HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL


    ***Zaman su a transcop Hilton hotel haka yacigaba da kasancewa babu wata shak'uwa tsakaninsu sosai ,sai dai Hamma Sageer yana k'ok'arin sauke nauyinta na ciyarwa da shayarwa da kulawa da ita,amma wata mu'amala da zata kusantasu da juna bata k'ara had'asu ba ,yawanci ma yana fallow ita tana bedroom ,ita d'inma tana yimasa biyayya da bin umarninsa ko yaushe ,ko batason cin abinci indai yace taci to zata ci ,haka nan tadena yawan kuka tunda ya nuna bayaso ,tanason tace yakirawo mata y'an gidansu a waya amma tana tsoro duk da tanada buk'atar hakan amma haka ta hak'ura .

Ranar da suka cika kwana uku da zuwa Abuja da sassafe taga yanata shiri alamar fita zaiyi ,tana zaune gefen gado tana ninke kayan da yacire yazo gabanta ya D’an duk’o zai d’auki wayarsa da take gefenta a ajiye ,cikin k’aramar murya yace “yaufa zamu bar gurinnan ki had’a mana kayanmu …” Kallonsa tayi ta d’anyi murmushi tace “daman nagaji da zaman gurinnan …ni dama gombe muka koma wallahi ….”ya D’an karkato Kansa shima ya tsura mata ido yace ” anan d’in ina cizonki ne hala ko … !?da sauri ta girgiza kai tace “ayya Hamma Sageer ba nufina kenan ba ” yad’an ciji lips d’insa ya k’ara matso da fuskarsa dab da tata yace “zan D’an fita yanzu zan dawo ,kar kisake nadawo natarar kinyi kuka , in bahakaba kin San sauran kema .

“Adawo lafiya ,Allah ya tsare ya kiyaye hanya “abinda tace kenan kanta a sunkuye ,bai San meyasa ba sai yaji dad’in addu’ar da tayi Masan a zuciyarsa ,a hankali ya amsa da ” Ameen “sannan yasa kai ya fice .

        Fitarsa babu dad'ewa ta kammala had'a musu komai ta gyara tsaf sannan tayi wanka ,batajin yunwa shiyasa ko kallon breakfast batayi ba ta shirya cikin wata bak'ar doguwar Riga me kyau da duwatsu da fulawoyi a jikinta batayi wata kwalliya ba illa turare da ta fesa ,ta yafa D'an kwalin kayan a kanta tanemi gefen gado ta zauna tana jiransa ,tun tana zaune har tafara hajiya da zaman ta zame ta kwanta rigingine tana lumshe idanu ,tuni bacci ya salallab'o ya saceta .



     Shikuwa Hamma Sageer yana fita harabar hotel d'in ya tarar da d'aya daga cikin ma'aikatan Mamma ya kawo masa mota ,bayan sun gaisa ya tashi key d'in motar me azabar kyawu ,sukayi sallama ya wuce shikuma Hamma Sageer yashiga motar yaja sai airport inda zai d'auko su Mamma wad'anda saura minti 15 su sauka a garin Abuja .



   Yana isa baijima ba jirginsu ya sauka ,yana nan tsaye mutane nata saukowa har ya hango Hamma Sulaiman ya fara dosowa ,Adda Nabeela na biye dashi ,sai Aunty Nafeesa ,sai kuma ta k'arshensu wato Mamma ,da hanzari ya tarbesu yafad'a k'irjin Hamma Sulaiman suka rungume juna ,wani farinciki yakeji na ganinsu ,Hamma Sulaiman yadinga Shafa bayansa yana k'ara rungumarsa da k'yar suka saki juna ,ya tsuguna har k'asa yana gaida Adda Nabeela ta amsa cikin tsananin fara'a da kulawa ,yana mik'ewa sai Nafeesa ta rungumeshi tana fad'in "k'anina " shima yad'an narke a jikinta yana fad'in "Aunty na ,na rantse nayi kewar Ku" sannan ya saketa ya juya wajen mahaifiyarsa da taketa kallonsa cikin so da kulawa kamar ta had'iyeshi ,fuskarsa da walwala ya ambaci "Mammana ....." Sai kuma ya k'arasa gabanta yana kwanciya kafad'arta idanunsa na cikowa da hawaye ,a hankali tad'agoshi tana murmushi ta kalleshi ,sai takai hannunta kan wuyansa ta tab'a k'ashin wuyan tana cewa "Sulaiman kudubamin yadda wannan angon ke rama ....yaseen angwaye k'iba sukeyi ba ramewa ba ,Allah dai yasa mu tarar da amaryar tayi k'iba ita...Dan idannaga rama a tare da ita to laifin kane"

Ya d’anyi murmushi a zuciyarsa yana fad’in “ai tafini ramewa ma ,wannan kukan da takeyi zai barta tayi k’ibane …. !?su kuwa Hamma Sulaiman dariya sukayi suna kallon Sageer .

Suna tafe a mota Sageer na tambayar lafiyar jama’ar gida ,Hamma Sulaiman yace ” kowa lafiya lau duk suna gaisheku ,kuma a hankali kowa zaizo ya ziyarceku “Ya lumshe idanu da fad’in ” Hamma Sulaiman ina Abdul d’ina yashiga ne .!?bana samunsa a waya ko nakira woshi …..”murmushi Hamma Sulaiman yayi yace “Abdurrahman yana lafiya lau ,kawai dai yanata shirye shiryen tafiya k’asar waje ne wai zaiyi wani course ,kuma ya sauya layin waya ne amma yacemin incemaka kana zuciyarsa ako yaushe kuma zakajishi da zarar komai ya daidaita agareshi “

Hamma Sageer ya runtse idanunsa zuciyarsa na ciwon rashin Abdul akusa dashi ,yasan tilas ce zatasa Abdurrahman Barin gida kodan yarage tunani ,zuciyarsa akwai mikin rabuwa da masoyiyarsa ,kamar yadda tasa zuciyar tafi ta Abdurrahman ciwo da Shiga k’uncin rashin masoyiya ,sweetynsa tabarshi bari na har abada ,hawaye ya ratso idanunsa amma yayi hanzarin mayar dasu.

Nan da nan suka isa hotel d’in inda zasu d’auki Hussaina su wuce gidan Mamma inda zasu zauna ,a fallow Hamma Sageer ya tsayar dasu yace duk suyi shiru yanason yayiwa Hussaina surprise ne ,yana shiga bedroom d’in ya tarar sai sharar barci takeyi a hankali ya matsa yana kallon fuskarta da tayi fayau tana walwali tamkar ta marigayiyar masoyiyarsa ,bai San lokacin da yakai hannu ya shafi fuskar ba ,sannan ya hura mata iskar bakinsa akan fuskarta ta ,a hankali tafara bud’e idanunta da suka d’anyi ja ta dubeshi tsigar jikinsa tad’an mik’e saboda saukar idanunta cikin nasa, da hanzari yad’ago kafad’unta yana mik’ar da ita tsaye tamkar zai had’e k’irjinsu guri guda ,fuskarsa kadaran kadahan yace “surprise” ta D’an juya idanunta da kad’a kai tace “Hamma Sageer for what…!?bai bata amsa ba illa D’an kwalinta da yacire akanta ,kyakkyawan gashinta da zubo kafad’unta yana k’yalli ,ya tattara gashin yayi baya dashi sannan yasa D’an kwalin ya d’aure mata idanunta ,yaje dai dai kunnenta yacemata ” zan baki mamaki ne ,idan mukaje zakiga abinda zan Nuna miki”yaja hannunta yanufi falon da ita ,itakam murmushine akan fuskarta dimple d’inta sai motsawa yakeyi.

Suna zuwa tsakiyar falon ya zagaya bayanta ya kwance d’ankwalin daga fuskarta ,a hankali yace “open your eyes ” tafara bud’e idanun a hankali suna rawa rawa ,ganinta yafara sauka akan Hamma Sulaiman da Adda Nabeela da ke tsaye suna doka murmushi .

Da sauri tak’ara ware idanunta sosai sai kuma tajuya da hanzari takife kanta a k’irjin Hamma Sageer jikinta narawa tana cusa kanta ak’irjinsa tana sauke numfashi ,cikin rawar baki tace”Wayyo Hamma Sageer idanuna gizo sukemin suna nunamin Hammana da Addana agabana….”hannu yasa yad’ago kanta a k’irjinsa ya tallafe fuskarta sannan yad’an d’aga mata girarsa idanunsa na narkewa acikin nata yace “ba gizo bane sune suka kawomana ziyara ” janyewa tayi daga jikinsa tatafi a hankali har zuwa gaban Hamma Sulaiman tasa hannunta tanad’an tab’a jikinsa alamun tabbatarwa ,ai tanajin da gaske cewar shid’inne agabanta batasan Sanda ta Daka wani uban tsalle ta afka k’irjinsa ta k’ank’ameshi ba ,shima da saurinsa ya tarbeta ya rungumeta ak’irjinsa a sanda yaji ta fashe da wani gigitaccen kika tana ambatar “wayyo Hamma Sulaiman d’inaaaaaaa????!

Comment
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page6⃣5⃣to6⃣6⃣

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W) YACE “IDAN KAGA BAWA NA SAB’O KUMA ALLAH YANA BASHI DUNIYA ,TO KASANI TALALA CE AKE MASA,SAI YA KARANTA FAD’IN ALLAH “LOKACIN DA SUKA BAR ABINDA AKE TUNATAR DASU DASHI ,SAI MUKA BUD’A MUSU K’OFOFIN KOMAI ,HAR SAIDA SUKAYI FARINCIKI DA ABINDA AKA BASU ,SAI MUKA KAMASU BA TARE DA SUN KINTSA BA

AIKI ME FALALA

LALLAI AN BIJIRO WA ANNABI (S A W) DA AL’UMMARSA ACIKIN BARCI ,SAI YAGA AL’UMMARSA ,ACIKINSU AKWAI DUBU SABA’IN WANDA ZASU SHIGA ALJANNA BA TARE DA HISABI BA,KUMA BATARE DA AZABA BA,WAD’ANNAN SUNE WAD’ANDA BASAYIN LALAS DA WUTA,KUMA BASA NEMAN MAGANI ,KUMA BASAYIN SHU’UMCI (CAMFI) A BISA ALLAH KAD’AI SUKE DOGARA

 ***Kawai sai Hamma Sulaiman ya zareta daga jikinsa yadireta kan kujeran falon ,sannan yayi hanyar fita yana cewa "Mamma ,Adda Nabeela kawai kuzo mu koma inda muka fito ,batayi farinciki da zuwan muba bakuga kuka ma take ba ....!?ya fad'a yana niyyar bud'e k'ofa yafita kamar gaske .



  Da hanzari Hussaina tamik'e har tana shirin fad'uwa k'asa saboda riganta da ta hard'eta ,taje ta rik'e rigan Hamma Sulaiman k'am sannan ta rungumeshi ta baya hawaye nafita a idonta amma haka ta daure takama dariyar k'arfin hali tana fad'in " na rantse inajin yau aduniya babu Wanda ya kaini murnar ganinku ,Hammana kukanma fa na murnar ganinku ne yaseen ...."ya juyo a hankali yana cireta a jikinsa sannan Yakama hannayenta ya rik'e yace "nito banasan ganin hawaye a fuskarki ,ko na farinciki ne banaso ,Dan haka ki gogesu " har zata kai hannu fuskarta Dan ta goge da sauri Hamma Sageer ya iso gabansu ya rik'e hannayen ta kansa a sunkuye yace "nine mai share mata hawayenta ai Hamma Sulaiman ,ko ka manta ne ....!?sannan yasa hannu ya goge mata fuskarta tsaf yanayi yanai mata wani shu'umin kallo tamkar irin yafara sonta d'innan .



      Dariya Hamma Sulaiman yayi yace " Sageer nagode da cika alk'awari da rik'on amana "sannan ya kalli Hussaina da ta lafe agefen jikinsa yace " dafatan kema kina rik'e amanar da nabaki kuma kina kulawa sosai da ita ...."tana wasa da mab'allin gaban rigar Hamma Sulaiman tace "eh Hammana ina rik'ewa sosai ,komai ni nake wa amanarka ,bana barinta tayi kuka ,bana barinta cikinta damuwa " Hamma Sageer wani kallon k'asan ido yake mata me kama da harara ,yayinda Hamma Sulaiman ya shafa kanta yace "good girl,toh jeki ki gaida su Mamma ,tun zuwanmu kin manta dasu a tsaye ko ...!?cikin kunya tasaki Hamma Sulaiman ta k'arasa gaban Mamma tazube tana kwasar gaisuwa ,d'agota tayi ta rungumeta sosai ajikinta tana amsawa cikin farinciki ,bayan Mamma ta saketa ta gaida Aunty Nafeesa ma ,itama kamar Mamma rungumeta tayi sosai cikin kulawa take shafa bayanta tana amsawa da tambayarta lafiyar ta ,ta amsa da komai lafiya lau .

Tana d’agowa ta kalli Adda Nabeela babbar Yaya magajiyar Umma kenan ,da sauri ta nufeta tafad’a jikinta tace” Addanmu maganin kukanmu …”Adda Nabeela tace “aini nayi fushi ,bayan kin manta damu a tsaye ta Sulaiman kawai kikeyi …” Ta k’ara k’ank’ameta tana k’aramar dariya tace “haba Addana waye zai manta da magajiyar ummansa a rayuwa ….!?murnan ganinkune duk yasa idanuna rufewa fa …Addana ina ummana ?ina Babana? Ina mummy ?ina Hamma Aminu?ina ya safwan ?ina Aunty Sakeena da Aunty Sadeeya ?ina Babangida da autan Umma ?…haka tadinga jero tambayoyi .

    Su dariya ma tabasu sai Adda Nabeela ce tana dariyar tace" ho ,Hussaina kenan !kowa yana lafiya ,kuma kowa yabada sak'on gaisuwa zuwa gareki, Babangida har fura da nono yasiyo yace nakawo miki ..."ta runtse idanu tana jin k'aunar ahalinta tace "Allah sarki Babangida D'an uwana ,wallahi ina kewarka sosai "

Kin tambayi kowa amma baki tambayi Abdurrahman ba …!?cewar Adda Nabeela tana kallon fuskarta ,Hussaina ta sunkuyarda kanta tanajin wani mik’i na taso mata tace “Addana ki k’yale ya Abdurrahman baruwana dashi domin kuwa yamin laifuka masu d’umbun yawa ….” Sai Adda Nabeela tad’ago fuskarta ganin har idanunta sun cicciko tace “kimasa afuwar duk wani laifi da yayi miki, kar abun yayi masa yawa kinji …..” Ta kwanta kafad’ar Adda Nabeela tana lumshe idanunta tace “Ya Abdurrahman yamin laifi mai d’umbun yawa ,amma kuma kowa yabonsa yakeyi akan abinda ya aikata ,hatta Hassanana da bata Raye ta yabeshi kuma tayimasa addu’a ,to nima ga addu’a ta nan zuwa gareka Ya Abdurrahman ,Allah yadubeka yayi maka abinda baka tab’a zato ba na alkairi ,Allah yabaka abinda kakeso duniya da lahira …..” Dukkansu da suke wajen saida suka amsa da Ameen ,yayinda tausayin Abdurrahman yacika zuciyar Hamma Sageer ba masaka tsinke.

Basu wani b’ata lokaci ba suka kwashi kayansu suka bar hotel d’in transcop Hilton suka nufi gidan Mamma da ke unguwar maitama ,unguwa mafi darajoji acikin birnin tarayya Abuja ,domin kuwa ta had’a manyan masu kud’i da k’usoshin gwamnati da manyan ma’aikata ,unguwa ce mai kyau da take d’auke da had’ad’d’un gidaje tamkar a k’asar waje, gidan Mamma bawani shahararren girmane da shi ba illah tsaruwa da kyawu ,part biyu ne had’ad’d’u Wanda ya had’a da na Mamma da na su Hamma Sageer, fad’ar yadda aka tsara gidan da abubuwa na more rayuwa b’ata bakine sai dai kawai ince muku komai yaji a wannan gida tamkar aljannar duniya .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button