FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Shi kuma ya amsa ya tusa cikin aljihu, be ce komi ba ya juya yayi ficewar sa
Girgiza kai kawai Doctorn yayi a ransa yana cewa, “Dr. Man problems”. Sai ya mayar da idanun sa kan Ɗahira dake barci tana fitar da numfashi a hankali, dayake yayi mata alluran barci ne, da alamun dai ta fara jin daɗin yanayin ta sabida yanda numfashin nata yake fita, kau da kai yayi kanta yaci gaba da aikin gaban sa.
Zuwa dare ta farka, duk da jikin babu sauƙi sosai, amma tunda tana ƙarƙashin kulawar likita ne tafi da, an sauya mata ɗaki ita kaɗai ce.
Da safe ko da Usman ya zo Hospital ɗin ko zuwa duba ta be yi ba, kasancewar asibitin da yake aiki ne
Doctor Shamel har office ya bi sa yana masa maganar Ɗahiran, da kuma yanda ya ga be je ya duba ta ba
Amma Usman ko bi ta kansa be yi ba, ce masa ma yayi “kar ya ƙara masa magana idan har ba sallaman ta zai yi ba”.
Shi dai Doctor Shamel sosai yake mamakin wannan hali na Usman, ya san dai yarinyan tabbas ƙanwar sa ce, duba da yanda suke mugun kama, amma kuma abinda be sani ba “meye ta zo yi nan?” Shi ne abin da ke masa yawo, duk da ya san Usman ɗin ya bar Hospital ba ya aiki, dama yana mamakin dawowar sa da cewan “zai yi two months a ƙasar, that’s why ya dawo aiki kafin ya tafi,” to amma kuma yana kyautata zaton akwai abinda suka zo yi da ƴar uwan tasa. girgiza kai kawai yayi ya cire tunanin a ransa tunda be shafe sa ba. Sosai yake ba wa Ɗahira kula wa, inda take samun sauƙi a hankali
Gefe ɗaya kuma Big Dady ya kira har sau biyu don yaji jikin ta, amma sai Usman yayi masa ƙaryan “tana barci” don yaƙi haɗa su
Abbu ma ya kira tunda Big Dady ya basa Numban Usman ɗin, shima the same haka yace masa, “she was asleep at the time.”
Sanda Big Dady ya sake kira, a lokacin Ɗahira tayi kwana biyu a asibitin, sosai ta samu sauƙi sai dai abinda ba a rasa ba, a lokacin ne Usman yaje har ɗakin nata ya bata wayan su gaisa da Big Dady
Lokacin Ɗahira na kwance ta juya wa ƙofa baya, tana sanye cikin fararen kaya na mara sa lafiyan Hospital ɗin, tunani me zurfi take yi idanun ta a buɗe ta ƙure wa waje ɗaya ido, babu abinda take kitsima wa illa yanda zata gudu daga Hospital ɗin nan a yau
Shi kuwa shigowar sa Direct gaban gadon ya isa, ya tsaya yana bin bayan ta da kallo, sai ya ɗauke kai yana haɗiyar yawu cike da ƙunci a zuciyar sa da ya rasa shi kwana biyu, tamke fuska yayi sosai kana yace, “keee”.
Hakan yasa ta ɗan yi firgigit ta dawo hayyacin ta, sai tayi saurin juyo wa tana kallon sa, sosai ƙirjin ta ya buga saboda kawai sauke idanun ta da tayi a kansa, zuciyar ta nan da nan ta sauya bugu kamar zata faso ƙirjin ta tsaban buga wa da ƙarfin da take yi. Ƙyafta idanu ta hau yi sai tayi saurin janye su daga kallon sa, sakamakon kallon da yake sakar mata da yanda take ji
Shima be ce komi ba illa latsa wayan sa da yayi ya kira Big Dady, ya miƙa mata ba tare da ya ce uffan ba
Ɗan ɗago kai tayi ta kalli wayan, kana kuma ta saka hannu ta amsa tana me kara wa a kunne, a lokacin Big Dady ya amsa call ɗin yana faɗin “Hello Daughter”
Kallon sa tayi ganin yanda ya tsaya mata ƙiƙam kamar zai faɗo mata, sai dai ya mayar da fuskar sa na mara sa mutunci, wanda kamar ƙiris yake jira. haɗiye yawu tayi tana sauke kai ta amsa da “na’am Dady”. Cikin sanyin murya irin na mara sa lafiya
Nan Dady ya soma tambayar ta jikin ta
She replied, “Very easily Daddy, sai dai missing ɗin ku da nake yi”.
Murmushi yayi yace, “kar ki damu Daughter ai kun kusa dawowa, ke dai kawai ki kula da jikin ki kinji? ba na son in sake jin an ce min baki da lafiya, na san halin ki idan kin saka damuwa ne a ranki yake saka ki ciwo, duk idan kin ji wani abu na damun ki just tell your brother kinji?”
Lumshe idanu tayi wasu zafafan hawaye suna zubo mata, lokaci ɗaya ta gyaɗa kanta kamar yana ganin ta, cikin raunin murya tace, “to..” tana datse baki jin kuka na son kufce mata
“Yauwa Daughter, bari in ba wa Abban ki ku gaisa, muna tare da Baba ne (Kaka)”.
“To”. Ta sake amsa wa cike da murna, domin sosai take son jin muryan kowa a gidan su, musamman Maman ta da Abbun ta, tayi kewar su matuƙa
Gaisa wa suka yi da Abba, inda shima ya tambaye ta jikin ta, sannan yayi mata nasiha sosai a kan biyayya ga miji, tare da ƙara haƙuri a rayuwa
Ita dai jin sa kawai take yi, a ranta tana jin kamar ya san halin da take ciki, “ina ma zata iya sanar da su halin da take ciki?” Amma tsoro da fargaba ya hana ta furta abinda take son faɗa
Daga nan Kaka ya amshi wayan, sun jima suna waya, inda take ta mishi shagwaɓa a kan “ita lallai lallai tana son dawowa gida ta gan shi” sosai take kuka a wannan lokacin domin ta kasa tsayar dashi
Usman dake tsaye yana kallon ta, hannu ya saka ya dalla mata a gefen kumatu
Inda ta saki ƙara tana ƙara ɓare baki
Kaka da duk ya ɗauki abin nata kawai tsaban rigima ne irin nata, sai yayi dariya yace, “ki yi haƙuri Mata ta, duk da kina kewa ta amma na san Real Mijin ki ya fi Ni buƙatar ki, ki yi haƙuri har ku dawo kinji? nima nayi kewar ki sosai, ji nake yi kamar in biyo ki nima”. Shima ya ƙare maganar ta sigan wasa
Kuka ta sake fashe wa dashi, tana shirin magana Usman ya ƙwace wayan
Inda ya kara a kunne yana cewa, “wai tsoho meye haka kake saka ta kuka?” Ya ƙare maganar da dalla mata harara
Ita kuwa sake fashe wa da wani sabon kukan tayi
hakan yasa ya saka hannu ya damƙe mata baki tare da hancin ta
Zaro idanu tayi ganin zata shiɗe, nan da nan ta soma kokawar cire hannun sa tana son shaƙar numfashi, amma ina ya saka ƙarfi sosai ya tamke ta yanda baza ta iya ƙwace wa ba, sai uhmmm.. uhmmmm take yi tana dukan hannun nasa, tare da sake ware idanun ta dake tsiyayar hawaye sosai
Tsaki yaja yana sauraron Kakan dake masa tsiya, a daƙile yace, “kar ka cinye min kuɗi na sai an jima”. Ya katse kiran ba tare da ya jira cewar sa ba. Maida hankalin sa yayi kanta yana kallon ta da fuska a ɗaure, sai kuma ya janye hannun sa yana sake sakar mata wani banzan kallo
Ita kuwa cikin kuka tace, “wai don Allah me nayi maka da zafi haka da kake son kashe Ni? Idan har ka tsane Ni ne meyasa baza ka ɗauki wuƙa ka daɓa min ba a kan wahalan da kake ba ni?” Cikin tsawa ta sake cewa, “ka sake Ni mana tunda ba ka ƙauna ta, wlh nima ba na son ka ko kaɗan, I hate you more than anyone in this world! Sai Allah ya saka min bazan taɓa yafe maka ba! I hate you so much USMANNN”. Ta ƙare maganar da wani irin kuka me ban tausayi
Sosai ransa yayi mugun ɓaci da maganganun da ta faɗa masa, ba kaɗan ba yaji ɗacin yanda take kallon ƙwayar idanun sa take sanar masa ba ta ƙaunar sa, “ita wace ce da ta isa ta kalle sa ido cikin ido tace masa ba ta ƙaunar sa” a zuciye ya saka hannu da ninyan cafke mata gashi, sai wayan sa ta soma ƙara, wanda hakan ya dakatar dashi yana bin wayan da ido
Mahaifin ta ne ya kira, sai ya ja dogon tsaki yana daka mata tsawa.
????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????