HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Umma wasu hawaye ne suka zubo mata na rashin d’iyarta ,kamar yadda k’arfin imani da hak’uri suka shigi Baba haka itama tasamu wannan falalar ,bata gigice ba ko kad’an illah innalillahi da taita maimaitawa a bakinta tana hawaye ,a k’arshe buta ta d’auka ta shige band’aki ta d’aura cikakkiyar alwala tazo ta d’au carbi tafara nemawa y’arta Rahama da gafara agurin ubangiji.

Abdurrahman kuwa k’ofa ya nufa zai fita a gigice ,amma Adda Nabeela tak’i barinsa ta rik’eshi gagam ,kuka yakeyi yana fad’in” ban San halinda sageer da tawan zasu kasance ba ,Adda Nabeela kibarni naje na gansu …”amma inah !Adda Nabeela tace”yayi hak’uri ,yanzu suma zasu tawo ….”ita kanta Adda Nabeelan takusa rasa tunaninta .

Aunty sakeena ma da Zahra kuka suke sosai ,sakeena na tuna maganar Hamma sulaiman da yayi da asubahin ranar ,Ashe wannan jarrabawar Allah zai aiko da ita shiyasa yake kuka tun kafin abin yafaru .

Mutuwa tambari !mutuwar rigar kowa !duk wani mahaluk’i sai ya d’ad’anata kamar yadda Allah (S W A)ya ambata ,kafin kaceme rasuwar Hassana ta baza unguwar herwagana ,duk Wanda yaji wannan mutuwar sai, ya koka ya zubda hawaye,kowa yabon halayenta yakeyi a wannan unguwa ,mutuwar ta tsayawa kowa a zuciya ,alokacin da ake cikin shagalin bikinta Allah ya d’auki abarsa ,gidan da k’ofar gidan yafara cika d’ankam da mutane ,musamman rana ta juma’a duk maza suna gida ana shirin tafiya masallacin juma’ar unguwar domin gabatar da sallar juma’a.

       Can asibiti kuwa haka Baba yayita cuku cuku har suka samu aka basu gawar Hassana ,a motar asibitin suka tawo gaba d'aya saboda Hamma sulaiman ba zai iya tuk'a tasa motar ba sai a asibitin ya barta ,Hamma sageer yana kusa da gawar yana aikin kallonta k'wak'walwar kansa na juyawa ,ji yakeyi tamkar barci yakeyi yake mummunan mafarki ba gaskiya bane ,tun yana kuka har hawayen ya k'afe sai bala'in juyawa da hajijiya da kansa yake masa ,Hussaina kuwa na jikin Mamma a rungume a cikin motar ,tun bayan da kunnuwanta suka jiye mata mutuwar rabin jikinta shikenan komai ya tsaya mata cak, bakinta ya b'ame takasa furta komai ,haka sassan jikinta ta kasa motsa ko ina, tanajin duk maganganun da sukeyi amma bata fuskantar komai a ciki ,Hamma sulaiman kansa bisa cinyoyinsa yarasa inda zai tsoma ransa yaji sanyi ,zuciyarsa ta dameshi da tsananin ciwo.

Isowar su gidan sai gidan ya kuma kacamewa da kuka, musamman da Baba yashigo shida Hamma sulaiman sai sauran ahalin nasa da k’ananan jikokinsa sukayi kansa suna ta kuka ,baiyi niyyar kuka ba amma haka hawaye ya zubo masa ,ya tarbesu yana rungumarsu yanata basu hak’uri ,Baba har gaban Umma yaje ya tsuguna tana zaune da carbi a hannunta tana shatatar hawaye,cikin sanyin murya yace “fad’imatu muyi hak’uri ,nagode miki da nazo na sameki cikin nutsuwar ki ,kicigaba da yi mata addu’a ita tafi buk’ata a halin yanzu ” sai takuma fashewa da kuka tanata ambatar” innalillahi wa inna ilaihirraji’un “Baba ya mik’e da hanzari saboda yadda yaji zuciyarsa tak’ara karyewa ,sai yaji ankamo hannunsa ….yana waiwayawa sai yaga Usman ne ya rik’eshi ,ya kalli Usman d’in yadda yaga yadda yaketa had’iyar zuciya yana gurshek’en kuka …sai Baban ya rungumeshi a jikinsa yana Shafa bayansa ,Usman ya d’ago kansa yace da Baba cikin kuka ” Baba ka yafewa Adda Hassana …sanda zamu baro asibitin ta rik’e hannuna tace na nema mata afuwa a gurin kowa “Baba yace ” na yafemata usmanu ,idan da akwai abinda yafi yafiya ma nayiwa Hassanata “sai Usman yajuya ya kalli Umma yace”Umma kema kinyi mata afuwar …!?Umma da kuka yaci k’arfinta takasa magana sai jijjigawa usman kai tayi ,haka Usman ya dinga bin mutane yana nemarwa Hassana yafiyarsu da afuwarsu ,kowa yace ya yafemata ,kasancewar Hassanar bame yawan kwaramniya bace shiyasa ma batacika yiwa mutane laifi ba .A k’arshe Usman yayi maganar da tabawa kowa mamaki ,domin cikin kuka yace ” inama nine na mutu ba Adda Hassana ba ,saboda ita Babba ce tafini amfani ,gashi yau saura kwana biyu bikinta da Hamma sageer ,yanzu ya Hamma sageer zaiyi ….!?sai kuma ya fad’a jikin Umma yacigaba da kukansa.

D’akin Baba aka wuce da gawarta ,za’a shiryata a sallaceta sannan akaita gidanta na gaskiya ,inda kowa na duniya sai yaje ,babba da yaro ,tsohuwa ko tsoho ,mata da maza ,yara da manya kowa sai yashiga wannan rami ????,Hamma sageer yaso shiga d’akin amma Baba yace ya Abdurrahman ya kamashi ya rik’eshi ,haka ya rungumeshi a jikinsa yanajin yadda jikin sageer d’in yayi wani irin zafi ,daman gashi bashida lafiya ga kuma dukan da mutuwa tayi masa,su Hamma sulaiman kuwa da Hamma Aminu da ya safwan da Babangida duk suna k’ofar gida an shimfid’a tabarmi an zazzauna jugum jugum ,wasu kuma nata alwala ,kasancewar za’a kai gawar masallacin juma’ar unguwar yadda da an idar da sallar juma’a sai a sallaceta a masallacin,mazan unguwar kansu mutuwar Hassana ta dakesu ba kad’an ba ,kowa kagani da hawaye a fuskarsa .

Cikin gida kuwa matane dank’am sun had’a baki sai karanta suratul yaseen da tabara (suratul mulk)sukeyi ,yayinda akayiwa Hassana wanka… Aka shiryata cikin likkafanin ta na tafiya gidanta na gaskiya ,a lokacin ne Baba yasa aka kirawo su Hamma sulaiman a waje, suka shiga suka zagaye gawar Hassana suna zuba mata addu’a iri iri da nema mata sauk’i da rahamar Allah ,suka karanta mata alk’ur’ani me girma ,sunayi suna kuka me tada hankali ,saida Baba yaga kukansu yayi yawa sannan yasa aka fita dasu Dan saida Babangida Yakuma sumewa,babu abinda yake hangowa irin sanda hatsarin yafaru ,bai tab’a bawa Hassana mutuwa ba ganin ko ciwo ita bataji ba ,aka d’aukeshi aka fita dashi aka yayyafa masa ruwa ya farfad’o ,sai kuma ya dinga shek’a amai kamar zai mutu shima ,nan da nan jikinsa ya d’auki mugun zazzab’i .

Aka taso Umma itama tazo kan gawar ,tayi mata addu’a mai d’umbun yawa ,a k’arshe tafashe da kuka cikin raunin zuciya take fad’in “na yafemiki y’ata ,Hassana ta Allah yabaki sa’ar tafiya yasa kishiga k’abarinki a sa’a ,Allah yajik’anki yayi miki rahamarsa ,Allah ya yafemiki Hassanata ” haka umma taita kuka da surutai da k’yar mummy Aisha tafita da ita.

Aka shiga da Hamma sageer ,ya tsuguna a gabanta yarasa mema zai karanta ,duk wasu addu’o’i ya mantasu tsabar rud’ewa ,yawanci ma addu’o’in da ya iya Hassanar ce ta koya masa, saida Baba yace “sageer kayi hak’uri ka karanta mata abinda ya sawwak’a shine gatan da zakayi mata ka Nuna mata soyayya ” kamar an tunkud’o adduo’in cikin kansa kawai yaji ya runtse idanu yafara karantosu da k’arfi ,muryarsa ta karad’e gidan yanata zazzaga addua cikin kuka da Nuna kewar masoyiyarsa ,ya dad’e yana addu’a sannan yasa tafukan hannunsa yarufe fuskarsa jikinsa na matuk’ar rawa yace “kin yimin gatan da aduniya narasa me yimin shi alokacin ,kin soni a lokacin da duniya take k’yamata ,kin nunamin k’auna tamkar ciki d’aya muka fito ,saida lokaci yazo dab kizama tawa sai kika tafi kika barni …wanene zaicigaba da yimin abinda kika fara…!?wanene zai cigaba da nunamin soyayya kamar yadda kika yimin…!?wanene zai cigaba da yimin nasiha da d’orani akan hanyar dai dai …..!?sweety na kintafi kin barni da tsananin kewarki ,nasan bazan k’ara farinciki ba har zuwa sanda zan iskeki matata ……Allah yayi miki Rahama ,Allah ya jik’anki matata ,Allah yayi miki tagomashi da jannatul Firdausi …..” Haka yaita addu’a yana tsananin kuka na tashin hankali ,Yakuma Tayar da hankalin mutane gida ya rud’e da kuka ana tausaya masa, lallai sageer yayi rashin masoyiya ta hak’ik’a.

Bayan Baba yasa anfita dashi aka shigo da Hussaina, wadda tunda aka shigo da Ita gidan tana jingine a jikin Mamma batayiwa kowa magana ba ,sannan babu hawaye a fuskarta ko d’is ,azabar tashin hankalin da take ciki ya zarce nakowa ,kamar wadda tashiga d’imuwa haka ta kasance ,kowa idan ya kalleta sai yayi kuka saboda kowa yasan antafka mata mutuwa babba,yadda aka direta gaban Hassana haka aka d’auketa babu abinda ta iyayi sai kallon gawar Y’ar uwarta .

  Aka shigo da makara aka saka Hassana a ciki ,maza suka d'aga za'ayi waje da ita mata sukasa ihu ,Baba ya tsawatar yace adaina kuka addu'a za'ayi mata ,haka aka fita da Hassana daga gidan mahaifinta,????fitar da ta tafi kenan babu dawowa.

Babu Wanda ya lura da mik’ewar Hussaina kawai sai ganin fitarta akayi da mugun gudu tabi mazan da suka d’auki gawar Hassana ,tana fita ta iske dandazon maza a waje, gaba d’aya bata cikin hankalinta kanta ko d’ankwali babu ,babu da Wanda idonta yafara arba sai sageer dake rungume a kafad’ar Abdurrahman .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button