FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2
Shi kuma tuni ya tashi ya fice.
Ɗahira da ta fita sai ta wuce wajen Kaka ta sanar mishi zata je gidan Hajiya Baseera tayi kwana biyu
Shima sai da yayi mata faɗan, “bata da lafiya be kamata taje ba”.
Amma takalallame shi da daɗin bakin ta tuni ya yarda, har yana bata saƙon gaisuwa
Fadil shi kuma nan ya maƙale mata sai ya bi ta, inyaso zuwa anjima shi zai dawo
Tace mishi, “ya biyo ta su je”.
Part ɗin su suka wuce, suka shirya, ita da kayan ta a ɗan jaka suka fito, Ali drever’n su shi ya tafi kai su tunda Aunty Amarya ta ce kar ta sake tayi tuƙi.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
“Suhail kira min Auntyn ka a ɗaki”. Cewar Abba da ya fito daga ɗakin shi yana saɓa malin-malin
“To Abba”. Inji Suhail ɗin yana tashi da sauri bayan ya ajiye remote ɗin hannun shi
Shi kuma ƙanin shi me suna Abdulra’uf da suke kiran sa Abdul; da sauri ya tashi ya nufi wajen Abban yana faɗin, “Abba na nima zan je”.
Hannun sa ya riƙe suna zama, da murmushin sa yace dashi, “a’a Abdul, ai ba nan kusa bane inda zamu je, kuma ɗaurin aure zamu je. Ka bari dai zan yi muku tsaraba ko?”
Gyaɗa kansa yayi cike da murna
“To kaima kira min Maman ka a ɗaki”.
Abdul ɗin na tafiya, shi kuma Suhail ɗin ya fito da kuka, Direct wajen Abban ya nufa dake tambayar shi “me ya faru dashi?”
Cikin kuka ya sanar mishi “Hajja ce ta duke shi”.
“To kayi shiru kaji? Kayi haƙuri baza ta sake ba”. Abba yafaɗa duk ransa babu daɗi yana shafa mishi kai
Aunty Jamila da ta fito daga ɗaki ita da Abdul ɗin tace, “ah ah kukan me kake yi kai kuma?”
Be iya ce mata komi ba tunda kukan yaci ƙarfin shi
Sai ta kalli Abba tana ce mishi, “har ka fito Alhaji?”
“Eh na fito, ki rarrashe shi don Allah bari in zo”. Yace hakan yana tashi ya wuce ɗakin Hajja Fatu. Yana shiga ya ganta kishingiɗe tana sakace. Da kallo ya bi ta ranshi a ɓace yace, “Wai Fatima me kike so ki zama ne? In aiko yaro ya kira ki shi ne kika dake shi?”
Kallon shi tayi itama da fuska a haɗe tace, “kai baka da ƙafan zuwa ka kira Ni ne sai dai ka aiko min agola ɗaki? To wlh duk ranan da ya sake shigo min ɗaki; wlh tallahi sai na farfasa mishi jiki”.
“To idan kin fasa don Allah, tunda zaman lafiya ne ba kya so, to, ina dai-dai dake kar ki fasa kinji? Sannan idan kin so yau ma kar in dawo in tarar baki yi abinci ba, wlh ranki idan yayi dubu sai ya ɓaci, duk iskancin dake kanki zan sauke miki”. Yana gama faɗar haka ya fice da sauri
Tsaki ta ja ƙasa-ƙasa tace, “kaɗan ma ka gani, ai ka auro wacce zata yi maka amma ba Ni ba, daga yau ita sai ta ɗauke maka duk abinda nake maka”. Sai ta sake jan dogon tsaki tana ɗaukar wayan ta ta hau kiran layin Hajiya Sa’ima.
Abba na fita sallama yayi wa Aunty Jamila ya fice
Ita kuma sai taja yaran nata suka shige ɗaki tunda babu abinda za su ɗauka a parlour’n, dama haka suke yi sabida baƙin halin Hajja Fatu.
Tana shiga Abba ya dawo da ninyan ɗaukan keey ɗin motan shi, ɗakin sa ya shiga ya duba be gani ba, sai ya tuna jiya a ɗakin Hajja ya sauka, kuma ya tabbata ya bar shi can, sai ya wuce can ɗin don ya ɗauka, amma yana shirin buɗe ƙofan ya jiyo maganar ta, dayake ba a hankali take maganar ba kasancewar ta san ya fita
A dai-dai lokacin take faɗin, “Ni ba wannan ba Hajiya Sa’ima, maganar wancan matsiyaciyan da nake son a raba ta da Usman, gaba ɗaya na dena runtsa wa tunda yaron nan ya fara nuna yana son komar da ita ɗakin shi, kenan buri na bazai cika ba na mayar da ita bazawara?..” sai tayi shiru tana sauraron Hajiya Sa’iman. Kafin kuma tace, “so nake yi yanzu mu koma wajen Malamin nan ya yi min aikin da ya fi wancan, wlh muddin ina numfashi nayi alƙawari bazan taɓa bari A’isha da ɗiyar ta su yi rayuwar jin daɗi ba, ada naci wannan alwashin bare yanzu da suka yi min sanadin mutuwar ɗana da nake matuƙar so, a kan shi duk na rasa wata ƙima ta a gidan nan, shikenan min ɗana na miji amma na rasa shi, dole ne in sake sanya mummunan gaba da tsana a tsakanin su, ta yanda ko ya ƙi ko ya so sai ya sake ta, su kuma burin su na son su ga sun daidaita su bazai taɓa cika ba, har ita Hajiyan ma wannan karon sai na haɗa ta da Malam tunda ta nuna yanzu ta dawo da son tsinanniyar….”
Daga nan Abba ya dena ji ya juya da sauri jikin sa na rawa, gaba ɗaya jin sa yake yi a wani irin yanayi, cike da ɓakin ciki da tsantsan ɓacin ran da kalaman Hajjan suka saka shi, sai ya wuce kanshi tsaye ɗakin Kaka
Inda suna zaune su uku, shi da su Abbu suna zaman jiran Abban ya zo su wuce ɗaurin Aure.
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
بسم الله الرحمن الرحيم
⚖
FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
JIKAR LAWALI CE✍️
Wattpad: UmmuDahirah????
\F.W.A????/
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY
EPISODE Sixty Seven
Yanda ya shigo musu ranshi a ɓace sai duk suka hau tambayar shi
Nan yake sanar musu da komi abinda yaji Hajja Fatu tana faɗi
Gaba ɗaya su kansu hankalin su ya tashi, “shin tun yaushe Hajja take wannan ɗabi’ar ba tare da sun sani ba? A ganin su dai suna zaune lafiya da Aunty Amarya, me ya jawo wannan mummunan tsanar?” Duk kan su sun shiga damuwa da rashin jin daɗin abun
Sai Kaka yace wa Abban, “ya je ya kira wo ta”.
Abba juya wa yayi ya koma can Part ɗin nashi, inda ya cidda ita tana wayan har yanzu bata gama ba, tsamo-tsamo ya kama ta tana wayan kansacewar ya bankaɗo ƙofan ne ya shigo
Sai duk ta daburce ta rikice ta rasa inda zata saka kanta. Yanda ta ga idanun sa sun kaɗa sun yi ja sai ta sake daburce wa, domin ta sadakar ma ya gama jin ta, tana shirin mishi magiya har ta duƙa a ƙasa
Sai ya dakatar da ita daƙyar ya furta, “ki ajiye kalaman ki ki biyo NI mu je”. Yana faɗa ya fice ya bar ta a wannan mawuyacin halin
Bata da tsimi bare dabara dole ta tashi tabi bayan shi zufa na keto mata, ta rasa ma wani addu’a zata kama tayi sabida tsaban tashin hankali, idan kuwa tabbas Abba ya ji abinda take faɗa ai ta kaɗe, shikenan asirin ta ya tonu, “wayyo Allah na na shiga uku Ni Fatu”. Bata sake rikice wa ba sai da taga sun shiga ɗakin Kaka
Kaka ransa a ɓace yace, “ashe ke mutumiyar banza ce Fatima? Duk Nasihan da muka yi miki ashe baki saduda kin zama mutumiyar kirki ba? Duk abinda ke faruwa tsakanin Usman da Nafeesa ashe duk ke ce kika jawo? Kina kuwa so ki gama da duniya lafiya? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. har wajen Boka kike zuwa a kan kin ga kin muzguna wa bayin Allan nan wato? Shin ina hankalin ki yaje Fatima? Wlh yau ina tirrr da halin ki, ina tirrr da kasancewar ki ɗiya a wuri na”. Sai ya kalli su Big Dady yace, “kai ku kira min gaba ɗaya mutanen gidan nan domin kowa ya san me ke faruwa, wannan ba abun ɓoye wa jama’a bane tunda abinda kika zaɓa wa kanki kenan, har ita Ihsan ɗin ku kira min ita”. Kaka ya ƙare maganar cikin matuƙar ɓacin rai da zafi