BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

.

        EPISODE Forty Six

        “Wlh idan baki rufe min baki ba sai nayi ƙasa-ƙasa dake a nan, bar ganin kina kwance a nan sai na ɓalla miki ƙasusuwa, mahaifin ki zai yi magana da ke, idan kika sake kika yi wani motsin da zai sa ya gane wani abu.. uhm wlh I will teach you a lesson”.

Cak ta tsayar da kukan nata jin ya kirayi mahaifin ta, da sauri jikin ta na rawa ta kai hannu ta amshi wayan da yake miƙo mata, muryan mahaifin ta taji ya doki kunnen ta, sai ta lumshe idanu tana me tsiyayar da hawaye, cike da sanyin murya take gaishe sa zuciyar ta cinkushe da kewar sa

Nan ya tambaye ta jikin nata?

Ta amsa mishi tana faɗin, “taji sauƙi sosai”. Kana ta soma jero masa tambayan “ina su Maman ta da su Umma? Har Fadil sai da ta tambaya”

Abbu yace mata, “babu su Fadil kusa, amma ga Maman ta su gaisa”.

Jin muryan Maman ta sai ta fashe da kuka tana me kiran sunan ta

Daga can Aunty Amarya tace, “har yanzu dai kin kasa girma ko? Kukan na mene ne?”

“Nayi kewar ku ne sosai Mama, don Allah ki saka baki ya dawo dani”.

Aunty Amarya ta gane wa take nufi, sai tace mata, “ke baki da baki ne? Duka-duka yaushe kuka tafi? Idan kin yi haƙuri nan ba da jima wa ba kamar yau ne za ku dawo, Allah ya muku albarka baki ɗaya”.

“Amin Mama”. Ta amsa ta tana me share hawayen ta da bayan hannu

Daga nan Aunty Amarya sallama tayi mata

While Usman ya amshi wayan sa, sai da suka yi magana da Abbu kafin ya kashe wayan. Ya dube ta fuska a tamke yace, “tashi mu je”.

Ko kallon sa bata yi ba, illa sake haɗe kai da gwiwa da tayi ta saki wani Marayan kuka, domin wayan nan da suka yi ba ƙaramin fama mata zuciya yayi ba, sosai take kuka kamar ana yanka ta, har wani shashsheƙa take yi

Hakan yasa ran Usman yayi mugun ɓaci, ya daka mata tsawan da ya razana ta lokaci ɗaya

A dai-dai lokacin ne Doctor Shamel ya shigo ɗakin, da mamaki yake bin Usman da kallo, sai yace, “what’s going on?”

“Ka bamu sallama zamu wuce gida yau”.

Murmushi Doctor Shamel yayi, cikin harshen turanci yace, “my friend ban da abun ka ka barta mana ta samu sauƙi, ka ga har yanzu da sauran rashin lafiya a tare da ita”.

Usman be kalle sa ba ya saka hannu ya riƙo nata, jan ta ya soma yi dole ta sauko a kan gadon tana ci gaba da kuka

Dr. Shamel yace, “Oh Man, leave her. Don’t hurt her. You see her crying. Maybe it’s her body.”

Shi dai be saurare sa ba tuni yayi waje da ita, be sake ta ba har sanda ya isa da ita motan sa, ya buɗe mazaunin gaba ya tura ta ciki, sannan ya rufe ya saka lock

Babu abinda Ɗahira take yi sai kuka tana me tsine masa a zuciya, har ya koma cikin asibitin ya dawo bata dena kukan ba

Yana shigo wa ciki ya daka mata gigitacciyar tsawar da dole ta ɗauke kukan cak a lokaci ɗaya

Be yi magana ba ya kunna motan ya nufi bakin Gate, sosai zuciyar sa take masa ƙunci, gaba ɗaya jin sa yake yi babu daɗi, yanda yayi ta ɗaga mata murya yana mata tsawa sai duk hakan ya saka masa ciwon kai, hakan yasa ransa ya sake ɓaci matuƙa, a wuya kawai yake yana jiran yayi maganin ta

Sai dai Allah be sa ta sake ko ƙwaƙƙwaran motsi ba, illa ajiyan zuciya da take ta sauke wa idanun ta a lumshe, yayinda ta ɗaura kanta saman cinyoyin ta.

     Suna isa gida tana jin ya tsayar da motan ta ɗago kai, sai ta buɗe motan ta fice da sauri, tana jin sanda ya ja dogon tsaki amma ko bi ta kansa bata yi ba, haka ta nufi ciki da sauri, sai dai dole ta tsaya har sai da ya zo ya buɗe ƙofan, jefa mata magungunan ta yayi dake cikin leda, sannan ya buɗe ƙofan, sai da ya tasa ƙeyan ta ciki kafin shima ya shiga

Tuni ta isa wajen kayan ta ta nemi wuri ta zauna saboda har yanzu tana ɗan jin jiri

“Ki gyara min gida tunda ke ƙazamiya ce, daga yau ba na son in sake ganin baki yi aikin da ke kanki ba, sannan wankin kaya na suna nan ki wanke min su na zuba miki a kan gado na, akwai igiyar shanya cikin Toilet ɗina ki shanya a ciki”. Yana gama maganar yayi waje ya fice, tare da rufe ta ta waje

Lumshe ido kawai tayi tana me jingina bayan ta da bango, sosai ranta ke suya sai dai babu yanda ta iya, ta san haka zata ƙare da uƙuban sa har sanda Allah zai yi su koma, “yau har akwai ranan da wani zai iya buɗe baki yace mata ƙazamiya?” Sai ta ɗan yi murmushin da yafi kuka ciwo tana me buɗe idanun ta, babu yanda zata yi dole ne tayi masa abinda yace, ko da kuwa wani ciwon ne zai kama ta, domin dai ta san wulaƙancin da zata fuskanta sai yafi halin da take ciki.

      Sai da ta ɗan samu hutu sosai, kana ta tashi ta shiga kichen, tea ta haɗa me kauri ta zo ta buɗe magungunan ta, inda ta cire Waɗan da zata sha, ta shanye da tea ɗin, sannan ta miƙe ta wuce ɗakin sa, gaba ɗaya babu ƙarfi a jikin ta, amma haka ta daure ta kwashe wankin da ta gani a saman gadon, Allah yasa ba masu yawa bane, ta nufi Toilet da su, akwai engine machine a ciki, amma ko da ta gwada yi a ciki ya ƙi yi; domin ya lalace. Sai ta cire ta saka a bucket, komi na buƙata akwai a wurin, haka ta zauna ta wanke masa tas har Singlet da ƙananan wanduna, zuciyar ta na tafarfasa har ta gama, shanya masa tayi kana ta fita ta je ta kwaso nata ta wanke a Toilet ɗin, sannan ta shanya a Toilet ɗin Parlour, tana gama wa ta gyara masa ɗakin sa, duk da babu datti sai dai gadon da ya yamutsa

Bayan ta gama ta share Parlour ta Yi moping, zuwa lokacin gaba ɗaya ta gama gajiya, kamar dai wani zazzaɓin ne ke son kama ta; tunda bata gama warke wa ba, zama tayi ta huta sannan tayi alwala ta gabatar da sallan azahar, kasancewar sauran sallolin da ake bin ta duk tayi su a Hospital, sai ta ɗan kishingiɗa zuwa sallan Asar.

     Sai biyar ta farka, nan kuwa ta sake jin daɗin yanayin ta, wanka tayi tare da Sallah, ta shiga kichen ta yi ma kanta girki sannan taci ta koma tayi shimfiɗa ta sake kwanciya, tana nan tana tunani har magriba tayi, sai da tayi sallah kafin ta soma muraji’ar Al’ƙur’ani, da kai take yi domin bata san inda zata samu ƙur’ani ba, dayake akwai hasken NEPA ko ina, hakan yasa ta ɗan ji daɗin zaman bata ji tsoro ba, sai da aka yi isha’i kafin ta kwanta tayi lamo, yanda tunani ya cika mata zuciya sai ta tashi zaune ta ɗauko ruwa ta sha magungunan ta, sannan ta haɗa dana barci da aka saka mata, sai ta koma ta sake kwanciya, babu daɗe wa barci ya sure ta, dama haka tafi so domin ba ta ƙaunar ya dawo ta ganshi.

     Sai goma na dare kamar yanda ya saba dawowa ya dawo, be bi ta kanta ba ya shigewar sa ɗaki, shima shirin barcin sa yayi ya kwanta abin sa.

            WASHE GARI

     Sai da ta bari ya bar gidan kafin ta tashi tayi wanka ta shirya cikin riga da skert na atamfa, sai ta saka Baby Hijab ta shiga kichen, Breakfast tayi wa kanta taci ta koma ta zauna, yanda ta ga babu abinda take yi sai zaman banza da tunani, hakan yasa tayi ta karatun Alkur’ani, kasancewar ta ba ma’abociya son kallo ba, ko kaɗan be dame ta ba, idan har ba wani ya kunna ta zo wurin ba, to ko kaɗan ba ta bi ta kai bare ta tuna dashi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button