HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sadiya ta d’anyi dariya tace “Hamma sulaiman wayar tasa tana hannuna ne ,nikuma tawa tana hannunsa ,musanye mukayi yau ” Hamma yayi kasak’e yace “musanye kuma …!?tace ” eh Hamma, akwai abinda zamu gwada juna dashi shiyasa mukayi musanyen waya yau …! Ya d’anyi tsaki yace “daga Aminun harke kun kasa girma ,sai girman jiki kawai da shirme ,yanzu haka za’ayi ta kiransa wayar Na hannunki ,gashi inason magana dashi da hanzari yanzu ” yana rufe baki ta amsa da cewar “ka kirashi da layina Hamma, zaka sameshi ,” yace “banida numbarki a wayana ,idan yadawo kungama shirmen kyace masa yakirani kawai ” da hanzari dan kar yakashe wayar tace “yanzu Hamma ina k’anwarka amma bakada numbata a wayarka ….!?shima ya maida mata da tambaya” angaya miki ina ajiye number mata a wayata ne ….!?yabata dariya ,shiyasa tana dariyar tace “amma ai akwai ta Aunty sakeena ko …!?yana shirin kashe wayar yace ” wannan ai sakeenan sulaiman ce “sannan ya kashe wayar yana duban Baba yana Shafa kai .

 Baba yace " ya akayi ne sulaiman ....!?baka sameshi bane ...!?Hamma sulaiman ya d'anyi murmushi takaici yana fad'awa Baba yadda sukayi da Sadiya ,shi kansa Baba saida yayi dariya da fad'in "wato Aminullah da Halimatu tamkar wasu yara suke har yanzu ,Allah ya kyauta "

Hamma sulaiman ya amsa da “Ameen dai Baba”.


Kwana biyu bayan wannan Malam Huzaifa yasan matsayinsa ,inda Hamma sulaiman da kansa yasameshi yayi masa bayani cikin nutsuwa da fahimta ,ya kuma bashi hak’uri sosai da sosai ,duk da maza nada dariya amma saida Huzaifa ya razana da jin maganar ,har kuka saida yayi agaban Hamma sulaiman na rasa Hassana da yayi ,haka Hamma sulaiman yaita rarrashinsa da bashi baki har ya hak’ura ya share hawayensa ,ya tabbatarwa da Hamma cewar ya hak’ura ,kuma yanaiwa Hassanar fatan alkairi .

Ko a Makaranta bai nunawa Hassana komai ba ,sai itace ma ta dingajin mugun tausayinsa ganin yadda ya rame tasan duk soyayyarta ce tajawo masa hakan ,kunyarsa sosai ta dingaji ganin yadda yadinga hidimar taimaka musu wajen musabak’ar da zasuyi ,Hussaina har kukan tausayin Malam Huzaifa tayi ,taitayiwa Hassana mita tana cewa ” banda abin soyayya ga inda tadace amma and’auketa ankaita inda bata daceba ,na rantse ko zan dafa alk’ur’ani kinfi dacewa da Huzaifa akan wancan mutumin …badan inason ya Abdurrahman ba da na wankewa Malam Huzaifa zuciya na karb’i tayinsa a madadinki”Hassana tayi murmushi yak’e tace “nima badan inason Hamma sageer ba da Malam Huzaifan shine farkon Wanda zan zab’a …toh sai dai soyayya da k’auna na Hamma sageer sun cika ruhina taf sisina “.

Sosai Malam Huzaifa yayi k’ok’arin ganin an gabatarda wannan musabak’a ,kuma su Hassana da Hussaina sune sukazo na d’aya ,wannan yak’arawa Hassana da Hussaina tausayinsa a zukatansu , Malam Huzaifa ya tayasu murna sosai ,kuma yaja Hassana gefe guda yace mata ” kisaki jikinki kidena jin kunyata ,ni musulmi ne na yadda da k’addara ,nasan kuma ba k’iyayya ce tasa kika zab’i wancan a kaina ba ,sai dan k’ila shine Wanda Allah ya zab’amiki a matsayin miji, duk yadda kika kai da sonsa da k’aunarsa idan Allah yayi shid’in mijinki ne to zaki aureshi ,haka kuma duk yadda kika kai da sonsa da k’aunarsa idan Allah yayi ba mijinki bane bazaki aureshi ba ,amma inayi miki fatan alkairi da addu’ar Allah yasa ki auri Wanda kikeso kodan farincikin zuciyarki .

Hassana ta share hawayen fuskarta ta d’ago ta kalli Malam Huzaifa tace”Dan Allah kayi hak’uri Malam “ya katseta yana murmushi yace” kidena bani hak’uri bakiyi min komai ba ,naso samunki na aureki saboda ina sonki ,kuma inason HAD’A zuri’a da gidanku saboda karamcinku ,dole za’a tausayawa Wanda yarasa mace irinki Hassana ,da nine nayi nasarar samunki shima wancan haka za’ayi tajin tausayinsa ,don haka ki kwantar da hankalinki ban rik’eki a zuciya ta ba ,inai miki fatan alkairi a rayuwarki “

Maganganun sa suka kuma karya mata zuciyarta ,sai dai soyayyar sageer tayi nisa acikin zuciyarta ,haka suka dawo gida daga gun musabak’a jikinta a sanyaye , kowa a gidan ya tayasu murnar samun nasarar su ,haka Hamma Aminu yace zai cika musu alk’awarinsu na kyautar da yayi niyyar yimusu idan har sunci musabak’ar ,Adda Nabeela ma tayi murna kuma tasiya musu abubuwa iri iri na taya murna.

  Soyayya sosai ake gudanarwa tsakanin Hassana da Hamma sageer kamar acinye juna ,sun aminta da juna sun mallakawa zuciyoyinsu da ruhinsu k'aunar junansu ,Hamma sageer ya zauce ya susuce da soyayya ,baya gajiya da ganin sweetynsa da tura mata text iri iri na soyayya ,yana yawan cemata .

you are the happiness of my life,I love you so much my sweety

Ko yace “

my happiness is to see you happy
my sadness is to see you sad

Wataran idan shauk’i ya d’ebeshi a gabanta yake tsayawa yana kallonta kamar ya had’iyeta yace”

you are my wife insha Allah ,mother of my children

Kalaman Hamma sageer na tsuma zuciyar Hassana ,wataran har kukan k’auna takeyi ,idan Hussaina taga tana kuka ta tambayeta menene sai tace “k’aunar Hamma sageer ke damun zuciya ta da gangar jikina sisina” sai hawaye yacika idanun Hussaina tace”shiyasa nake kishin mutumin nan wallahi ,gabad’aya kin wawushe soyayya ta kin bashi “Hassana ta rungume Hussaina tace ” kidena kishi da Hamma sageer sisina ,son da nake masa ya bambanta da irin Wanda nake miki, na rantse da za’a tsaga zuciyar Hassana k’ila sonki za’a fara tararwa,na tsaya ina fad’ar irin son da nakemiki k’auyanci ne a gurina ,ked’in kece komai nawa ,kece zuciya ta ,kece gangar jikina ,kece jinin da ke yawo a jikina sisina .

Da k’auna ta d’ebi Hussaina saita rungume Hassana itama tana hawayen murna da k’aunar Y’ar uwarta ,k’am suka rungume junansu tamkar su dawwama a haka.


B’angaren mamma da tasamu labarin abinda ke tsakanin sageer da Hassana har sadaka tayi ,tana murna taceda Aunty Nafeesa “kullum addu’a ta Allah yasaka soyayya a tsakanin yaran nan ,Ashe Allah ya amsa ,nagodewa Allah ,kuma nagodewa Hassana da tazama tsani wajen dawo da Muhammad d’ina hankalinsa ,Nafeesa sageer da kansa yazo yanemi afuwata akan abinda yafaru a baya ,nice me laifin amma haka ya durk’usa agabana yana kukan Neman tafiya ta ,nikuwa mezanwa Allah banda godiya da k’ara neman afuwarsa da istigfari akan laifukana “

A wannan lokacin kowa ya sanda maganar Hassana da sageer a danginsu da gidansu ,manya sun Shiga zancen angama maganar aure,da zarar sun kammala Makaranta za'ayi bikinsu ,soyayya ake bugawa babu kama hannun yaro .

Agefe guda kuma Hussaina da NATA masoyin ya Abdurrahman na zabga tasu soyayyar suma.

  Abu d'aya ke tayarwa da Hassana hankali da sata kuka a kullum ,idan ta tuna masoyan ta guda biyu Na gaba da junansu ,yadda Hussainan ta ta tsani sageer ....haka sageer yake nuna halin ko inkula da Hussaina ,ko zancen Hussaina bayaso Hassana tayimasa idan suna tare......."

k’ak’a k’ara k’ak’a,wace irin k’iyayyace tsakanin sageer da Hussaina haka…!?shin sunyiwa Hassana adalci kuwa idan sauka cigaba da nunawa juna k’iyayya…!?

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

      *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page3⃣5⃣to3⃣6⃣

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W)YACE “BAYA HALATTA GA MUSULMI MAI IMANI YA K’AURACEWA D’AN UWANSA MUSULMI SAMA DA KWANA UKU ,(MA’ANA YAYI GABA DASHI)DUK WANDA YA AIKATA HAKA,ZAI SHIGA WUTA KO YA MUTU

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W )YACE ” BABU WATA RANA DA BAYI SUKE WAYAR GARI FACE MALA’IKU GUDA BIYU SUN SAKKO ,D’AYANSU YACE “YA ALLAH KABAIWA MAI CIYARWA MAYEWA ” D’AYANSU KUMA YANA CEWA “YA ALLAH KABAIWA MAI RIK’EWA MAMMAK’O (ASARA)

****Hassana da Hussaina zaune cikin d’akinsu tare da Zahra takawo musu ziyara ,hirar su sukeyi da yadda za’a tsara biki a k’awatashi sosai ,Zahra tana ta ambato abubuwan da za’a gabatar a bikin, su dai dariya kawai sukeyi suna jinta.

  Hussaina ce tace" Zahra duk abubuwan da kike zayyanowa ba masu yiwuwa bane ,dan ko Baba ya yarda nasan Hamma sulaiman ba zai amince ba ...haka zaice albarkar auren ake nema ba yawan shirme ba "Hassana tace " abinda nakeson fad'a kenan sisina kika rigani ,koni ina bayan Hamma sulaiman ...bancika son yawan party a biki ba ,saboda wallahi duk anan ake zubarda albarkar auren, kiga aure da anyi anfara samun matsala, saboda mun bar fad'ar ma'aiki muna aikata son ranmu ",Hussaina ta gyara zamanta tana kallon Hassana tace " kin san kuwa yadda ya Abdurrahman yaci buri akan bikin nan ...!?ai wallahi yace dole ayi party a bikin mu ,yacemin fa abokansu dake k'asar waje ma zasuzo bikin ..."Zahra tayi shewa tace "wallahi inayin ya Abdurrahman ko garin ba kowa ...!ai ni ina bala'in son harkar rak'ashewa ...yama za'ayi ace za'ayi bikinku lami ...!?zan samu Aunty sakeena ta lallab'a mana Hamma sulaiman ya amince mu gwangwaje a bikin nan " Hassana ta tuntsire da dariya tace "kijawo mata matsala dai ...!na rantse akan hakan Hamma zai iya yimata yajin magana na sati guda..." Zahra tace "yaseen sai dai in bata lafe abinta a bed ba ...sanda zai amince bazaiyi shawara da kowa ba " Hussaina ta d'alawa Zahra duka a cinya tana dariya tace "bakida mutunci Zahra ,mu Hamman mu baya lafewa a bed " Zahra ta Sosa cinyarta ta kanne ido d'aya ta d'aga girarta tace "Allah ko. ..!?Ashe baya lafewa a bed ...!?inajin Aunty sakeena a ruwa tasamo sadauki da k'annensa ko ...!?sai Hussaina ta d'ora hannu aka tace " Zahra kinfi k'arfina ....na rantse Aure zamuyi miki kema ...tunda kin tafasa kafin ki k'one "Zahra ta juya idanu tace " aini aure ba yanzu ba sai nazama professor tukun ".
   A dai dai wannan lokacin wayar Hassana tayi k'ara alamar shigowar sak'o ,tana dariyar maganar su Zahra ta d'auki wayar tana dubawa sai taga Hamma sageer ne ya turo sak'on .

Nakasa komai sweety ,ganinki kawai nake son yi wallahi ,ina waje kifito

Fuskarta ta k’ara washewa da fara’a tanajin son Hamma sageer nakuma mamaye ruhinta ,kawai sai ta mik’e daman ashirye take tsaf da ita, illah turare da ta d’auka takuma fesawa ,sannan tazaro hijab d’inta wankakke gogagge tasa a jikinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button