FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2
“To gagarumin abu ne dai ya faru, yau dai asirin Fatu ne ya tonu, ayi yarinya sam ta fita daban da ƴan uwan ta, wannan wani irin tsana ne haka?” Nan dai ta kwashe komi ta sanar mata, kana ta ƙara da faɗin, “Ni ina ga Ɗahira ba laifin mijin ki bane, a gani na gwara ki koma gidan ki ku ci gaba da zama tunda gaskiya ta bayyana, duk abinda yayi miki ba a cikin hankalin shi bane, taya ma kina a matsayin jinin sa zai nuna miki wannan rashin imanin? kema zaki gane tabbas ba a hankalin shi yake ba, abun da nake roƙon ki da shi ki manta komi ya wuce domin ki ba ma mara ɗa kunya, duk sharrin da take bin ki da shi ki nuna mata Allah ya fi ta, kar ki taɓa bata damar da zai saka ta cin ma burin ta”.
Ɗahira da take ta faman kuka tun jin labarin komi, sosai zuciyar ta ke mata zafi, “meyasa Hajja Fatu ta tsane ta? Me tayi mata a rayuwa?” Abinda take ta ambata a ranta kenan tana ƙara Volume ɗin kukan ta
Hajiya Baseera rarrashin ta ta hau yi tana faɗin, “Ke yanzu ba kuka zaki yi ba, yanzu kuka ya ƙare tunda kin gano musabbabin abinda ke faruwa, mijin ki kawai zaki riƙe gam kinji ko?”
“Amma Kakalle ai tun kafin Hajja Fatu ta shiga tsakanin mu ya tsane Ni, meyasa ya tsane Ni tun ina ƙarama ta? Ki tambaye shi meyasa? Ina son in sani. Idan har be faɗa min ba bazan taɓa ganin farin shi a idanu na ba”. Ta ƙare maganar tana kuka sosai
Usman da duk zuciyar sa ta karye da kukan da take yi, cikin raunin murya na wanda juriya ne kaɗai ya hana shi shima ya koka yace da ita, “na san nayi miki laifi Ɗahira amma kiyi haƙuri kinji? bani da hujjar da zan iya kare kaina a wajen ki, amma ina roƙon ki da ki sake bani dama, ki manta komi ya wuce, zan gyara Laifuka na nima, zan kuma mantar dake duk wani baƙin ciki na da kika ƙunsa, zaman mu tare ne kaɗai zai sa ki yafe min sannan ki manta komi a rayuwar ki, ina son ki Ɗahira! Ina matuƙar ƙaunar ki! bazan iya rabuwa dake ba ki yafe min kinji?”
Yanda Kalaman sa suke ratsa mata kunnuwa dole ne zuciyar ta ta karye, tana ji a ranta tabbas ta yafe mishi, sai dai baza ta iya buɗe baki tayi masa magana ba, baza ta iya ce mishi ta amince da zama da shi ba, tana ganin ya dace ta sake yarda dashi a karo na biyu? Har yanzu zuciyar ta bata gama yarda da shi ɗari bisa ɗari ba, tana ga kamar yaudaran ta yake yi, mutumin da ya tsane ta tun tana tsumman goyo har girman ta; kuma yanzu ya dawo ya ce yana son ta? Duk bakin da ya furta tsana ko da ya dawo ya furta so; to, kar ka taɓa amince wa da shi, domin ƙarya yake yi akwai manufa a zuciyar sa. sai ta sake fashe wa da kuka tana tashi da gudu tayi hanyar ɗaki ta shige
Da kallo suka bi ta har Usman ɗin domin ya kasa ma motsa wa, “Why can’t she forgive him?” Ya tambayi zuciyar sa, sai kawai ya lumshe idanu hawayen ciki suna sauka a dandamalin fuskar sa
Hajiya ce tace mishi, “ya bi ta ɗakin ya rarrashe ta, tunda shi saɓo-tumaki ne da zai zauna yana mata kuka, kar ma ya fito ɗakin ba tare da sun daidaita ba”. Sannan ta tashi ta wuce nata ɗakin
Shima kuma sai ya miƙe yabi bayan Ɗahiran, sai da ya tura ɗakin ya shige kafin ya rufo ƙofan har da saka keey.
Nima dai na ware tunda an bar Ni a parlour. ????
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
بسم الله الرحمن الرحيم
⚖
FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
JIKAR LAWALI CE✍️
Wattpad: UmmuDahirah????
\F.W.A????/
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY
EPISODE Sixty Eight
A taƙaice please. Kuyi haƙuri sabida abubuwa sun yi min yawa dole zan taƙaita labari na daga nan, ba wai don ya ƙare ba, amma dai na san kowa na son jin ƙarshen labarin shiyasa zan taƙaita.
An kai ruwa rana kafin Ɗahira ta yarda ta koma gidan Usman, a lokacin cikin ta ya shiga wata na biyar ne
Sai da aka sake shagulgula isu-isu ƴan gidan kafin ta tare, inda aka gyara mata ko ina
A ranan dai Usman yayi kwanan farin ciki, yau ga shi ga Ɗahiran shi cikin sukuni, domin ta rigada ta sallama tuni ta yafe mishi komi ya wuce, tunda ta koma kuma biyayya take mishi kamar yanda aka santa, hakan ya ƙara jawo shaƙuwa me ƙarfi da ƙauna a tsakanin su
Inda Usman ɗin ya so su wuce TURKEY yayi hutun amarcin sa da ya ɗauka
Amma Kaka ya hana, ya ce, “dole sai ta haihu”.
Ba don ya so ba ya haƙura
Ita kanta Ɗahiran ma ba ta son zuwa sabida idan har suka je rayuwar da tayi a can ne zai dawo mata, amma bata ce mishi komi ba.
Cikin ta na wata shida Aunty Zulaiha ta haifi ɗan ta na miji, an yi suna inda yaron yaci sunan mahaifin mijin ta Aliyu, za su na kiran shi da Aiman.
Fannin Hajja Fatu kuwa don dole tayi ladab yanzu, domin ba kaɗan ba Abba yake gasa mata aya a hannu, duk wani jin daɗi yanzu yayi ƙaura a wajen ta.
Matsalan da Shakira take fuskanta wajen mijin ta Sahabi, zama dai ya ƙi daɗi, domin ashe har yanzu be dena bata ƙwayoyin hana samun ciki ba, ko ɓatan wata bata sake yi ba, sai da dubun shi ta cika ashe Allah ya bata ciki, daga baya da ya gane sai ya je ya siyo magani ya bata, ciki ya zube lafiya lau, duk a tunanin ta Allah ne ya ƙaddara hakan, domin yanda Sahabin ya nuna damuwarsa tsantsa dole ta cire tunanin komi, sai daga baya kawai ta kama shi yana waya da abokin shi, inda yake faɗa mishi komi "shi ne yake bata maganin hana ɗaukan ciki, don shi wlh be ƙaunar haihuwa yanzu sai nan gaba," sanadin da aka yi ta fitina kenan, daga ƙarshe dai aka raba auren dole duk da rai be so ba, amma su Big Dady sun ce, "dole sai ya sake ta, ya je can ya auro wacce ba ta son haihuwar". Ita kanta Shakiran hakan ya fi mata, domin burin ta yanzu kenan ta samu ciki, tunda ga shi duk ƴan uwan ta da yaran su, Fadila ma yanzu tana ɗauke da nata cikin, sai dai be kai wancan matsala ba, haka ma itama Aunty Zainab.
Ɗahira ta haihu lafiya ta samu Baby Boy, inda yaro yaci sunan Abbun ta, sunan Kaka kenan, Al’ameen, za su kira shi da sunan A’sim
An yi shagulgula an gama lafiya.
Sai kuma a lokacin ne aka yi bikin Firdausi ita da sauran ƴan uwan ta jikokin Granny, sun je sun kwana sun raɓashe.
Sai da Ɗahira tayi arba’in kafin suka tafi Turkay, satin su uku a can suka wuce Saudiya suka yi umra, sannan daga can suka wuce Dubai, sun yo wa ƴan uwa siyayya kala-kala inda suka dawo gida. Zaman su sai son barka, domin ƙauna tsantsa suke nuna wa junan su, gefe kuma ga ɗan su dake ta wayau tubarakalla.
Kwatsam sai aka wayi gari Kaka be da lafiya, ciwon kwana ɗaya don har ya samu sauƙi ma, ashe ciwon ajali ne, inda ya ce ga garin ku nan, mutuwar da ya girgiza ahalin nan gaba ɗaya, wanda sun daɗe basu manta bawan Allan nan ba.
Bayan wasu shekaru, yanzu Ɗahira har ta sake haihuwar ɗiyar ta mace me sunan Hajiya, Asiya, suna kiran ta da Huda.
Itama Fadila yanzu tana goyon ɗan ta na biyu ne me sunan Abbun su, duk ka yaran ta maza ne. Yusra ma ta sake haihuwar har da tsohon ciki yanzu. Shakira ta samu miji ta yi aure, sai dai a Zaria yake, kuma yana da mata ɗaya da yara biyu, suna zama lafiya babu wani hayaniya tunda yana da shi, kuma ya barta tana ci gaba da aikin ta. Itama Sa’adatu yanzu tayi aure a can Legos ɗin, har ta dawo da Zahra da tayi wayau Masha Allah, kamannin ta da uban ta sai ƙara fito wa yake yi, duk wanda ya kalle ta sai ya tuna da Baffa, Allah sarki rayuwa kenan.
TAMMAT BILLAH… ALHMADULILLAH.. ALHMADULILLAH.. ALHMADULILLAH… Duka-duka a nan na kawo ƙarshen littafi na, abun da na faɗa dai-dai Allah ya bani ladan, kuskuren da nayi kuma Allah ya yafe min
saƙon gaisuwa ga masoya na bazan taɓa manta ku ba, na gode sosai da nuna min ƙauna da kuka yi, Allah ya bar mu tare har a aljanna, Love You fisabilillahi.. taku JIKAR LAWALI ????????????❤️????