HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

AIKI ME FALALA????

*MANZON ALLAH (S A W )YACE *DUK WANDA YAYI SALLAH CIKIN YINI DA KUMA DARE SAU GOMA SHA BIYU ,ZA’A GINA MASA GIDA ACIKIN ALJANNA,RAKA’A HUD’U KAFIN SALLAR AZAHAR ,DA RAKA’A BIYU BAYANTA ,SANNAN KUMA RAKA’A BIYU BAYAN SALLAR MAGRIBA ,SANNAN RAKA’A BIYU BAYAN SALLAR ISHA’I ,SAI KUMA RAKA’A BIYU KAFIN SALLAR ASUBA*”

SADAUKARWA GA DUK WANI D’AN GARIN GOMBE STATE ,ALLAH YASAKA MUKU DA ALKAIRI GOMBAWA ,HASSANA D’AN LARABAWA NA K’AUNARKU SOSAI DA SOSAI????????????

BARKANMU DA JUMA’A BABBAR RANA SISTERS ,ALLAH YABAMU ALBARKACIN WANNAN RANA ,INA GAISUWA GA MASOYANA????????????

***Hamma Sageer yashiga tsananin tashin hankali da rud’iya a sanda yaji an d’aura aurensa da Hussaina,jikinsa yana makyarkyata yafad’a k’irjin Abdurrahman yanata juya kai …yarasa inda zai tsoma ransa yaji dad’i ,wani irin tashin hankali yakeji yana d’awainiya dashi tamkar kansa zai juye ….

Yana rungume jikin Abdurrahman wani masifaffen amai ya yunk’uro masa …take yafara kelayashi ajikin Abdurrahman tamkar zai amayar da y’ay’an hanjinsa ….gabad’aya mutanen dake wajen sukayo kansa sunayi masa sannu ….amai sosai yake shekawa hawaye na tsartuwa a fuskarsa ,Abdurrahman rik’e yake dashi duk jikinsu ya b’aci ,Hamma Aminu ne yazo ya janye Sageer daga jikin Abdurrahman ,sai Sageer d’in ya langab’e ajikin Aminu tamkar sumamme ,haka aka d’aukeshi zuwa gidan Aunty Nafeesa jikinsa zafi rau saboda zazzab’in da yakamashi a take ,,Mamma tayiwa doctor waya akan yazo ya duba Sageer …kafin doctor yazo Hamma Aminu da Ya Abdurrahman sun gyarawa Sageer jikinsa Wanda idanunsa ke rufe amma hawaye basu bar gangarowa ba .Likita yana zuwa ya duba shi yasa masa drip yayi masa allurar barci ko Dan k’wak’walwar sa ta huta.

        A can gidama tunda Hussaina taji ance an d'aura aurenta da Hamma Sageer tafad'i sumammiya ,sai da Umma tadinga Shafa mata ruwa a fuska sannan ta farfad'o ,tunda ta farfad'o take wani irin kuka da surutai tarasa ina zata tsoma ranta taji sanyi ...mutuwar Hassana tadawo mata d'anya tamkar ranar da Hassanar ta rasu ,ba ita kad'aiba mutane da dama a ranar mutuwar d'anya ta dawo musu kowa saida yayi kuka, Hamma Sulaiman d'akinsu ya safwan yashige ya kwanta akan katifarsu yana zubda hawaye ,sakeena tabishi har cikin d'akin tasamu guri ta zauna dab dashi ,ganin hawayen da yakeyi sai tazame ta kwanta akan k'irjinsa ...inda taji zuciyarsa na tsananin bugawa ..itama hawayen yazubo mata har ya malala akan k'irjinsa ,a hankali tace "Abban sadauki " yanajin muryarta yasa hannu ya rungume matarsa, ya matseta a k'irjinsa yafashe da kuka yace "sakeenan Sulaiman daman haka mutuwa take da d'aci ....lallai duk Wanda bai San d'acin mutuwa ba toh ba'a tab'ayi masa bane ...iyalin gidanmu muntaso cikin farinciki da kyautatawa juna sakeena ...ko ina sha'awarmu akeyi ana kwatance da gidanmu ...amma yau mutuwa ta wargaza mana farincikin mu ...mutuwa tayi mana gib'i a zuri'ar mu .....mutuwa ta tafi da farincikin mu a wannan lokaci ....na rantse sakeenan Sulaiman bantab'a jin rayuwa tayi min K'unci kamar na wannan lokacin ba ....." Ya kuma fashewa da kuka .

A hankali sakeena tad’aga k’irjinsa ta mik’e zaune ,sannan tasa hannayenta ta kama nasa hannayen tana k’ok’arin mik’ar dashi zaune ,ya yunk’ura ya mik’e zaunen yana tsiyayar hawaye ,ta k’ura masa idanu tana kallon yadda mijin nata ya rame yafita a hayyacinsa ,sai tasa hannayenta ta share masa hawaye tace dashi “shin waye yabaku Hassana ne …!?ya kalleta da jajayen idanunsa yace ” Allah ne yabamu ita “sai tasa hannunta a kyawawan lab’b’ansa tana zagayawa tace ” toh yanzu kuma Allah ya karb’i abarsa hakan sai yazama laifi …!?ya girgiza kai hawayensa nak’ara zubowa ,sai tajawoshi ta d’ora kansa a tsakiyar k’irjinta ,yayinda tad’ora kanta saman kansa, tayi ajiyar zuciya tace “kai da kake babba kak’i kwantar da hankalinka ,kak’i kayi hak’uri da nufin ubangiji inaga k’annenka kuma….!? Kashigo d’aki ka kwanta kana kuka su Yaya kakeso suyi …!?dukanmu fa sai dai mu tattara muyi hak’uri da tsarin ubangiji ,rayuwar ma nawa take Abban sadauki …!?mu kanmu dole watarana akirawomu matattu …zanyi maka tuni akan amanarka, ga Hussaina can na kuka kowa ya rarrasheta tak’iyin shiru ….ya kamata ka kula da amanarka bawai kaima ka k’unshe kanka a d’aki kana kokawa ba .

  Jin maganarta sai yaji k'warin gwiwa ya shigeshi ,ya tabbatar sakeenan sa gaskiya tafad'a masa ,Allah da yabasu Hassana yafisu sonta da k'aunarta ,d'if yaji kukansa ya d'auke ,ya mutstsuke fuskarsa a k'irjin sakeena yana sauke wahalallen numfashi ...sakeena tad'an runtse idanu tana ajiyar zuciya saboda yadda sak'on mijinta ke ratsa jikinta ...yadda yake goga hancinsa tsakanin k'irjinta yayi mugun sanya mata kasala ,saida ya goge fuskar tsaf sannan yad'ago fuskarsa babu hawaye illah idanunsa dake nuna alamar yasha kuka sosai .

Ta kalleshi saitaga fuskarsa tayi mata mugun kyau ,musamman da ya d’anyi mata murmushi ,kawai saita kai bakinta tad’an sumbaci lips d’insa ,sannan tafad’a k’irjinsa ta rungumeshi tanajin son mijinta da tausayinta na tasomata ,ya d’agota daga jikinsa ya tallabe fuskarta yana kallon cikin idanunta ,ya sanyaya murya yace “kiyi hak’uri dani sakeena …nasan a tsukinnan bana baki kulawar da tadace …banida nutsuwane gabad’aya shiyasa …amma kiyi hak’uri dani zuwa wani lokaci kad’an ” saita sunkuyar da kai tana murmushi tace “babu komai mijina …bana tare da damuwar komai ,damuwata itace naganka cikin damuwa ” yace “nadena damuwa sakeenan Sulaiman ,Allah yayi miki albarka ” ta amsa da “Ameen ” sannan ta zarce dacewa “ina sonka mijina” shima ya amsa da “nima haka …Sulaiman mallakin kine sakeena …jeki ki kawomin Hussaina d’akin nan kinji “

     Haka sakeena ta mik'e tafice daga d'akin taje tatawo da Hussaina wadda tsananin kuka yakusa makantar da idanunta ,domin dusu dusu take gani ,Hamma Sulaiman ya zaunarda ita kusa dashi yadinga rarrashinta da nasiha ,ayoyi da hadisai ya dinga jawomata har jikinta yayi sanyi ta rage kukan ,amma idan tatuna a yanzu tazama matar Sageer ba Abdurrahman ba saitaji tamkar tamace tahuta itama ,ranar ad'akin suka wuni shida Hussaina sai Babangida da Usman da suma sukazo d'akin suka rakub'e ,ranar ko masallaci Hamma Sulaiman baijeba a d'akin yasa sukayi alwala yajasu sallah ...abinci kuwa har d'akin Aunty sakeena takawo musu ,yasasu a gaba yana basu abaki yana rarrashin k'annen nasa... Shikuwa ko loma d'aya ya kasaci ,sai Usman ne yadinga d'ebowa da cokali yana bawa Hamman shima ,Hussaina kuwa da k'yar take cin abincin jinshi takeyi tamkar magani acikin bakinta .

Hamma Aminu da ya safwan da ya Abdurrahman sunacan gidan Aunty nafeesa d’akin da Hamma Sageer yake ana k’ok’arin ceto rayuwarsa.


 Kimanin kwana goma Sha biyu kenan da d'aura auren su ,dukkansu har zuwa lokacin basa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ,inka gansu duk sun zabge sun k'ara ramewa .....kuma har alokacin Sageer da Hussaina basu k'ara ganin juna ba ,ko gidansu Hassana yaje domin gaida Baba baya ganinta ,kullum tana d'aki a k'unshe cikin k'uncin zuciya da rashin walwala ,mutuwar Hassana tatafi da duk wata walwala da farincikinta ,magana ma idan ba tazama doleba bayinta takeba ,babu abinda tasa a gaba idan ba salloli da yiwa Hassanarta addu'a ba ,sai kuma fatan mutuwa da takeyiwa kanta a kullum domin tanaji azuciyarta tamkar almara wai tazama matar Sageer .....Abdurrahman ya haramta agareta .



        Ranar da daddare Hamma Sageer na zaune kusada Baba a tsakargida yazo gaishesu kamar yadda yasaba ,Umma takawowa Baba tuwon sa gabansa bayan Hamma sageer ya gaisheta sun k'arayiwa juna ta'aziyya ,kansa a sunkuye hawaye nason cikowa idanunsa ,Baba ne yace "matso muci abinci Sageer ...yau masu tayani cin abincin duk basanan ,nasaba cin abinci da mutane banason ci ni kad'ai " Hamma sageer yad'an girgiza kai yace"alhamdulillah Baba bana tareda yunwa bazan iyaci ba "sai Baban yazura masa idanu yana kallonsa ,daga bisani ya girgiza kansa yace " duk Wanda yadubeka yasan baka cin abinci sageer ...dubi yadda karame kamar ba kaiba ...wannan horon da kukewa juna kaida Hussainar duk fa ba daidai bane ...kamarfa kuna nuna fushi da yin Allah ne ...meyasa bazakuyi hak'uri da k'addarar Ku ba ....!?hawaye ya tsiyayo akan fuskar Hamma sageer yasa hannu yana gogewa ,Baba yaci gaba da cewa "ni kaina mahaifinta nida mahaifiyarta mun hak'ura da rashinta addu'a kullum muke Binta dashi ..Ku tayaya zaku sawa ranku damuwa Ku hana zukatanku walwala ....!?ina lura da duk wani Abu dayake faruwa tsakaninka da matarka sageer ,tunda aka d'aura aurenku baka tab'a nemanta Dan kuga juna ba ....kullum zakazo gidannan ka gaishemu amma baka tab'a Neman Inda takeba ...kasani cewa Kaine namiji kuma kai Allah yabawa ikon kiwonta da kulawa da ita a yanzu ....a lissafina yau saura kwana biyu Ku wuce abuja fa ....tambayata agareka shine " shin idan kunje abujar haka zaku cigaba da kasancewa kuna gaba da juna tamkar ba ma'aurata ba ....!?sageer ina ganinka tamkar su Sulaiman ne a idanuna, shiyasa duk wata gaskiya zan iya fad'amaka ita kodan ka tsira "Hamma Sageer yak'ara duk'ar da kansa k'asa zuciyarsa na bugawa yace " kayi hak'uri Baba ,insha Allahu zan gyara "sai Baban yayi murmushi  yace" to sageer Allah yabaka iko yayi maka albarka ,yanzu tunda bazaka ci abincin ba katashi kashiga d'akinsu Hussainar kuga juna ...itama kullum tana d'aka bata fitowa taga hasken rana kamar matar liman "gaban Hamma Sageer ya tsananta bugawa ...shikuwa da wane ido zai dubi Hussaina....!? A matsayinta na matarsa ....!?ko k'anwar masoyiyarsa ...!?ko kuma masoyiyar Abokinsa ...!?yayi shiru kansa ak'asa k'irjinsa na tsananin bugawa ,sai da Baban yakuma maimaita masa sannan yayi k'ok'arin mik'ewa a hankali ,yafara  takawa cikin tafiyar nutsuwa tamkar yana tausayin k'asa yanufi d'akinsu Hussainar ...Baba yabishi da kallon tausayi yana girgiza kansa ,sannan yasa baki yayi kiran Umma yace ta mayar masa da abincin d'akinsa a can zaici .

Kamar bazai shigaba ,amma haka ya daure ya d’aga labulen d’akin tareda sallama cikin k’aramar murya ,kwance take a k’asan carpet d’in d’akin male male cikin wata k’aramar riga iya gwiwa tamkar ta bacci ,tasa hannayenta ta rufe fuskarta dasu da alamun tunani takeyi ko bacci tafara ,,ganinta ahaka yasa yad’an runtse idanunsa yana kawarda kansa cikin dukan zuciya .

Ya D’an cije lips d’insa sannan yak’ara d’aga murya yakuma sallama akaro na biyu sautin muryarsa yasata d’age hannanyenta zuwa duban Inda yake tsaye,a razane tafara k’okarin mik’ewa tsaye saboda kid’imewa …bata tab’a zaton zai iya shigowa d’akin awannan lokacin ba …garin mik’ewa rigar jikinta ta hard’eta tatafi luuuu zata kifa ,sai yaji azuciyarsa tamkar Hassanarsa CE zata fad’i da wani irin zafin nama yayi hanzarin tarota tafad’a jikinsa …hannayenta bisa kan wuyansa yayinda nasa hannun yake kan kafad’unta yarik’eta GAM,kallon fuskokin junansu sukeyi zuciyarsu na tsananin bugawa har suna iya jiyowa da harbawa ,Hamma Sageer ya k’urawa fuskarta idanu yana kallon fuskar Hassanarsa a tata fuskar ,ya lumshe idanunsa yana sakin ajiyar zuciya yayinda Hussaina take amatuk’ar tsorace tamkar tasaki fitsari takeji ,idanunsa alumshe yafara yin k’asa da Kansa zuwa tata fuskar domin yahad’e fuskokinsu ,Hussaina tazaro idanunta awarwaje hawaye naciko idanunta ,bata k’ara tsorata ba saida taji saukar fuskar Hamma Sageer akan tata fuskar ,ya had’e goshinsu waje d’aya ,hancinsu na gogar juna …bakinsa dab da nata suna shek’ar numfashin juna ,itama lumshe idanuwanta tayi saboda yadda numfashinsa yake ratsa jikinta ,saukar bakinsa kan lips d’inta yasata hanzarin bud’e idanuwa hawaye na zubowa ,jikinta na matuk’ar rawa tabud’e baki cikin kyarmar murya tace “Hamma Sageer ba sweetyn kabace fa bud’e idanunka kagani ….” Cikin slow yabud’e idanunsa yana sauke wani irin gajiyayyen numfashi ,ya sauke idanunsa akan fuskarta yana kallon yadda dimple d’inta kemotsawa idanunta a warwaje ,sai lokacin zuciyarsa ke tunasar dashi bafa Hassanar sa bace ,ba sweetynsa bace ….da hanzari yasaketa yana tureta daga jikinsa da k’arfi ,saura kad’an tazube k’asa Allah ya taimaka ta tsaya da k’afafunta .

Juya mata baya yayi jikinsa na rawa .

  Haushin Kansa ya kamashi ,hawaye yaciko idanunsa har ya kwararo akan kyakkyawar fuskarsa ,da wata irin murya yace mata "kiyi hanzarin gama shirye shiryenki ....insha Allah jibi zamu wuce abuja " yana fad'in hakan yasa kai yafice daga d'akin da hanzarinsa yana goge hawaye.

Tamkar aradu haka taji saukar maganarsa ,gabad’aya ta manta da batun wata abuja ,Hassana tatafi ta barta ,Ya Abdurrahman ya gujeta ,yanzu kuma ana shirin rabata da iyayenta da danginta gabad’aya ….!?wace irin k’addara da jarrabawa CE take bibiyarta haka ….!?

Sai ta d’ora hannayenta aka tarushe da wani matsanancin kuka tana kiran sunan Allah …….????!

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page5⃣3⃣to5⃣4⃣

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

TUNASARWA????

JARRABAWAR DA ZA’A YIWA MUMINAI

AK’ARSHEN RANAR ALK’IYAMA KAFIRAI ZASUBI ABINDA SUKE BAUTAWA SAI SU KAISU HAR WUTA,JAMA’A JAMA’A TAMKAR GARKEN DABBOBI,ZASU SHIGA DA K’AFAFUNSU KO DA FUSKOKINSU,BABU WANDA ZAI SAURA SAI MUMINAI DA MUNAFUKAI ,SAI UBANGIJI YAZO MUSU YACE “ME KUKE JIRA ?SAI SUCE ” MUNA TSIMAYAN UBANGIJINMU NE ,SAI SU GANSHI TA KWABRINSA IDAN YA YAYESHI ,SAI SU FAD’I SUYI SUJJADA ,SAI DAI MUNAFUKAI BAZASU IYA YIN SUJJADAR BA ,KAMAR YADDA ALLAH YACE “RANAR DA ZA’A YAYE GA BARIN KWABRI KUMA AKIRASU ZUWA SUJJADA BA ZASU IYABA”, SANNAN SAI SU BISHI SAIYA SANYA SIRAD’I KUNA A GWADA MUSU HASKE.SA’ANNAN A D’AUKE HASKEN MUNAFUKAI

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button