HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

   " For give me "yafad'i kansa a sunkuye ," Don Allah ki yafemin nayi alk'awari bazan sake ba tunda bakyaso ...."ya d'ago kansa yana kallon fuskarta duk ya jishi cikin damuwa ganin yadda take hawaye .

“Da hawayen ta dubeshi muryarta na rawa tace “Hamma sageer ” yaji kiran har k’wak’walwar kansa shiyasa ya kasa amsawa illa zuba mata ido da yayi a marairaice …itama kallonsa takeyi tace “saboda banaso zaka daina …..!?da sauri ya kad’amata kansa alamar hakane …sai tayi murmushi me ciwo hawayenta ya k’ara zubowa tace” nikuma banaso kadena saboda ni ,nafison kadena saboda Allah …”ya kuma binta da kallo yana jinta can cikin zuciyarsa …sai kawai yasa hannu cikin aljihunsa yafito da handkerchief d’insa me kyau ya mik’o mata yanai mata nuni tashare hawayen fuskarta …tamik’o hannun yasaka mata yanata kallon k’unshin da ke hannunta…tana goge fuskar takuma bud’e baki tace dashi “meyasa bana ganinka kwana biyu …meyasa kadena fitowa waje….!? Kansa a sunkuye yace ” banason nafito kiganni da sigari ne …shiyasa nazab’i zaman gida saboda inajin kunyar kiganni da ita “wani miskilin murmushi tayi tace ” Hamma sageer “a hankali yad’ago ya kalleta ,tace ” kanajin kunyar na ganka kana shan sigari ko …!?ya gyad’a mata kai ,ta juyar da kanta gefe tana kallon Flowers d’in da aka shuka a harabar gidan tace “toh meyasa bakajin kunyar Allah …!?bayan kasan ko ni ban gankaba …shi yana kallonka a duk inda kake …..!? Kamata yayi kaji kunyar Allah da tsoran sa baniba “wani mugun tsoro ya daki zuciyarsa …lallai Hassana tafara tunasar dashi abinda ya manta ….take shima hawayen yaciko idanunsa duk yayi kalar tausayi .

 Ganin hakan sai zuciyar Hassana tafara jin dad'i.... Da alamun tafara nasara akan sageer ganin yadda jikinsa yafara sanyi ...shiyasa ta jawo kujerun bayansu ta nuna masa d'aya tace " Hamma sageer zauna kaji wata magana"baiyi musu ba yaja ya zauna jikinsa a sanyaye yanata kallonta ...itama taja d'aya ta zauna sannan ta fuskance shi tace "Hamma sageer " ya k'ara ware idanuwansa a kanta bai amsa ba ...kallon da yake mata yasa jikinta rawa ..shiyasa ta sunkuyar da kanta tafara magana cikin nutsuwa da muryar Jan hankali tace "kasan me Hamma sageer ....!?wata Y'ar naseeha nakeso nayi mana ...nasan bakasan koni wacece ba ..kuma nasan dole zakaita mamakin menene dalilina na shigowa rayuwar ka ....!?Hamma sageer tun ranar da nafara ganinka najika a zuciya ta tamkar jinina ,kuma naji bazan iya barinka a halin da kake ciki ba saboda daga ganinka nasan cewar k'addara ce tasaka ciki ba halayyarka ce ta asali ba .....ilai kuwa Ashe hakane ...karkayi mamakin cewa nasan labarin ka kuma nasan menene yasaka a wannan halin ......"

Ta d’ago ta kalleshi saitaga gabad’aya yanayinsa ya sauya yanai mata duban mamaki fuskarsa d’auke da tashin hankali iri iri ,kallon da tayi masa yasashi runtse idanu …minti d’aya bayan haka yabud’esu tare da kwararowar hawaye a kan fuskarsa …hannayensa bisa k’irjinsa yadafe saitin zuciyarsa saboda bugun da takeyi kamar zata fad’o….

Sai tak’ara duk’ar da kanta tacigaba “hak’ik’a bazan hanaka kuka ba Hamma sageer ..saboda nima da naji labarinka nayi kukan saboda tausayinka …sai dai kasani k’addarar kace haka ..daman tuni Allah yarubuta hakan zata faru amma ta silar “mamma “..Hamma sageer yadda da k’addara kyakkyawa ko Mummuna tilas ne wajibi ne tunda suna cikin shika shikan imani….dole ne kayi imani da k’addarar da ta sameka kan cewa dukkan alkairi ko sharri da ya kasance da kai ,to da k’addarawar Allah ne kuma da hukuntawarsa ,domin shi Allah mai k’addara abinda yakeso ne da kuma abinda ya nufa …manzon Allah (S A W)yace ” da zaka ciyar da kwatankwacin dutsen uhudu na zinare cikin d’aukaka addinin Allah ,bazai karb’a daga gareka ba har saikayi imani da k’addara tukunna ,kuma kasan cewar dukkan abinda yasameka bai zamo me kuskure makaba,abinda ya kuskure maka kuma ,dama can bai kasance zai sameka ba ….da zaka mutu ba akan wannan ba da kashiga wuta “

Bayan imani da k’addara akwai hak’uri a gaba …Hamma sageer bakayi hak’uri da abinda yasameka na rasa mahaifinka ba ,saima zuciyarka da zugar abokinka sukasa kafad’a halaka kanaji kana gani …Allah (S W A)yana cewa acikin alk’ur’aninsa me girma “Ana cikawa masu hak’uri ladansu ba tare da k’ididdiga ba ” haka kuma manzon Allah (S A W)yace “duk Wanda yayi k’ok’arin hak’uri ,Allah zai taimaka masa wajen yin hak’urin …kuma babu wata kyauta da aka bawa d’ayanku da takai kyautar hak’uri”

Wallahi Hamma sageer da kayi hak'uri a lokacin da yafi maka akan rayuwar da ka afka kanka ciki...shaye shaye babban zunubi ne me girma ,musamman abinda mutum zaisha ya kawar masa da hankali yasashi maye...ko acikin alk'ur'ani me girma Allah (S W A)Ya ambaci kayan maye da aikin shaid'an ...harma Allah yayi mana umarnin mugujesu zamu rabauta "duk da haka Hamma sageer inason kadena shan kayan maye saboda Allah ...kayi hak'uri da k'addarar da ta sameka ...sannan katubarwa Allah abisa laifin da ka aikata...ko domin albishir d'in da Annabi (S A W )Yayi mana akan cewa " Ana share munanan ayyuka ,akuma kankaresu da wasu al'amura,daga ciki akwai .

1 ,yin tuba na gaskiya
2 ,yin istigfari
3 ,aikata kyawawan ayyuka
4 ,jarabtuwa da wasu musibu
5 ,yin sadaka
6 ,addu’ar d’an uwa.

  Wad'annan ayyukan duk suna sawa a share munanan ayyukan mutum ...hakanan sab'on Allah ko aikata zunubi sunada munanan tasiri masu yawa akan mutum ,tasirinsu akan zuciya shine,lallai suna gadar da kad'aicin zuciya da duhun zuciya ,da kuma k'ask'anci da cuta ,(rashin lafiyar zuciya)kuma sukan kangeshi daga ubangiji Allah ...kamar yadda ka kasance kullum cikin kad'aici da duhun zuciya .


   Tasirinsu ga addini kuma shine ,sab'o yana gadar da wani sab'on ,yana kuma hana yin biyayya ,haka kuma yakan katange bawa daga samun gajiyar adduo'in da manzon Allah (S A W)yayiwa muminai ,da wadda mala'iku keyiwa muminai .


   Tasirinsu ga arzik'i shine ,lallai zunubi (sab'o)yana hana arzik'i ,kuma yana gusar da ni'ima da albarkar dukiya.

Hamma sageer ko da damuwa tacika zuciyarka ba shaye shaye ne mafita agareka ba ,kamar yadda faruk ya rinjayi tunaninka ya sa kabi ra’ayinsa ….akwai addu’ar da Annabi (S A W)ya koya mana wadda idan kana cikin damuwa ka karantata …Annabi yace “matuk’ar ka karantata Allah zai tafiyar maka da damuwarka yakuma musanya maka da farinciki a maimakon damuwar” wannan addu’ar itace…..!

Allahumma inni abduka ibn abdika,wabni amatika,nasiyati bi yadika,madhin fiha hukmuka,adlun fiha kk’ada’uka.As’aluka bi kulli min huwa laka,sammaita bihi nafsaka,au allamtahu ahdan min kalk’ika,au anzaltahu fi kitabika,au ista’asarta bihi fi ilmil ghaibi indaka,an taj’alil k’ur’anil azima rabi’a k’albi,wa nura sadri,wa ja’al huzni,wa zahaba hammi

Hamma sageer a duk lokacin da kasamu kanka cikin damuwa ko wani bak’inciki ,to ka daure ka karanta wannan addu’ar ,insha Allah zaka sami yayewar damuwarka ….ka daure ka kai zuciyarka nesa…kuma kafi k’arfin zuciyar ta hanyar hanata abinda takeso matuk’ar sab’on Allah ne …..”

    A bazata taji hamma sageer ya kama hannunta ya rik'e gam, jikinta ya d'auki wani irin mugun rawa saboda yadda taushin hannunsa ya ratsa nata, tunda take babu wani namiji da yatab'a rik'e hannunta idan ba y'an uwanta ko mahaifin taba...shiyasa ta rud'e tad'ago a gigice tana dubansa ,hawaye tagani sosai akan kyakkyawar fuskarsa suna gudu ...gabad'aya idanunsa sun sauya kala ,ganin sai kuka yakeyi kuma yak'i sakar mata hannu yasa tayi k'undunbalar magana "Hamma sageer ko rik'e min hannun nan da kayi sab'on Allah ne ..kai d'in ba muharramina bane ...kuma min kai munzalin da yazama haramun a tsakanin mu jikin wani ya tab'a wani ...ka sakar min hannu ka kumayi istigfari akan hakan "

A hankali yasaki hannun nata muryarsa na rawa ya ambaci” Astagfirullah ya Allah”sannan yayi baya ya kwantar da kansa a jikin kujerar da yake zaune idanunsa a lumshe yafara magana da raunin murya “Nagodewa Allah da yasa ban kasance muharrami a GAREKl ba…wallahi Allah yayi miki wata baiwa da ke kanki bakisan kinada itaba,irinki na dad’e ina nema …irinki najima ina addu’ar Allah yabani …irinki zuciya ta kullum take mararin samu….daman akwai irinki a rayuwa …!?Ashe akwai mata masu irin wannan kyawun halin….!?na zaci ai duk halin mata iri d’aya ne …daga masu muzgunawa mazajen su sai wad’anda burinsu kayi lalata dasu ,musamman irin Matan da suke damuna a school….” Ashe ba haka bane ….!?Ashe akwai mata masu ilimin addini wad’anda suke aiki da iliminsu …..ni bazan iya godiya agareki bisa k’ok’arin da kikayi a kaina ba …sai dai zan tayimiki addu’a zuwa k’arshen numfashi na …Alfarma d’aya zan nema agareki …dafatan kuma zakiyimin ita……!?

 Har lokacin idanunsa a rufe suke, ni mamakin yadda yabud'e baki yake magana me tsawo nake ,saboda tun had'uwar mu bai tab'a magana me tsawo irin hakaba ,Ashe Hamma sageer na magana haka ...!?


    Jin nayi shiru yasa ya bud'e idanunsa akaina yana faman kallona ...tsigar jikina tayi wani irin tashi saboda yadda kalar idanunsa ta wani juye... Ina k'ok'arin kawar da kaina naji yayi magana da k'aramar murya "in tambayeki alfarmar zakiyi min ....!?

Nace ina d’an gyara zamana”

“Ka tambaya indai batafi k’arfi naba kuma bata sab’awa addini da shari’a ba zanyi maka Hamma sageer “kaina a k’asa na amsa masa.

  "So nake ki yarda dani ,ki amince dani ,ki zama MATAR AURE NA "

Kalaman Hamma sageer kenan a gareni da suka kusa kurumta min kunnena….kunnena yafara yimin gizo kamar banji dai dai ba …shiyasa nad’ago da niyyar ince ya maimaita min maganarsa …ina d’agowa na hangi Aunty Nafeesa na tawowa inda muke……..!

kuyi hak’uri yanayin posting d’ina zai canja ,ba koyaushe zaku dinga samuba saboda mun koma makaranta,

Comment
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

TYPING????

???????? HASSANA????????

              *DA*

❣???? HUSSAINA????❣


® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page2⃣5⃣to2⃣6⃣

WATTPAD:hassana3329

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W )YACE “MAFI SHARRIN WURIN ZAMA A WURIN ALLAH RANAR TASHIN K’IYAMA MUTUMIN DA YA CUD’ANYA DA MATARSA KUMA ITAMA TA CUD’ANYA DASHI ,SANNAN KUMA SAI YA RINK’A BAYYANA ASIRINTA A WAJE

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W)YACE ” WANDA YA ROK’I ALLAH MUTUWAR SHAHADA BISA GASKIYA ,TO ALLAH ZAI BASHI MATSAYIN SHAHIDI KODA KUWA YA MUTU NE A BISA SHIMFID’ARSA

DEDICATED TO

NABEELA DIKKO MARUBUCIYAR(TARBIYYA)INA YINKI SOSAI ,NAGODE DA K’AUNARKI NABEELA????????????

   ****Tana k'arasowa inda suke Hamma sageer yace"Aunty Nafeesa kitayani murna nayi matar aure "kawai sai Aunty Nafeesan tabishi da ido tana Neman k'arin bayani ...yayinda mamakin Hamma sageer yacika zuciyar Hassana  matuk'a.

Da yaga bata ganeba sai ya nuna mata ni yana wani irin murmushi me narkar da zuciya yace ” ita nakeso Aunty na ,na rantse farat d’aya tagama da zuciyar sageer Aunty “wata muguwar kunya ta lullub’eni ganin yadda yakewa Aunty Nafeesa shagwab’a yana magana yana nunani da hannunsa .

  Murmushi me kama da dariya Aunty Nafeesa tayi ,a hankali kuma ta tsuguna gaban kujerun da muke ,nikuma tuni na kife kaina a kan cinyata, na k'udundune saboda kunyar ta da ta lullub'eni ....yana ganin ta tsuguna yakuma jawo kujerar sa dab da ita yana d'an d'ora kansa akan kafad'arta ...dai dai kunnenta ya tsayar da bakinsa yafara rad'a mata magana" kitayani yak'in yad'a manufa Aunty na ,wannan yarinyar fa cikin y'an mintuna tagama ragargaza zuciyar k'aninki ...yaseen ban tab'a cin karo da mace me balagar harshe da fasaha irin taba "da Aunty Nafeesa taga k'anin nata ya zauce nikuma nak'i d'ago kaina ,kawai sai tasa hannunta a gefen cinyata tace " Hassana Ashe da na kirawoki gun sageer kika zauna kuna shan soyayya ....!?wato ma kin manta dani kenan ...!?ai tana jin abinda Aunty Nafeesa tace tayi hanzarin d'agowa tana rantsuwa tana d'aga hannaye "wallahi Aunty Nafeesa ba soyayya na tsaya yi da Hamma sageer ba ....kin ..." Wani d'an haske wal ya katse mata maganarta tad'an juya saitaga waya a hannun sageer ya saita ta yana ta d'aukarta photo ,da sauri ta mik'e tsaye kanta a k'asa tace "Aunty Nafeesa muje inji kiran naki ko ...!?

Shima da saurin ya mik’e ya matso dab dani kamar zai ture Aunty Nafeesa dake kusa dani yace ” ina zaki ….!?baki bani amsa bafa please ….bazaki tafi ba sai naji amsar ki ….do you love me ….!?don Allah ki amsamin…”

      Ya k'ara bata kunya sosai  ,tasa hannayenta tarufe fuskarata,....shiyasa ya dubi Aunty Nafeesa a marairaice yaja hannunta yana cewa"kefa takejin kunya shine tak'i sakewa ....don Allah Aunty shiga gida ko zatayi magana "bai tsaya ba saida yakaita k'ofar shiga falo sannan yasaki hannunta yana cewa " shiga ciki Aunty ...zakuyi magana latter yanzun time d'inane "

Aunty Nafeesa naji nagani haka tashige ciki tana murmushi da godewa Allah …rabon da taga sageer cikin irin wannan yanayin har ta manta …bayan farincikin da ta hanga a idanunsa harda gingimemiyar soyayya ta hanga.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button