HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Babangida da Usman da suka dawo daga siyo kaza sukayi tsuru tsuru ,basusan menene ya faru ba ,sai Alokacin Adda Nabeela takuma magana tace” banga abin tada hankali Dan sageer zai tafi da Hassana Abuja ba ,ni Abuja ai kamar gidace aguna ,tunda ina raka Babansu Auwal sa’i da lokaci musamman idan wani aikin ya taso, Hussaina ki kwantarda hankali ki keda Hassanarki mutu ka raba takalmin kaza “duk suka d’anyi murmushi ,Umma na fad’in ” nifa da naga Hassana na wannan kukan wallahi nazaci wata babbar matsalar ce, Ashe wannan zancen ne ,toh ai sai dai kuyi hak’uri shi Aure babu inda baya kai mutum ,Allah yayi muku albarka ,ya k’ara had’a mana kanku “.

Duk suka amsa da Ameen ,sannan Adda Nabeela ta karb’i kazar da aka siyo me uban yawa ,Usman ya d’akko k’aton tire aka juye aciki ,sai k’amshi takeyi tasha kabej da cucumber da tumatur da albasa.

 Gabad'ayansu har iyayensu kowa yasaka hannu sunaci a kwano d'aya cikin farinciki da walwala ,banda Hussaina da gabad'aya bata cikin nutsuwarta ,hankalinta atashe yake jin rabuwarta da gudan jininta ,haushin sageer takeji sosai sai dai dole tayi hak'uri babu yadda zatayi ,Da Hassana ta lura Hussainar ba ci takeba ,da hannunta ta dinga yabar kazar tana saw a Hussaina a bakinta ,idan hawaye yatawowa Hussaina, sai Hassana ta girgiza mata kai tayi mata murmushi ,duk suna lura dasu amma babu wanda yasake cemusu kanzil .

Hamma sulaiman ne ya ture hannun Aminu yana d’an hararansa yace ” wai kai ba anbaku naku kud’in kazar bane zaka cinye mana tamu ….!?Baba yayi dariya yace “barshi yaci sulaiman ,albarkar iyaye da ta y’an uwa yake nema ” Hamma Aminu yana dariya yace “kamar kuwa kasani Baba ,wani dad’i nakeji inacin Abu tare da Ku wallahi ,nifa tunda nake a duniya bantab’a jin kaza me zak’in wannan ba …Babangida amma dai da Zuma aka gasa kazar nan ko ….!? Dukansu suka kwashe da dariya har safwan ya cire hular kansa yasa a gefen Aminu yace ” Bari nasamaka waigi Hamma Aminu”.

Sai wajen goma na dare su Hamma sulaiman suka tafi gidajensu ,itama Adda Nabeela Babansu Auwal yazo ya d’auketa da tarin kayan arzik’in da ya kawowa Umma da Baba,shi Raman akwaishi da alkairi ,mutum ne me kyauta ,kuma ya d’auki su Baba tamkar sune suka haifeshi.


Da Hamma Aminu Yakoma gida sai Sadiya tak’i kulashi wai tayi fushi ,ta kumbura fuska tana shagwab’a da turo baki,ya lallab’a ya rungume abarsa yana sakin ajiyar zuciya ,a kunnenta yake rad’amata “haba Amsad d’ina …haba k’anwar Aminullah kuma masoyiyarsa …idan kikayi fushi da Aminullah ina zaisa kanshi …kisaki fuskarki na goyaki matata ” ta kwace jikinta tana matso kwalla tace “ba dai nika kashewa waya ba ….!?ya kuma rik’ota yana Shafa wuyanta zuwa fuskarta yace ” wata matsala muka tsaya kashewa a gida fa ,ga Adda Nabeela itama tazo ,shiyasa nakasa tasowa na taho wallahi “tasa yatsansa a bakinta tana d’an cizawa kad’an tace” wace matsala ce tataso a gidan kuma …!?ya d’an lumshe idanu yanajin tsotsar da takewa d’an yatsansa har cikin naman jikinsa yace “hmmm ,sageer ne zai tafi da Hassana Abuja bayan bikinsu ,shinefa Hussaina tad’aga hankalinta tanata kuka tun yanzu ,har tajawo Hamma sulaiman ya mareta ” ta cire hannunsa a bakinta tana fad’awa k’irjinsa da k’arfi ,ya d’an runtse idanu da fad’in “wash !wayyo Allah Na Amsad zaki fasamin k’irji ,hakama fa d’azu Hussaina tafad’o akai sanda Hamma ya mareta ,na rantse idan yayi ciwo zaki rasa na kwanciya kiyi bacci” tasa hannu tana Shafa k’irjin nasa a hankali yadda zaiji dad’i tace “wannan zancen ne ya dakeni wallahi ,banda aure me zai raba yarannan …Ku kanku maza kuna k’ulafucin gida bare su mata ,na rantse har nafara tausaya musu kan lokacin ” yana d’an Shafa bayanta ya d’ora hab’arsa akanta yace”da anyi auren kowacce zakijita lif a jikin mijinta ,kema bagaki kin mannemin ajiki ba ,”tayi dariya tana d’ago kanta ta kalleshi tace”ina kaza ta …!?ya d’an d’aga mata girarsa ya hura mata iskar bakinsa yace “gata nasiyo miki ,amma ki tabbatar idan kikaci kazata ,nima zanci taki kazar ” da sauri tamik’e tana dariya tace “wallahi wayo zakamin kawai ….ni banida wata kaza ..” Shima yayi dariya yana janyo ledar kazar yace “toh zokici Raguwa …har yanzu kin kasa sabawa da Abu d’aya …rannan fa inajin Aunty sakeena nabaki shawara ,har wasu abubuwa naga tabaki ,Amman kin kasa sabawa ” tazo ta zauna ajikinsa yana bata kazar ,saida ta tauna ta had’iye sannan tace “Aikuwa ina k’ok’ari ,kai d’inne bana wasaba ” shima yayi dariyar yana sumbatar goshinta yace “zakiyi bayanine Yarinya “


Wajen sati biyu da fitowar maganar tafiya da Hassana Abuja ,inkaga Hussaina zaka tausaya mata ganin yadda tayi bala’in ramewa ,batada aiki sai kuka ,wajen bacci kuwa k’ank’ame Hassana takeyi ajikinta tanajin babu abinda zai rabata da Y’ar uwarta,Umma tayi lallashin tafita sabgarta ,gidan sai yazama babu dad’i saboda babu karad’in Hussaina,daman itada Babangida ne masu cika gidan da magana ,to shima kewarsu har tafara shigarsa tun kafin bikin ma ,sai dai kaga yaja gefe ya zabga uban tagumi ,Usman kuwa wani k’ara mannemusu yayi ko kad’an bayason ya matsa daga kusada su .

        Rana d'aya aka kawo lefen y'an biyun ,kusan komai da sageer yasawa Hassana to Abdurrahman ma yasawa Hussaina,kaya Nagani nafad'a kuwa , A maimakon farinciki sai Hassana da Hussaina suka zama basuda aiki sai kuka, ganin rabuwarsu da juna na k'ara kusantowa kusa,Ya rage saura wata biyu bikinsu ,zasuyi candy nan da wata d'aya.



  Yawan kukan da Hassana takeyi yasa Hamma sageer yace "sweety mu hak'ura da bin Mamma Abujar nan ....kukan ki yana karya min zuciya  wallahi " tayi murmushi tashare hawayenta ,lokacin suna zaune cikin sabuwar motarsa dal da Mamma tasiya masa, tace"tunda nariga nayi niyyar tafiyar ,ai zantafi ,Hamma sageer ko kai bazakabi mamma ba ni zan bita nacika mata burinta ,kawai dai nasan zanyi kewar da bantab'a yinta ba ...sisina zata Shiga wani hali idan bata ganina ....wazata dinga kallo yana maye mata gurbi na ...!?

Duk da bataso yana tab’ata amma saida yakama hannunta ya runtse a NASA hannun …tana kuka yana kallon hawayenta kamar ya lashesu yakeji ,cikin sanyin murya yace mata “Abdurrahman zai maye mata gurbinki …kamar yadda nima zan maye miki gurbinta ,zan zaame miki komai a rayuwa da yardar Allah …zan mayemiki gurbin Umma da Baba ,zan mayemiki gurbin Adda Nabeela da Hamma sulaiman,zan mayemiki gurbin Hamma Aminu da ya safwan ,Haka zan mayemiki gurbin Babangida da Usman,nayi alk’awari zan zame miki dangi ,iyali ,ahali,zan kula da rayuwarki fiyeda inda bakya zato sweety .

Alokacin kamar ta rungumeshi taji ,sai dai akwai shamaki a tsakani,cikin zubar hawaye tace ” zaka iya wannan sadaukarwar agareni Hamma sageer…!?ya jinjina kai idonsa cikeda soyayya yace”zan iya ,da ikon Allah zan tabbatar da abinda nafad’a”tayi murmushi wani hawayen nazubowa tace”Allah yabaka iko Hamma sageer ……Ubangiji yabaka ikon cika wannan alk’awarin “

Ya amsa da “Ameen ya rabbiy ” ya zarce da nanata mata Kalmar “inasonki sweety na ,wallahi ina tsananin k’aunarki ” ita d’inma dayake cikin shauk’in so take ,tuni ta amsa masa da cewar “nima ina Sonka Hamma sageer ….na rantse ban san iya adadin yawan k’aunarka a zuciya taba……”

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page3⃣9⃣to4⃣0⃣

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W)YACE “DUK WANDA YABAR JUMA’A SAU UKU BAIJE MASALLACI BA ,KAWAI DOMIN KASALA ,KO KUMA DOMIN SASSAUCI DA AL’AMARINTA (JUMA’AR)FACE ALLAH YA KIFE ZUCIYARSA,(SAI DAI INDA WANI DALILI)” DUK WANDA YABAR YIN SALLAR LA’ASAR AYYUKANSA SUN B’ACI

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W)YACE”DUK WANDA YAYI SALLAR ASUBA CIKIN JAMA’A ,SANNAN YA ZAUNA YANATA AMBATON ALLAH HAR FITOWAR RANA,SANNAN YAYI RAKA’A BIYU ZAI SAMI LADA KAMAR HAJJI DA UMRA CIKAKKU

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

Wata d’aya bayan haka sukayi candy a Makaranta ,ranar duk k’awayensu na murna amma su kuka suka dinga yi ,ganin ranar rabuwa nata matsowa agaresu ,duk sun rame saboda k’ulafuci .

Ya Abdurrahman tun yanawa Hussaina dariya har yadawo lallashinta saboda yaga tad’aga hankalinta da yawa ,indai yazo haka zata sakashi a gaba da kukanta ,takance masa “ya Abdurrahman ni duk naji banson yin auren ma …badan komai ba sai banason narabu da rabin raina ,gashi wannan Abokin naka zai k’ara nisantani da ita” sai takuma fashewa da kuka .

      Abdurrahman fuskarsa da jimami yace "aure bafa rabuwane na din din dinba, yawan kukannan da kikeyi yana bani mamaki kamar zaki auri Wanda bakyaso tawan....!? Idan baki daina ba zan had'aki da mummy wallahi ,kinga yadda kika rame kuwa ...!?duk k'ashi yafito miki a wuya ...haka kikeso akaimin ke k'ashi da rai babu wata kyakkyawar tsoka da hannu zai tab'a yaji dad'i......!? Da hawaye a fuskarta amma saida ta harareshi saboda jin abinda yace ,ya tuntsire da dariya yana kai hannu wuyanta yad'an tab'a k'ashin wuyan yace " da gaske fa ...Dan Allah dubi k'ashi b'aro b'aro ....ki kwantarda hankalinki kina tare da Hassanarki babu me rabaku ....yawan kuka da damuwar da kikeyi shine yake sakawa itama tashiga damuwar fa ...wallahi garake kinfita cab'awa ma ...zaki zauna gari d'aya da danginki da iyayenki ...gani yayanki zan zamemiki miji agareki ,zan nunamiki soyayyar da zatasa ki manta da Hassanar ma "ya k'arasa yanai mata gwalo ,aikuwa takuma fasa kuka tana diddira k'afafu cikin kuka tace" wallahi babu wani dad'i ko soyayya da zatasa na manta da ita ....ya Abdurrahman kana raina yawan soyayyar da nake matako ....!?ban san ya ranar rabuwarmu zata kasance ba ...inasonta wallahi ,na rantse ya Abdurrahman ina tsananin k'aunarta "ganin kukan da takeyi yasa yakamo kafad'unta ya rik'e gam, cikin sanyin murya yace " tawan "ta kalleshi fuska duk tafara kumbura saboda tsananin kuka ,ya lumshe ido yabud'e yace " wasa nake miki ,ai nasan soyayyata tayi kad'an ta mantar dake rabin ranki....kiyi hak'uri kinji ,nasan kina tsananin sonta ,nima kuma zanci gaba da tayaki sonta ....."ta d'an fad'a gefen kafad'arsa ta jingina da k'irjinsa tana ajiyar zuciya ,baiyi niyyar rungumeta ba amma haka yasa hannunsa ya rungumeta a jikinsa yana jijjigata ,wata irin soyayya na ratsa jikinsa da tausayinta ,a haka har bacci ya kwasheta a jikinsa saboda bata samun bacci da daddare sai yawan kuka .

Saida baccin yayi nisa sannan ya zameta a jikinsa ya kwantar da ita kan kujerar d’akin nasu,ya gyara mata kwanciyar harda samata filon kujera a k’irjinta ,yagoge mata busassun hawayen fuskarta ,tausayinta yakeji sosai a ransa ,mik’ewa yayi yafito daga d’akin ya tarar da Umma a ktcheen tana girki ,ga Hassana a zaune kan tabarma a tsakar gida tana yanka salat ,Usman kuma a gefenta yanata had’a mata salat d’in yana bata tana yankawa .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button