin, tare da faɗa mishi abinda zai ɗauko mishi, shi kuma ya wuce ya fice
Bazai iya tafiya be ga fuskar Ɗahira ba shiyasa kai tsaye ya wuce Part ɗin su.
Duk suna zaune a parlour’n ban da Ɗahira dake kichen tana ma kanta faten tsaki da take sha’awan sha
Tana jin muryan Usman ɗin sa’ilin da yayi sallama yana gaishe da su Abbu, sai da gaban ta yayi muguwar faɗi tayi saurin dafe ƙirjin ta tana ƙwalalo ido, “kar dai ace wannan ɗan iskan ya zo maimaita min abinda yayi min ne jiya?” Tayi maganar a fili tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudun tsere
Jin kamar hiran su da Abbu ne yasa ta matsa da sauri ta leƙa kanta, ta hange shi yana zaune a kujera sai dai ya juya wa ƙofan kichen ɗin baya, sai Umma da Fadil a wajen, Aunty Amarya kuma ta tashi ta wuce ɗaki
Ajiyan zuciya ta sauke sai kuma taja gajeren tsaki ta wuce taci gaba da abinda take yi, sai dai duk bata da cikakken nutsuwa domin har ta yanke shawaran zama a kichen ɗin idan ta gama sai tasha faten nata tunda taji kamar be da alamar tafiya. Ta gama kenan tana zuba wa a Plate sai ganin shi tayi a kichen ɗin, kafin ma ƙamshin sa ya shigan mata hanci har ta ga dogayen ƙafafun sa a gaban ta, da sauri ta ɗago kai tana ware manyan idanun ta a kan shi da suka yi fari tarr babu ko kwalli
Wanda kallon nan ba ƙaramin sagar mishi da jiki yayi ba, sai da ya wani lumshe idanu ya buɗe su daƙyar ya sake aro jarumta wajen kallon ta
Ita kuma tuni ta janye idanun ta ta sake haɗe rai tana zazzare idanun, a ranta tana mamakin rashin kunya irin na Usman, ko dama haka yake? Ya zai shigo mata kichen ya baro su Abbu a Parlour? tana son mishi magana amma kuma haushin sa yasa tayi gum don taga iya gudun ruwan shi. Tana gama zuba faten a Plate ɗin ta rufe sauran a tukunya ta sunguma na Plate ɗin zata fice
Sai yayi saurin saka hannu ya damƙe nata yana matsa wa gaban ta, cikin sanyin murya idanun sa na kanta yace, “Nafeesata babu gaisuwa haka ake yi? Ko don na zama maƙiyin ki shiyasa har yanzu bazan samu arziƙin da za’a iya gaishe Ni ba? Domin ki fa nazo”.
Da ya san yanda take ji da kasancewar su waje ɗaya da ko kaɗan be zo inda take ba, gaba ɗaya har raunin ta yana shirin fito wa sai dai sosai tayi Jarumtar dakewa, daƙyar ma take iya numfashi saboda yanda take ji a jikin ta, saurin janye hannun ta tayi ba tare da ta kalle shi ba tayi ƙofa ta fice da sauri
Shi kuma yabi bayan ta tana saka ƙafa a ɗakin ta shima yana saka wa
Dayake tuni Abbu ya fice wajen Kaka shi da Fadil, wannan dalilin ne ya samu ya biyo ta kichen. Ita kuwa Umma tana zaune ta hange su sun wuce ɗin, sai ta kama haɓa kawai ta saki wani ashar da ya suɓuce mata bata shirya ba.
Ɗahira dake shirin zama a ƙasan ɗakin sai ganin mutum tayi a gaban ta. Da sauri ta ajiye Plate ɗin tana faɗin, “lafiya wai? Ka san dai be kamata kana biyo NI ɗaki na ba ko?”
“A kan me? Ba ke matata bace?”
Tsaki taja tana cewa, “ka dena ma tunanin wannan tun tuni na tashi a matsayin matar ka, Please Malam fitan min a ɗaki kaji ko?” Ta ƙare maganar tana nuna mishi hanya fuskar ta a tamke kamar bata taɓa sanin mutunci ba
Sai yayi guntun murmushi ya kawo hannu zai shafa fuskar ta tayi saurin matsar da fuskar, “hmm kin yi min kyau sosai Sweety, meyasa kike son min tsaki ne ki dena kin ji ba na so? Kuma na zo ganin baby na ne ko kar in zo?”
Jin haka sai tayi shiru ta zauna ta saka hannu a faten ta soma sha a hankali, duk da a takure take amma bata ko nuna hakan ba a fuska, nuna wa ma tayi tamkar ma babu shi a wurin
Shi kuma sai bin ta yake yi da kallo yana sake ƙare wa jikin ta da ya tafi dashi kallon tsab
Dayake tana sanye da riga da skert ne ƴan kanti Robber, rigan me wuyan V irin nasa fara, amma nata kamar vest ne don ya fi taushi sosai, sai skert ɗin me santsi ja da Flower’s da aka yi da kalan fari, kanta sanye da hula na kayan
Sosai yanda yake bin ta da kallon yake shiga har can cikin jikin ta, gaba ɗaya ta rasa sukunin ta, duk yanda taso ta daure amma ta kasa sai ta ɗago kai tana bin shi da kallon harara cike da haushin kama sa da tayi yana mata wannan kallon maitan
Shi kuma sai a lokacin ya wani ajiye numfashi yana ware idanun sa da suka ƙanƙance suka soma sanja kala
Ranta duk a ɓace tace, “don girman Allah ka fita ka bani wuri kar wani yayi tunanin wani abu kake yi a nan, tunda kai baka da kunya Ni ina dashi”.
Sai kawai taga ya zauna a gaban ta, daƙyar ya furta, “nima zan sha”. Kafin ma ta ba shi amsa ya tsulma hannu a ciki ya soma kaiwa baki
Tsaban takaici da ya cika ta sai ta yunƙura zata tashi
Yayi saurin janyo ta ta koma ta zauna daɓas
Da kallo ta bi shi kamar zata yi kuka jin sai da ta bugu da ta koma ta zauna. “Wai kai ba ka iya sukuni ne sai kayi mugunta?” Tayi maganar a fusace tana banka mishi harara
Be ce mata komi ba illa ci gaba da yayi da shan faten, sai dai yana riƙe da hannun ta be saki ba
Fushi tayi ta kasa motsa wa bare tasha faten zuciyar ta sai tafarfasa take yi da haushin Usman ɗin, gaba ɗaya ya takura mata har hawaye sun soma taruwa a idanun ta, sosai ta kumbura tayi fam jira kawai take yi ta mishi bala’i, amma ganin yaƙi ce mata uffan ya zaƙe sai shan faten shi yake yi ya bar ta da tsinkewar yawu, sai da ta kalle shi kafin ta kalli Plate ɗin, sai ta saka ɗaya hannun nata ta janye tana faɗin, “wannan ai mugunta ne, ya za’a yi ka zauna kana shanye min faten ko kai ne me cikin?”