HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaba tayi tanawa Umma sallama yabiyota a baya, duk gidan da jama’ar biking and’ad’e antafi gun dinner .

   A soro sukayi kacib'us da Hamma Sageer yana niyyar shiga gidan ,D'an kaucewa yayi yana Sosa k'eya ganin Hamma Sulaiman yad'an russuna yana kwasar gaisuwa ,hannunsa Hamma Sulaiman yarik'o yana girgizawa da fad'in "ango ango ,ango kasha k'amshi gabad'aya matarka ta dameni tasani fitar da ban shirya ba ...."

Hamma Sageer yayi k’asa da kai yana murmushi da satar kallon Sweetynsa tauraruwa me haskakawa a zuciyarsa ,Hamma Sulaiman ya saki hannunsa yafice daga soran yanufi wajen dalleliyar motarsa yana shirin bud’ewa ,yayinda yakewa Hamma Aminu magana akan ya juya tasa motar su tafi wadda Hussaina da Ya Abdurrahman ke baya a k’ame sai shan hirar soyayya sukeyi k’asa k’asa ,sai Sadiya da ke zaune gaban mota ta hard’e ,Dan Abdurrahman da cewa yayi Aunty sadiyar tashiga wata motar bazasu tafi tare da itaba ,Hamma Aminu yace wallahi bai isa ba k’afarsa k’afar matarsa.

A can soron kuwa Hamma Sulaiman na fita Hamma Sageer yayi wuf ya matso jikin Hassana zai kamata yakai jikinsa ,tsananin ado da k’amshin da jikinta ke fitarwa yayi matuk’ar gigitashi ,da hanzari ta kauce tak’i bashi damar hakan ,yayi mugun marairaicewa yana matsowa a hankali zuwa jikinta ,muryarsa bata fita sosai yake magana “don Allah Sweety kibarni …kibarni yau na rungumeki a k’irjina ko zanji salama abisa zafin k’aunarki da nakeji ….

Girgiza masa kai tayi tana kallon idanuwansa da zallar soyayyarta tacikasu ,sai sauke numfashi da ajiyar zuciya yakeyi ,matsowa tayi dab da kunnensa ganin yadda yake lumshe idanuwa tayi magana tamkar me rad’a ” kwana d’aya tal ya rage nazama taka Hamma Sageer ,kar kayi gajen hak’uri kajira gobe ,ranar da idan ka rungumeni lada zaka samu ,amma yanzu da sauran lokaci banason kayi abinda zaka sab’awa Allah ……”tana gama magana tayi hanyar fita tana cewa “mu kad’ai ake jira tawo Hamma Sageer,
Jikinsa a salub’e ya biyota ya jera da ita, tuni Hamma Sulaiman yana tsaye yana jiransu ,nan da nan suka shige motar shima yashiga yaja suka tafi.

Suna isa wajen taro yadawo kansu, aka saki taken amare da angwaye ana watsa musu flowers cikin taku na burgewa suke takawa har zuwa mazauninsu ,
Sakeena kuwa ba k’aramin mamakin ganin mijinta tayi agun ba ,barin k’awayenta tayi tanufi mijinta taja hannunsa suka fita har wajen motarsa ,shidai biye yakeda ita har sukaje wajen tanata b’ata rai da mitar meyasa yazo ….!?mamaki ya kamashi ya dubeta yana cewa ” zuwan nawa ya zama laifi ne ….!?tana buntsuro baki tace “kallafa y’ammata da yawa agurin nibanason aita kallemin mijina…!

Dariya tabashi sosai ,yana kallonta hannunsa rik’e da nata yace ” haba Sakeenan Sulaiman me y’ammata zasuyi dani bayan duk kin tsofar dani ….”ta juya idanu ta tana karkad’awa tace “Kaifa nawane ni kad’ai Abban sadauki ,shiyasa banason kana Shiga taron mata ana kallemin kai ….inajin a zuciya ta duk mazan duniya babu Wanda ya kaika komai …” Murmushi ya kumayi yace “ki k’arawa malaminki kud’i sakeenan Sulaiman Dan kin gama mallakeni na rantse…..!

Wani irin murmushi tayi tana Mirza yatsunsa a hannunta tayi k’asa da murya tace” Abban sadauki ….”
D’aya hannunsa yasa yad’ago kanta yadubi idanunta ya sakarmata wani kyakkyawan murmushi me girgiza zuciyarta ,a hankali ya furta cewar “idanuwanki da muryarki da jikinki sun gayamin buk’atarki ,ko baki furta ba Sulaiman yagane Sakeenansa tana buk’atarsa ……to Sulaiman a shirye yake …Dan haka sakeenan Sulaiman tak’ara shiryawa itama yau tamkar amarya zata jita …..!

K’irjinsa kawai ta afka tana sunne kanta tana dariya ,duk duniya bataga me saurin gano abinda takeso ba irin Sulaiman d’inta,kuma da zaran yagano zaiyi iya k’ok’arinsa wajen biya mata buk’atarta koda shi bashida buk’atar hakan ,ta tabbatar mijinta babban adali ne meson yimata adalci a rayuwar aurensu.

Dinner tayi kyau anci an Sha anyi abubuwa da dama wad’anda suka k’ayatar ,misalin k’arfe Sha d’aya na dare aka tashi.


Ranar lahadi misalin k’arfe goma na Safiya aka d’aura Auren Sageer mustafa da Hassana Abubakar akan sadaki dubu hamsin lakadan ba ajalan ba ,haka nan aka d’aura auren Abdurrahman Aliyu da Hussaina Abubakar abisa sadaki dubu hamsin lakadan ba ajalan ba,d’aurin Auren da yasamu halartar manyan mutane daga garin Gombe da ma wajenta ,unguwar herwagana tamkar ta tsage saboda jama’ar da suke tuttud’owa ,haka nan cikin gidan matane dank’am kowa yaci kwalliya ana shan shagali,abinci kuwa gashinan burjik sai Wanda kakeso ,tunda akace an d’aura auren duk jikin amaren yake a sanyaye …saboda sun San a yau zasu rabu da iyayensu kowacce akaita gidan mijinta,hatta Babangida da Usman yau jikinsu a sanyaye yake matuk’a babu wannan wasan da suka saba ,sai Ya safwan nema da yaketa shige da ficen kai abinci waje yake tsokanar amaren ,Shiga d’ari fita d’ari ya kallesu yayi musu gwalo da fad’in “yau wasu yara zasu bar gidannan dolensu ” saida Adda Nabeela tace zataci mutuncinsa sannan ya sarara musu,ganin har Hussaina iya rigima tafara kuka.

Baba da su Hamma Sulaiman kuwa warkajaminsu suketayi na kulawa da bak’i sai kai kawo sukeyi ,farincikin Baba da Umma bazai misaltuba ganin sun aurar da yaransu guda biyu a wannan rana.

Har lokacin da angwaye suka shigo da tulin Abokansu Dan yin gaisuwa bayan gama d’aura aure,amaren na k’unshe a d’akinsu cikin k’awayensu ,Hamma Sageer sai wurwurga idanu yake yanason ganin amaryarsa amma bai ganta ba ,ji yake tamkar idanunsa zasu makance saboda rashin ganinta….yana kallo Abdurrahman yatashi yashige d’akinsu Hassanar amma shi yakasa saboda kunya ,har suka gama gaishe gaishen suka mik’e Dan tafiya baisa matarsa a idanunsa ba ,gashi wata shagwab’a yakeji ta musamman ,kukan farinciki yakeso yayi kuma bayaso yayishi agaban kowa sai sweetynsa ,

Suna fita soro yaga sadauki da Auwal D’an Adda Nabeela zasu shigo ,sunsha kwalliyarsu da shadda ta ankon d’aurin aure, jawo hannun sadauki yayi Yakama kunnensa ya rad’amasa cewar “kaje d’akin su Auntynku ka rad’amata tazo d’akin su safwan na soro inason ganinta” amsawa sadauki yayi yana murmushi sannan yaja hannun Auwal suka shige gidan.

Da sallamarsa ya kutsa d’akin ,can ya hango Hassanan a k’arshen d’akin tazuba tagumi idanunta jajir ,ga Hussaina sai gurshek’en kuka takeyi ga Ya Abdurrahman tsugune a gabanta yana aikin rarrashi da lallab’awa cikin sigar soyayya ,d’akin da akwai yawaitar mutane wad’anda suke tayiwa Hussaina dariyar kukan da takeyi,haka sadauki yaita tsallake mutane da nufin isa gun Hassana Dan Isar da sak’on da aka bashi,har saida Aunty sakeena tace” sadauki INA zakane kake tsallake mutane haka ?yana tafiyar yakecewa “momy an aiko ninefa ” bai tsayaba saida ya isa gaban Hassana sannan ya durk’usa dab da kunnenta ya rad’a mata sak’on,
Duk da fad’uwar da gabanta yakeyi hakan baisa tak’i zuwa kiran mijinta ba ,itama burinta taga Hamma Sageer tsaye agabanta a matsayin mijinta ba saurayinta ba ,da mayafinta akanta tamik’e taje tagayawa Aunty sakeena kiran da Hamma Sageer kemata,murmushi Aunty sakeenan tayi tace”maza kije kiran mijinki k’anwata”

Haka tadinga wuce mutane anata kiranta da “amarya kinsha k’anshi” ,itadai murmushi kawai takeyi har ta isa d’akinsu Ya safwan da ke soron gidan,
Gabanta na fad’uwa tad’aga labulen d’akin tashiga tareda kwarara sallama,babu kowa a d’akin sai Hamma Sageer da ke tsaye yajuya bayansa cikin shigar angwaye me k’ayatarwa,banda k’amshin turaren jikinsa babu abinda ke tashi a d’akin,a wani irin slow ya juyo jin sallamarta yana dubanta ,abubuwan da tagani a idanunsa yasa jikinta yafara mazari k’afafunta na rawa,saura kad’an tazube k’asa ya tawo da sassarfa yasa hannayensa masu tsananin taushi ya d’agota yana wani irin kallonta idanunsa cikeda hawayen k’auna ,da wata murya me sanyi yace “sweetyna yau kin zama matata,so nake na kwanta ajikinki nayi kukan farinciki ….Dan Allah sweety ki rungumeni a jikinki yau nazama jaririnki kinji …..” Jikinta na rawa ta runtse idanunta k’irjinta na bugawa ,tanaji Hamma Sageer yafara ware hannayenta yana shigewa jikinta a hankali ,Kansa yakife a k’irjinta yana shak’ar k’amshin jikinta yana ajiyar zuciya ,kafin wani irin kuka ya k’wace masa ,sosai ya fashe da kuka hawayensa na malala tsakiyar k’irjinta …..yasa hannayensa ya rungumeta k’ak’am yana sheshshek’an kuka da ambatar “sweetynahhhhhhh………!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button