HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Sunfito yiwa Umma sallama suka iske d’akin da bak’i masu zuwa ,gidan har yafara shiga yanayin biki ,ga Babangida zaune Umma nabashi kud’in d’inki zai karb’o mata ,mutane na ganinsu akafara amare amare ,haushi Yakama Hussaina ,itafa gabad’aya jitake kamar ma kar tayi auren ,Hassana kuwa murmushi tayi suka gaida jama’ar gurin sannan sukayiwa Umma sallama .
Babangida yace ” Ku tsayani mutafi hanyarku zanyi nima fa ,nakai mashin d’ina gyara mota zan hau”Hassana tace “ka karb’i na ya safwan mana ” ya mik’e yana cewa “ya safwan Baba ya aikeshi nefa ,kuma mashin d’in ya hau ” har sun juya sai Usman dake zaune yace “Adda zan biku ” Hassana ta tsura masa ido tace “ka zauna kataya Umma aiki Usman !wannan tafiyar babu kai acikinta ” baiyi musu ba yace “toh Adda adawo lfy ,Allah yatsare hanya ” har sunfita tsakar gida Hassana takuma dawowa takalli Umma sosai tace “Umma bakida sak’o…!?Umma tace ” sak’on me Hassana …!?Hassana tad’an d’aga kai sama kamar me tunani ,sai kuma ta sauke kanta a fuskar Umma tace “nazaci zaki bada sak’o gun Aunty sakeena ne ….!?Umma tace ” banida sak’o wallahi kutafi Allah ya tsare”Hassana tace “Ameen Umma mun tafi ” Umma takuma cewa “asauka lafiya .
Suna fitowa waje kawai sai ganin Hamma sageer sukayi ,Hassana ta d’age nik’ab d’inta tana murmushi tace” yanzu Hamma sageer dawowa kayi …!?d’azun nan fa kazo katafi ….gashi dai kakoma gidan Mamma amma baka gajiya da zarya ko …..!?sai ya d’an karya wuya yana k’arewa fuskarta kallo yace “ahaf daman nasan abinda zuciya ta tafad’amin gaskiya ne ..” Ta gyara tsayuwarta tace “me tagaya maka !?ya d’an matso yana Shafa kai yace” tacemin ga sweetyn ka can tana shiryawa zata fita unguwa ,shinefa nayi saurin tawowa na kaiki saboda kar wasu mazan su ganemin ke “Babangida da Hassana sukayi dariya ,yayunda Hussaina taja gefe can ta juya musu k’eya ,batason ganin sageer ko kad’an ,laifinsa yak’ara yawa saboda zai d’auke mata rabin ranta.
Sai sannan Hamma sageer ya lura da Babangida ,Babangida ya gaisheshi yana Sosa k’eya ,sannan ya juya yana kallon Hassana yace ” sis ,bari intafi kawai ,sai kundawo “Hamma sageer ya tambayeshi inda zashi sai Babangida yace ” zani karb’owa Umma d’inki ne “Hamma sageer yace ” bari mu ajiyeka k’anina ,sweety kuzo mutafi mana… “Hassana tad’anyi far da idanu tace” gidan Hamma sulaiman zaka kaimu …wai za’ayi mana k’unshi ne …”shima yayi murmushi zaiyi magana kawai sukaga Hussaina tayi gaba tafara tafiya.
Da sauri Hassana tabita ta rik'o hannunta ,ta kalleta ido cikin ido tace "ina Neman alfarmar kizo Hamma sageer ya kaimu a motarsa idan har na isa dake ..." Jikin Hussaina yayi matuk'ar sanyi sosai ,bada niyyarta ba kawai Hassana taja hannunta takaita har gaban motar ,ta bud'e tasaka Hussain a ciki ,Babangida ma yashiga baya kusada Hussaina ya zauna ,Hamma sageer da Hassana suka shiga gaban motar.
Sun fara tafiya Hussaina dai tayi muk’us a baya ,fuska lullub’e cikin nik’ab ,idanunta ne kurum a waje,haka nan batajin dad’in jikinta ,ko Babangida da yakemata magana banza tayi masa,shiyasa shima yarabu da ita, sun kawo Babangida dai dai shagon da zai amshi d’inkin Hamma sageer ya tsaida motar, Babangida na shirin sauka ya dakatar dashi ya d’ebo kud’i masu yawa ya juyo ya mik’awa Babangida yace”ga kud’in d’inkin Umman to “Babangida ya d’an zaro idanu yace ” Hamma sageer ai Umman tabani kud’in kagansuma a aljihuna “yafad’a yana k’ok’arin d’ebo kud’in a aljihunsa,sai ya dakatar dashi yace”ka mayarwa da Umma kud’inta ,ka karb’o mata da wad’annan ” tilas Babangida ya karb’a yana godiya ya fice a motar.
Hamma sageer na k’ok’arin yin kwana suka had’a ido da Hussaina ta galla masa harara da idanunta ,inda shima ya b’alla mata harara da nasa idanun.
A k’ok’arinsa nayin kwana wata mota ta tawo da mugun gudu kamar zata tashi sama ,cikin k’iftawar ido ta banke motar Hamma sageer da mugun k’arfi ,kafin kaceme gaba d’aya motar tafara wani irin gangarawa a gefen titi kafin takife da Hamma sageer da Hassana da Hussain a a ciki…….????
A gigice Babangida ya waiwayo dab da zai Shiga shagon d’inkin ,cikin matuk’ar gigicewa da rud’ewa da fitar hayyaci ya d’ora hannu aka ya k’wala wani mugun ihu da fad’in “innalillahi wa inna ilaihir raji’un…….????”
Comment
Share
Vote
Pls
HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
TYPING????
???????? HASSANA ????????
*DA*
❣???? HUSSAINA ????❣
TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
page4⃣1⃣to4⃣2⃣
WATTPAD:hassana3329
® PEN : WRITERS ASSOCIATION
~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~
TUNASARWA????
MANZON ALLAH (S A W )YACE”ALLAH YACE A HADISIN K’UDUSI “DUK WANDA YA NUNA K’IYAYYA GA MASOYI NA ,TO INAYI MASA SHELAR YAK’I DANI
AIKI ME FALALA????
MANZON ALLAH (S A W )YACE” KA YAWAITA YIN SUJJADA GA ALLAH ,DOMIN BABU LOKACIN SA ZAKAYI SUJJADA FACE SAI ALLAH YA D’AUKAKA DARAJARKA ,YA KUMA GOGE MAKA ZUNUBAI,”SALLAR NAFILA DA MUTUM ZAIYI YAYINDA BABU MAI GANINSA,YAFI SALLAR DA ZAIYI AGABAN MUTANE DA DARAJA ASHIRIN DA BIYAR
Ihun Babangida ne yafito da mazan dake cikin shagon da gudu Dan ganin meke faruwa ,da hanzari suka isa ga motar inda da k'yar aka zak'ulosu ,Babangida banda kuka cikin gigita babu abinda yakeyi .
Sanda aka cirosu k'ark'ashin motar Hamma sageer da Hussaina a sume suke, jikinsu duk jini saboda ciwukan da sukaji ,amma ita Hassana babu ko k'warzane ajikin ta illah matuk'ar buguwa da tayi a k'afafunta da cikinta ,kuma bata suma ba sai dai da k'yar take iya bud'e idanunta ,bakinta yanata motsi tana ambaton Allah .
Babangida yayi kanta hawaye sharaf sharaf yana ambatar sunanta ,ya kamata ya rungume ajikinsa yanata kuka, cikin zafin ciwo me ratsa k’wak’walwa tayi magana a hankali ,saida Babangida yasa kunnensa akan bakinta sannan yaji abinda take iya fad’a ,muryarta bata fita sosai take ambatar “Hamma sageer da sisina ,Ku dubaminsu Allah yasa babu abinda ya samesu ” Babangida na matuk’ar kuka yace “sister gasunan …gasu a gefenmu basu cikin hayyacin su ” ta runtse idanu hawaye ya b’ulb’ulo kamar famfo bakinta na motsi take furta “subhanallah !inna lillahi wa inna ilaihir raji’un “
Mutanen ne suka sunkuyo kan Babangida da yake zaune rashe rashe rungume da Hassana a jikinsa ,can gefe kuma sun janye Hamma sageer da Hussaina, d’aya daga cikinsu ne yake tambayar Babangida “ka sansu ne …!?cikin kuka Babangida yace ” eh ,yayyena ne “yace ” subhanallah toh yakamata muyi hanzarin kaisu asibiti ,kaga wad’ancan sun zubda jini da yawa sosai ,numbar wa zaka bamu mu kirawo a gidanku …!?Babangida dake faman kuka ya kasa magana saboda shi gabad’aya kansa ma ya kwance yakasa tuna numbar kowa ,sai Hassana ce cikin matuk’ar k’arfin hali tajawo kunnen Babangida dai dai bakinta ,cikin muryar da bata fita sosai tace “kabasu numbar Hamma sulaiman kaji ” yana kukan ya tallabe fuskarta yace “Kaina ya kulle ,bazan iya tuna numbar ba wallahi ,sannu ,sannu kinji …” Ya kuma fashewa da kuka ,a hankali itama hawayen ya ratso idanuwanta takuma cewa cikin k’aramar murya “kadena kuka Babangida ,karb’i wayar a hannunsu nagaya maka numbar sai ka kirashi ,numbar tana kaina na haddaceta ” da sauri Babangida ya amshi wayar hannun mutumin Hassana na fad’a masa numbobin ,da k’yar yake iya dannawa saboda hawayen dake shatata sun hanashi ganin madannan wayar sosai ,har yagama sawa ya danna kira ,ta dad’e tana ringin kafin Hamman ya d’aga cikin nutsattsiyar muryarsa yayi sallama .
Cikin yanayin tashin hankali Babangida yakuma fashewa da kuka yace "Hamma sulaiman mun shiga uku ,wayyo Allah Nah !Hamma sulaiman dake zaune a office d'insa suna tattaunawa shida Hamma Aminu akan d'aurin auren ,yaji muryar Babangida cikin yanayin kuka ,cikin rud'ewa yake tambayar Babangida abinda yafaru ,amma ina Babangida yakasa magana sai gurshek'en kuka yakeyi " sai mutumin ne ya amshi wayar yayiwa Hamma sulaiman bayani ,yakuma fad'amasa inda abin yafaru ,k'arshen gigicewa Hamma sulaiman ya gigice ,cillar da wayar yayi ya fizgi hannun Aminu yanata maimaita "innalillahi wa inna ilaihir raji'un ,Aminu d'auko motarka mu hanzarta ....subhallah ...lahaula wala k'uwata illah billah ...!
Aminu da ya fahimci zancen shima a rud’e yake gabad’aya ,Hamma sulaiman yashiga motarsa ya tasheta da mugun gudu ,yayinda Hamma Aminu shima yashiga tasa ya rufa masa baya, cikin mintoci kad’an suka isa gun saboda gudun da suka tafka ,da matsanancin gudu suka bud’e motocin suka fito ,mutane cike dank’am agurin ana jajantawa ,me motar da ya bankesu kuwa ko tsayawa baiyi ba ya gudu daman .
Hamma Aminu yayi kan su Hussaina yana kallon yadda goshinta ke fidda jini ,tana kwance samb’al a sume ,ga Hamma sageer shima jikinsa duk jini da hannunsa da ke karye ,ko alamun numfashi babu ajikinsu ,hannu kawai Aminu yad’ora aka yafad’i agabansu yana zubda hawaye da ambaton Allah .
Shikuwa Hamma sulaiman gun Hassana da Babangida yayi ,da Sauri ya tarairayo Hassana dake jikin Babangida ya d’agota ,cikin tsananin ciwo ta bud’e idanunta ta kalli Hamma sulaiman ,saita kamo hannunsa hawaye ya zubo mata ,a hankali take k’ok’arin nuna masa inda su Hussaina suke ,tace “Hamman mu kazo …!?Hamma nakasa tashi in taimaki sisina da Hamma sageer …inaji ina gani k’afafuwana sun kasa motsi Hamma …Dan Allah katemaka musu Hamma sulaiman ” wani irin ciwo ya murd’eta ta runtse idanu zufa na yanko mata ,cikin yanayin azaba tace “inajin kamar ana sossoka min wuk’a a cikina …amma karka damu dani Hamma …kaje kafara kulamin da wad’ancan mutanen masu daraja a zuciya ta ,don Allah Hamma ” Hamma sulaiman dai yazama mutum mutumi ko motsi yakasa banda zuba mata idanu da yayi cikin gigita da kid’ima,da wani ciwo ya murd’eta kafin kaceme ta sume a jikin Hamma sulaiman itama.