HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Wani irin kallo naga tana yimin kamar ta kifamin mari ,sannan tasa hannunta ta girgiza kafad’ata tana fad’in “me kikace …..!?me nake shirinji …….!?me hakan ke nufi …….!?

Comments
Share
Vote

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

Masu son shiga group d’ina suyimin magana da wannan number

08080049548

TYPING????

???????? HASSANA ????????

              *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

WATTPAD:hassana3329

page 7⃣to 8⃣

SADAUKARWA

GAREKU KANO STATE WRITER’S ,ALLAH YA K’ARA HAD’A KANMU ,YA K’ARO BASEERA DA ZAK’IN HANNU????????????

1 .Hauwa(real smasher)
2 . Maryam (Manab )
3 .Rabi’at SBS big gal

  1. Surayya
    5.Fauziyya me agogo
    6.feedyn bash
    7.Binta Umar Abbale
    8.Jannat (real takowa)
    9.Laurat
    10.Aunty hubby

Aci gaba da gashi suya sai ran sallah????????????

***Bansani ba shiyasa nake tambayarki ko ke kin Sani ………?in kin sani ki fad’amin pls ….???? cewar HASSANA tana kallon sisinta da langab’ar da kai .

    Jawo hannunta HUSSAINA tayi suka zauna a gefen katifar ,tana rik'e da hannun Hassanar GAM ta k'uramata ido cikin sanyin jiki tafara magana "Rabin raina wannan alamomin da kika zayyana min fa nuni suke da alamun so .......in banyi kuskuren hasashe ba k'ila son wannan D'AN DABAN kika fara ,Wanda kuma shine Abu mafi muni da zaki aikata wallahi ........

Gaban Hassana ya yanke ya fad’i jin kalamin sisinta …..wane irin so kuma ….?kawai batasan mutum ba tafara sonsa…….? Ita dai tasan ba so bane kawai dai tana jin tausayin sa ne ,kuma tana jin sa a ranta tamkar jininta ,shiyasa ta bud’e baki da k’yar tana duban fuskar HUSSAINA da dimple d’inta ke motsawa saboda yamutsa fuskar da takeyi tace” ba so bane sisina, akanme zan soshi …,?kar ki manta ban sanshi bafa ……kawai dai ina tausayinsa ne ,San……..

“A kanme zaki tausaya masa ……?ta katseta ,sannan taci gaba “shima baiji tausayin kansa ba, cutar da kansa yakeyi balle a tausaya masa ,Rabin raina idan ma sonsa kika fara kiyi k’ok’arin cireshi a ranki ,Dan banga ta inda alak’arki dashi ta dace ba ,ke salihar baiwar Allah ce me hankali da sanin ya kamata da bin dokokin Allah ,shikuwa almubazzari ne ,Mara kunya ne ,sannan ba mutumin arzik’i bane ……..wallahi tun randa nafara ganinsa naji na tsaneshi ,bana fatan wata alak’a tashiga tsakaninki da wannan D’AN DABAN …..Dan haka be care full Rabin raina …….

Runtse idanu Hassana tayi saboda azahirin gaskiya taji zafin kiran sageer D’AN DABA da sisinta tayi ,bud’e idanu tayi tana duban sisinta ,sai kuma tazame ta kwanta kan cinyarta a hankali tace ” pls kidena kiransa da D’AN DABA ,ki kirashi da sageer ko Muhammad “

Ture kanta HUSSAINA tayi tana fad’in “d’agamin cinyata ni ,kuma da D’AN DABA zan dinga kiransa har ABADA ,sunan da yadace dashi kenan ,domin kallon farko da nayiwa idanunsa nagansu a shanye na tabbatar shaye shaye yafara juyar masa da k’wak’walwa ,Dan haka sunansa D’AN DABA A GURINA ……

Bata kuma magana ba ta mik’e ta jawo abincinsu tana fad’in ” tashi muci abinci ,ko kuma naje nafad’awa Umma kin fara soyayya da D’AN DABA”

Sosai Hassana ta kwashe da dariya jin abinda sisinta ta fad’a ,wai tafara soyayya da D’AN DABA ……Ganin tana dariya sai Hussaina ta rage idanunta tanai mata kallon uku saura kwata tace “Au dariya ma kike…..? Toh nafasa fad’awa Umman ma Hamma sulaiman zan fad’awa ,kin San dai duk yadda yake kaffa kaffa dake ,da nuna ked’in ta gaban goshinsace yanajin wannan maganar casamin ke zaiyi ……!?

A casani saikace wata masara …..inji Hassana kenan tana murmushi ,sannan takuma d’age gira tace ” bazaki bari a casani ba ai nasani ,sai dai a casamu tare ……

Hussaina takama hab’arta tana cewa”

Saboda kinsan haka shiyasa kike son kawomin rainin hammata …….!?nagaji da wannan maganar sakko muci abinci ,Allah sosai kika bani mamaki Rabin raina ,kuma idan Yaya Abdurrahman d’ina yazo saina gaya masa ,kodan yatayani jimami kuma ya hukuntamin ke ……in kikayi wasa kuma mukaje islamiyya nahad’aki da Malam huzaifan ki ……ince yana zaune za’a shashi basilla …….

Da dai Hassana taga mitar tak’i k’arewa tilas ta sakko tasaka cokali a abincin ta d’ebo ta nufi bakin Hussaina dashi ,da murmushi a fuskarta take fad’in ” Ha …..bud’e bakin in baki sisina ….da alamu yunwa kikeji shiyasa kike ta masifa ko ….?

Saida Hussaina ta shammaci Hassana sannan ta d’aka mata duka a cinya kuma ta karb’e abincin hannun Hassanar ta cinye tana dariya tace “nima na rama “tabar Hassana da susar cinya ,haka sukaci abincinsu cikin nishad’i da walwala ,kan ajima Hussaina ta mance da zancen wani sageer ,daman kuma ita mutum ce Mara rik’o ,lokacin da akayi Abu alokacin zatayi magana a kansa shikenan anwuce gurin…….bata kuma maganar sageer ba illah hirar masoyinta Abdurrahman da tacika Hassana dashi .


A Daren bayan sallar isha Hamma sulaiman ne tare da Hamma Aminu a gaban Baba, bayan sunci tuwon Umma ,sosai Baba ke tambayar su yanayin harkokinsu suna bashi amsa daidai gwargwado ,duk da Hamma Aminu ne me magana sosai ,shikuwa Hamma sulaiman a tak’aice yake maganarsa .

Baba ne yace ” Sulaiman kace zamuyi magana ko ……?amma saboda miskilanci kak’i magana …..to ni tunda kak’iyi gashi ni nayi ….me kakeson cewa …..?

Duk’ar da kansa yayi yana murmushi ,sai Hamma Aminu ne yayi dariya yace “Baba ai kasan halin mutumin naka magana tsada take masa ,ni narasa yadda sakeena takeyi dashi ,ita kuma gata da fara’a da yawan magana .

“Baba yayi k’aramar dariya yace ” ya kuwa zatayi dashi ….?haka take hak’urin zama da abunta …..Rannan fa Babangida ke ban labari wai yaje gidan suna hira da sakeenan shi sulaiman na zaune baisa baki ba ,da ya tashi yin magana bud’ar bakinsa sai cewa yayi “duk duniya banga mai yawan karad’inki ba sakeena bakinki baya gajiya ne …..?kai ni kun dameni bari in bar muku gun ……ya tashi yayi shigewar sa d’aki “

Hamma Aminu yayi dariya yana kallon sulaiman da kansa ke sunkuye ana bada labarinsa ,yace “Hamman mu kai Baba ke jira……ya kamata ka sauk’ak’a mana zaman nan ….danni wallahi Amsad tace yau nakoma da wuri akwai surprise da zata bani “

Hamma sulaiman ya d’an hararae shi,sannan ya matso sosai kusa da Baba ya kama hannun Baban ya rik’e yace “Baba don Allah kayimin alk’awarin zaka amince da abinda zan fad’a maka ….. Kaji Babana “

” Baba ya k’urawa d’an nasa idanu cikin k’aunarsa da jin sa aransa ,ko acikin yaransa ba k’aramin so yakewa sulaiman ba ,ya kalli Hamma Aminu suka had’a idanu ,shima Aminu kasak’e yayi yana mamakin Hamma sulaiman ,shikuwa wace magana ce da yake rok’on Baba ya amince tun kan ya fad’eta …….!?

Dariya Baba yayi yace “nak’i wayon sulaiman ,bazanyi alk’awari ba ban San me zaka fad’aba ,alk’awarin da zan maka d’aya ne matuk’ar abinda zaka fad’a naji ya kwantamin to zan maka adalci na yarda da shi ….karkaji komai bud’e bakinka kayi magana ,a gaban Babanka me k’aunarka kake”

Hamma sulaiman ya d’ago kyawawan idanunsa masu kama da madara ya kalli Baba ,sannan yakuma sunkuyar da kansa cikin sanyin murya da ladabi ,a hankali yace “Baba “….. ” Babana daman inason………..

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

TYPING????

???????? HASSANA ????????

             *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page 9⃣to ????

WATTPAD :hassana3329

SADAUKARWA

GAREKU GROUP D’IN HASSANA DA HUSSAINA FAN’S INAJIN DAD’IN SHARHINKU AKAN WANNAN BOOK TUN KAFIN INYI NISA ,KU D’IN NA DABAN NE ACIKIN ZUCIYA TA INA YINKU KAMAR YADDA KUKE YINA ,MASU YIMIN FATAN ALKAIRI DUK INA GODIYA ,KUCIGABA DA BINA LABARI YANZU AKA FARA????????????

MASU TAMBAYAR SHIN NID’IN LITATTAFAI NAWA NA RUBUTA …..?

TOH GA AMSARKU ????

HASSANA D’AN LARABAWA LITTAFINTA NA FARKO SHINE SANADIN HOTO ,LITTAFI ME CIKE DA TSANTSAR FAD’AKARWA ,ILIMANTARWA DA NISHAD’ANTARWA ,GAMI DA TAUSAYI ME RATSA ZUCIYA ,GA WANDA BAI KARANTA BA YA NEMA YA KARANTA DAN YA K’ARU DASHI ,YANZU KUMA INA KAN RUBUTA ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button