HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

      Umma tad'agota daga kafad'arta ta kalleta tace "me kika yiwa Sageer d'in da har kike nemansa kinemi yafiyarsa ...!?ta D'an runtse idanu hawayen yakuma zubowa cikin muryar kuka tace " naci mutuncin Hamma Sageer ,na muzantashi a gaban idonsa da bayan idonsa ,na kirashi da D'an iska Mara biyayyar iyaye ,na kirashi da D'an daba D'an shaye shaye agaban Hassanata ,amma Umma Hassanata bata tab'a fushi dani ba duk da son da takewa Hamma Sageer d'in ,ko zuciyarta tayi ciwo sai dai tayi kuka amma bazataji haushina ba saboda son da takemin, tana yawan yimin nasiha akan hakan amma nakasa ganewa ,duk da halayyarsa da ya sauya besa nayi masa uzuri na dena kallonsa da abun ba ,kullum Hassana ta tana gayamin k'addarace tasaka Hamma Sageer a wannan halin amma nakasa ganewa ,Hassanata ta rufamin asiri bata tab'a bayyana muku abinda nakewa mijin da zata aura ba ......"ta d'anyi shiru tanata shesshek'ar kuka sukuwa kallonta kawai sukeyi musamman Umma da mamakin maganar Hussainar yasata sakin baki tana kallonta ,Hussaina taci gaba da cewa "Ummana yau nayi mafarkin da yak'id'imani ya dagula lissafina ,mafarkin da ya kasance ya ruguzamin komai na tsarin rayuwata ,mafarkin da ya kasance silar rabuwa ta da Hassana ta rabuwa ta har abada ,mafarkin da ya kasance rabuwa da masoyina Ya Abdurrahman saboda sadaukarwar sa ,mafarkin da yakasance rabuwa da dangina da ahalina zuwa wata rayuwa ta daban ,Ummana Allah yana sona da rahamarsa da har ya kasance duk abubuwan da Nagani acikin mafarki ne ba gaske ba ,shed'an ne yadinga zugani a lokacin da nakewa Hamma Sageer rashin kunya da tozarci Wanda ba halayyata bane ,ba kuma tarbiyyata bane ,a yau nayi nadamar abinda na aikata ,kuma zanbawa Hamma Sageer hak'uri domin Neman yafiyarsa da afuwarsa ....."



       Kan Hassana a sunkuye tana taya sisinta zubda hawaye ,yayinda Ya Abdurrahman ya k'ura mata idanu yanajin kamar ya jawota jikinsa ya rarrasheta saboda yagaji da ganin hawayenta ,haka nan zubarsu tanasawa yaji duniya tayi masa zafi ,Umma kuwa b'acin rai tasamu kanta ciki na irin wulak'ancin da Hussaina take zayyanawa Wanda tayiwa Sageer ,Ashe haka ta zubar musu da mutunci agurin surukinsu ...!?zai dinga ganin kamar basu bata tarbiyya tagari ba ...duk da dai ka haifi mutum ne ba ka haifi halinshi ba ,to meyasa Hassana ta b'oye musu hakan !?da ta sanardasu Aida tuni sunyiwa tufkar hanci,sosai Umma fuskarta ta nuna fushi  amma ta taushi zuciyarta ganin ita kanta Hussainar cikin tsananin nadama take .......

Sunso ta bayyana musu menene ya faru a mafarkin da tayi ,amma kiran sallar magariba ya katsesu ,Umma tace abari bayan sallar isha’i su Baba da Hamma Sulaiman sun dawo da sauran jama’ar gidan ,sai abajeta a fai fai Hussaina tabada labarin komai da abinda ya razanata har tafara nadamar abinda ta aikata ,kuma Umma ta umarci Ya Abdurrahman da ya kirawo Sageer a waya yace yazo shima bayan sallar isha’i ,Abdurrahman yana gogewa Hussaina hawayen ta da handkerchief d’in hannunsa yake furta “indai wannan D’an halak d’inne zaki Ganshi ko ba’a kirawoshi ba Umma …..baya iya d’aukar lokaci baiga rabin ranmu ba fa …….


K’arar ringin d’in wayar tane ya sata hanzarin katse maganar da takewa Usman ,a hankali tamik’a hannu ta d’auki wayar ta mik’e tafito daga falon Baba inda dukansu ahalin gidan ke zaune suna jiran isowar Sageer ,shi Hamma Sulaiman ma wani takaici ne Yakama shi a sanda yaji wai tarasun da akayi Hussaina ce tayi mafarki kuma zata bada labarin mafarkin ,banda Umma ce tace ya tsaya da tuni yayi warewarsa gida wallahi ,su kuwa dukansu zaune suke suna tab’a hira banda Hussaina da tazuba tagumi tayi gum da bakinta ,Babangida nema me cemata ” sis gaskiya duk da banji labarin mafarkin nan ba nasan ya dakeki sosai ,kinga yadda kika firgice kina zare ido kamar b’era a bakin mage ….”girgiza kai kawai tayi tagoge hawayenta tace “barni Babangida ,wallahi naga rayuwa …” Sosai Ya safwan da Ya Abdurrahman suka kwashe da dariyar maganarta ,wai taga rayuwa ,
Hassana kam kunyar su Baba ce ta Janata d’aga wayar Hamma Sageer ,har said a tafito daga falon sannan tad’aga da sallamarta ,ta zarce da cewa “Hamma Sageer d’ina ….” Daga can ya lumshe idanunsa sassanyar muryarta na ratsa ilahirin jikinsa yace “sweety naaaaa,na k’araso fa ina k’ofar gida ” itama tad’an lumshe idanu ilahirin jikinta na mutuwa tsabar shauk’in masoyinta ,cikin murya me dad’i tace “Hamma Sageer gidanku nefa ….kawai kashigo meye na tsayawa a waje….” Cikin murmushi mekama da dariya yace”kin min izni …”kamar tana gabansa ta jijjiga kai da fad’in “nayi maka izni Hamma Sageer ,
” Da sharad’i “abinda ya ambata kenan ,ta karya wuya tana k’ara k’ank’ame wayar tace” bazan tsallake sharad’inka ba ,ni me cika sharad’inka ce aduk sanda ka ambatamin “

  Ya runtse idanunsa yana sakin ajiyar zuciya yace "babu abinda idanuna keson gani irin kyakkyawar fuskarki sweety ,so nakeyi ina shigowa nafara cin karo dake kiyimin murmushinki me narkar da zuciya ta ...." Da azama tace "wannan kad'ai kake buk'ata ....!?shigo kawai kasamu abinda kakeso dani zaka fara tozali ...."



 A hankali yafara takowa zuwa soron gidan har cikin tsakargidan da hasken wutar NEPA ya haskake shi ,tana tsaye tana kallon shigowarsa zuciyarta na bugun soyayya ,manyan kaya ne ajikinsa na wani brown d'in yadi d'inkin boda ,sai hula zanna bukar da ta dace da kwalliyarsa ,tunda k'afafunsa suka tako tsakargidan k'amshin turarensa ya game ko'ina ,ita dai kullum Hamma Sageer kyau yake k'arawa a idanunta ,musamman da ya kasance D'an gayu me tsananin tsafta.

Cak! Ya tsaya yana k’are mata kallo yana wani marairaice idanu ,yadda kallonsa yake Shiga jikinta shine yasata saurin sunkuyar da kai tana murmushi ,doguwar Riga CE a jikinta tayi rolling da veil d’in ,saita hard’e hannunta a k’irjinta kanta a sunkuye ,da wata irin murya ya ambaci “sweety na ….” Tad’ago kanta tana kallonsa tana murmushi ,sai ya bud’e hannayensa alamar tazo ya rungumeta ,har da cewa “zo sweety ,don Allah zo kiji ….!?wani irin zaro idanu tayi tana d’aga masa hannu da girgiza kai tana jujjuya idanunta da yi masa alamar babu kyau fa ,shima girgiza kan yakeyi yana karya wuya alamar ta temaka masa yana tayi mata alamar tazo gareshi ,wani irin sak’o suke aikawa da junansu ta hanyar idanunsu da hannayensu da sarrafa jikinsu ba tare da magana ba ,dariyar da sukaji itace tadawo dasu hayyacinsu ,da Sauri Hassana ta kalli inda taji dariyar sai taga Ashe Usman ne yake k’yalk’yala musu dariya yana tsaye a k’ofar falon Baba yad’aga labule yana kallonsu ………

*comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page7⃣5⃣to7⃣6⃣

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W ) YACE “YARDAR ALLAH TANA TARE DA YARDAR IYAYE ,DUK WANDA YAKE SON A FAD’AD’A MASA ARZIK’INSA ,KUMA AYI MASA JINKIRI CIKIN GURABUNSA(WATO A RIK’A TUNA WA DA SHI HAR BAYANSA )TO SAI YA SADAR DA ZUMUNCIN SA

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W ) YACE ” KUNYA BATA KAWO KOMAI SAI ALKAIRI ,KUMA YACE “KUNYA TANA DAGA CIKIN IMANI ,KUMA YACE ” ABUBUWA GUDA HUD’U SUNA DAGA CIKIN HANYOYIN ANNABAWA ,(SUNNONI)SUNE KAMAR HAKA:

1, KUNYA
2, SANYA TURARE
3, YIN ASUWAKI
4, DA KUMA YIN AURE.

SADAUKARWA GA

KANO WRITERS FANS ,INAJIN DAD’IN ADDU’ARKU GARENI DA KUMA JIN DAD’IN YADDA LITTAFINNAN YASHIGA RANKU KULLUM KUKE NEMANSA ,WANNAN SHAFIN NAKUNE KUYI YADDA KUKESO DASHI ,ANA KYAWUN TARE SISTER’S????????????????????????????

BARKANMU DA JUMA’A SISTERS ,ALLAH YABAMU ALBARKACIN WANNAN RANAR ,GA GORON JUMA’A NAN NABAKU ASHA KARATU LAFIYA????????????????

***Girgiza kansa yayi yana sunkuyar da kan k’asa ,a hankali ya furta “babu komai mammana …..”

Kusa dashi ta samu ta zauna tana rik’o hannunsa da tsananta kallonsa ganin yadda duk yayi wani iri ,cikin murmushi tace “Akwai wani Abu Muhammad ,duk wata mahaifiya tana gane yanayin da d’anta yake ciki na dad’in rai ko akasin haka ,menene yake faruwa ……!?

       Yaso ya b'oye mata saboda baima San ta inda zai fara gayamata maganarba ,sai dai nacin da ta nuna akan tanason ji yabashi k'warin gwiwar fara magana ,kansa na k'asa ya ambaci sunanta " mammah...."

“Na’am Muhammad Sageer ….” Ta amsa tana duban kyakkyawar fuskar d’anta mafi soyuwa a zuciyarta ,
“Wani alk’awari na d’aukarwa k’anwar sweety Wanda bazan iya cika mata shiba, harshena ne yayi azarb’ab’in furtawa ban Ankara ba mamma …..”

Har lokacin fuskarta cikin walwala take ,ta shafa kansa tace “babu kyau karya alk’awari Muhammad ,indai kanada yadda zakayi ya kamata kacika mata alk’awarinta …domin rashin cika alk’awari yana daga alamomin munafuki da aka zayyana …”

Yayi shiru k’irjinsa na bugawa yana Dana sanin furta alk’awarin ,har saida mamma tace “meyasa kayi shiru …!?kayi magana kaji Muhammad ,
D’agowa yayi ya kalleta ya girgiza kansa sannan yace ” banida ikon cika wannan alk’awarin ne ,domin idan zan cikashi zan sab’awa wadda banida kamarta duk duniya …!?idonta na cikin nasa tace “wacece wannan ….!?tana direwa ya amsa cikin karsashi ” mahaifiyata …..”wani irin lumshe idanu mamma tayi saboda jin dad’i tana k’ara k’ank’ame hannun sageer d’in a hannunta tace “me yakawo mahaifiyarka acikin alk’awarinka ….!?

         Ya kuma yin k'asa da kansa yana Jan numfashi yace " nayiwa mahaifiyata alk'awarin binta Abuja nida matata idan an d'aura mana aure, yayinda nayiwa k'anwar matata alk'awarin zama anan ba tare da tafiya Abuja ba saboda buk'atar ranta da son in kyautata mata ,Ashe ban saniba nayi kuskure Mammana ,buk'atar mahaifiyata itace gaba da komai ,Dan haka dole na zab'i alk'awari d'aya na cika na kuma yi watsi da d'aya alk'awarin duk da nasan akwai laifi a kaina "ya d'ago yana kallonta yayinda itama d'in fuskarsa take kallo cikin wani yanayi ,ya cigaba da cewa " ni Muhammad Sageer nazab'i alk'awarin mahaifiyata a matsayin Wanda zan cika ......"

Ta jima tana kallon fuskarsa sannan ta kawar da kai fuskarta da murmushi tafara magana “Tun ranar da na ambata maka cewar ina son kubini Abuja bayan biki na tabbatar da cewar zuciyarka batason hakan ,amma saboda biyayyarka ka hak’ura da son zuciyarka Dan kabi ra’ayina ,Muhammad ka cinye jarrabawata ,domin daman na gwadaka ne domin naga har yanzu inada sauran k’ima da girma a idanunka ko sun gama zubewa gabad’aya ,to a yanzu nagane kuma na fuskanci lallai har yanzu zuciyarka ni take ambata a matsayin mahaifiya kuma zaka cigaba da fifita buk’atata akan takowa ,Dan haka ba maganar tafiya Abuja yanzu …zamu cigaba da zama a mahaifarmu …Abuja sai dai muje Dan yawo ko wani Aiki …..”

    Yana saurarenta zuciyarsa na begen Sweetynsa wajen dagewarta akan yiwa mahaifiyarsa biyayya ,yanzu gashi sanadin biyayyar tasa komai ya warware masa cikin sauk'i ,duk da yaji dad'in hakan a zuciyarsa amma sai yad'an b'ata fuska cike da shagwab'a yace "No ,nidai Mamma mutafi Abuja kawai ,a k'yale maganar k'anwar Sweety kinji ....,

Mik’ewa tayi tana dariya ta dungure kansa tace” zamuje Abuja Muhammad ,ammafa sai da yawo …..nasan Aure babu inda baya kai mutum amma ni daman gwadaka kawai nayi banida niyyar raba Hassana da Y’ar uwarta da iyayenta zuwa wani gari na daban da zasu d’auki lokaci basuga juna ba ,yanzu zancen da nake ma gidan da zaku zauna tuni angama shirya komai yana unguwar( Oji Quarters)yanzu haka daga can muke ni da Nafeesa da Nabeela da Sulaiman da da mummyn Abdurrahman ,
Tsananin mamaki ne ya kamashi shiyasa yasaki baki yana kallonta ,duk yaushe akaita tsara wad’annan abubuwan basu Sani ba …!?wato har su Hamma Sulaiman sun San a Gombe zasu sauna ba Abuja zasu tafi ba kenan …!?lallai dagashi har Sweetyn da k’anwar Sweetyn sun zama dolaye .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button