BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

         A haka ya zo ya tarar da ita zaune cikin ruwan aman tana ta rawan sanyi. Tunda ya shigo ya sauke idanun sa a kanta ya haɗe giran sama dana ƙasa yana jin zuciyar sa na sake ƙunci, take ya nufe ta gadan-gadan yana cewa, “baki ji abinda nace miki bane kafin in fita? Ke me taurin kai baza ki yi abinda nace miki ba ko?”

Ta ma kasa yin magana illa kallon sa da take yi, domin ji take yi idan ma ta tanka sa tabbas zuciyar ta zata buga da baƙin ciki, shiyasa ta rufe idanun ta tana jiran abinda zai yi mata

Tsawa ya daka mata yana cewa, “ki tashi ki gyara min gida ko in ci uwar ki a gidan nan”.

Sosai ta tsorata da tsawan da yayi mata, ta zabura zata tashi, sai dai ta kasa sabida rawan da jikin ta yake yi, da zaran ta yunƙura zata miƙe sai ta zame ta bugu a tyles ɗin parlour’n, hakan yasa ta fashe da kuka tana rawan baki, tana son furta masa baza ta iya ba amma ta kasa

Hannu yasa ya janyo ta kiiiiiiiii… ya ingiza ta cikin Toilet ɗin

“Maza ɗauki mopper ki gyara min gida ko in Yi biji-biji dake yanzu”. Ya sake daka mata tsawa

“Me..yasa.. ba ka da tau..sayi ne wai? Me.. me nayi maka.. ne? Ka bar Ni na koma ggida tun..da..” sai ta kasa ƙarisa wa saboda kukan da take yi

Idanun sa jawur ya aza kanta yace, “ai baki ga komi ba daga abinda na shirya miki, Ni dai kika aura ko?” Sai ya karkaɗa kai kafin yace, “Wlh daga ke har waɗanda suka aura min ke sai na sa ku kun yi dana-sani, kamar yanda kika ƙuntata min rayuwa, ke ma sai na ƙuntata miki”. Sai ya juya da ninyan fice wa, har ya fita ya dawo ya sake nuna ta da yatsa yace, “ki gyara min gida a karo na ƙarshe..” ya juya ya fice da sauri. Direct ɗakin sa ya wuce ya shige Toilet, shower ya kunna ya shiga ruwan na zubar masa daga sama zuwa ƙasan shi, zafin da yake ji a zuciyar sa ji yake yi kamar ana ƙara masa icce yana ruruwa, duk da ruwan sanyin dake dakan jikin sa, amma ji yake yi ko kaɗan babu sauƙi, dauriya me dauriya ya gwada yin sa amma ina, kawai sai ya fashe da kuka, domin ji yake yi idan be je ya kashe ta tsaban tsanar da yake mata ba, bazai taɓa sukuni ba, abinda yake ji tun ɗazu kenan amma ya kasa daure wa

Nan tunanin addu’a ya faɗo masa, ya soma lalubo abinda zai faɗa, daƙyar harshen sa yake iya faɗin, “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un…” Ya ƙame ƙam a wajen yana ci gaba da karanta wa a ƙasan zuciyar sa, ya daɗe a haka kafin ya soma jin abunda ke zuciyar sa yana lafa masa, daƙyar ya tuɓe kayan jikin sa ya yi wanka ya fito, a haka ya zube kan gadon sabida rasa inda yake masa daɗi a jiki.

      Ita kuwa baiwar Allah Ɗahira tunda ya bar ta take kukan ta, sai da tayi ma’ishi kafin ta yunƙura ta tashi, a duƙe- a duƙe ta soma kwatanta aikin ko zata iya, har dare ya tsala tana abu ɗaya, gaba ɗaya ta gama jiga ta, har faɗi take yi tsaban wahala, sai ta tashi taci gaba, aikin da zai ɗauke ta mintoci, sai ga shi ta shafe tsawon daren tana yi, daga ƙarshe ta zube a ƙasa tare da rufe jikin ta, taci gaba da rawan sanyi, bata ko runtsa ba sabida azaban ciwo, a haka safe ya cin mata, zuwa lokacin baza ka taɓa gane Ɗahira ce ba, sabida yanda gaba ɗaya ta zabge tayi wani irin muguwar rama, idanuwan nan nata sun sake fito wa sun koɗe sun yi zawur, dama ga ta ba auki ba haka ta sake sirance wa gunun tausayi, tamkar wata ƙaramar yarinya ce a kwance a wajen

Har haske ya gama fito wa bata iya tashi ba, yunwa ke addabar ta amma ta kasa yanda zata yi ta nemi abinci, jikin ta yayi zauu kamar garwashin wuta, sai karo take yi da haƙora.

        A haka Usman ya fito da shirin sa, tunda ya kalli inda take sau ɗaya ya tabbatar da ta gyara wajen, sai ya ɗage kai yai ficewar sa.

   Lumshe idanuwan ta kawai tayi tana sake lafe wa a ƙasa, bata san wani tunani ya kamata tayi ba, bata taɓa tunanin akwai wani rayuwa da zata iya shiga har taji tana ƙaunar mutuwar ta ba, sai a wannan gaɓar, tayi dana-sanin amince wa da auren nan, tabbas da tasan irin azabar da zata tarar kenan; da tayi guduwar ta, da dai ace ta zauna da wannan mara tausayin, ko kaɗan bata taɓa tunanin ƙiyayyar da yake mata ya kai har haka ba, da ya gummaci ganin mutuwar ta da rayuwar ta, tabbas yau tana kaico da rayuwar ta da ta kasance a ƙarƙashin maƙiyin ta tana me neman lahirar ta, kuma bata da hanyar da zata iya kufce wa hakan

Sai ta sake fashe wa da wani irin kuka me ban tausayi dake fito wa daga can ƙasar zuciyar ta yake ƙara mata raɗaɗi da ƙunci me ciwo, tuna wa da tayi da iyayen ta, sai dai ga shi tayi musu nisa babu yanda za’a yi ta fita ta koma gare su, suna can ba tare da sun san halin da take ciki ba. Tasha kukan ta ma’ishi babu me rarrashin ta, inda ta wuni curr a kwance bata san inda kanta yake ba, domin kuwa wani sabon zazzafan zazzaɓin ne ya sake rufe ta, abun ka da bata saba da damuwa a rai ba, haka ta wuni zuciyar ta na mata zafi kamar ana soya mata, daƙyar take iya numfashi, har dare kana wani wahalallen barci ya sure ta, wanda be da maraba da suma, domin kuwa gaba ɗaya numfashin ta ba ya fita da kyau, idan ta ja numfashi sau ɗaya; sai ta shafe fiye da second biyar kafin ta sake jan wani.

             *

           Sai wajen ƙarfe 10:40pm. Usman ya shigo gidan, be kalli inda take ba ya wuce kai tsaye ɗakin sa, zama yayi gefen gadon sa yana zare Cumbas ɗin ƙafafuwan sa haɗe da socks ɗin, yana gama wa ya cire wrest watch ɗin hannun sa ya ajiye, sannan ya miƙe ya kwaɓe kayan sa ya shige Toilet, wanka yayi ya fito ɗaure da alwala, sallan isha’i yayi da be samu yayi ba, sai ya koma kan sofa ya zauna yana latsa laptop ɗin sa, har yayi kamar mintuna biyar, ko me ya tuna ya miƙe ya ɗauko wayan sa dake ajiye gefen bed side, ya soma latsa wa, kai tsaye WhatsApp ya shiga yana bincike a kan sakon da Friend ɗin sa ya turo masa, a nan tunanin mutanen gida ya faɗo masa, sai ya ɗan dakata yana kame goshin sa, shaf ya manta da wani kiran gida a rayuwar sa, ga shi har suna son wuce sati ɗaya da barin gida ba tare da ya kira ba, tabbas ya san akwai matsala, domin ya san yanzu haka suna nan sun damu, duba da yanda ba shi kaɗai bane ya taho. Tsaki yaja yana fita daga WhatsApp ɗin, shiru yayi yana tunanin Numban wa zai kira

Still tsakin ya kuma ja tuna wa da yayi ba Numban sa da yake amfani bane a wayan, tabbas ya san sun neme sa ba su same sa ba, Kai tsaye Numban Hajiya ya rubuta ya kira

Tana ɗauka abin da ta soma tambayar sa, “shin ina ya shiga tsawon wannan lokacin be kira su ba?”

Be bata amsa ba, sai ya soma gaishe ta a daƙile kamar yanda ya saba

Amsa wa tayi tana sake jeho masa tambayar farko

Sai yace mata, “wai be samu time bane, sabida ya koma Hospital ɗin da yake aiki yana ci gaba da zuwa har sanda za su dawo”.

Ajiyan zuciya kawai ta sauke, ko kaɗan bata damu ta san halin da Ɗahira ke ciki ba, sai ce masa tayi “to yaushe kenan kake sa ran dawowa?”

“Kamar nan da Two months”.

Dogon tsaki taja, cike da ɓacin rai tace, “wato ta shanye ka shi ne zaka kai har wannan lokacin baka dawo ba? Uwar me kuke yi da baza ka dawo ba sai ka kai lokacin nan?”

Shiru yayi mata be tanka ba

Kamar yanda itama bata sa ran zai tanka ɗin ba, amma sai ta sake cewa, “ina magana kayi min shiru, ko cin amarcin ne har yanzu baka gama ba sai zuwa nan da two months ɗin?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button