HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

A wannan lokacin Hamma sageer da Hussaina suka sami barci me nauyi a yanayin da suke ,haka barci ya kwashe Adda Nabeela da mummy Aisha ,wadda da k’yar suka lallab’a ya Abdurrahman yabi su Umma gida ,Dan so yayi ya kwana Baba ya hana.

Kowa yasamu barci amma banda Hassana da tsananin ciwon ciki ya addabeta ,amma tak’i tashinsu gudun karta katse musu baccinsu ,illah wasu hawaye masu tsananin k’una dake kwaranya a idanunta suna sauka a cinyar Hamma sageer.


Washe gari alhamis ma haka asibitin yakuma cika sosai da mutane ,duk Wanda yaji abinda yafaru sai yazo ya dubasu ,kuma a ranar ne matsanancin ciwon ciki yakuma addabar Hassana ,ko da akayiwa doctor bayani yazo ya dubata ,sai yayi kiran Baba office d’insa ya tabbatar masa da cewar Hassana tayi matuk’ar buguwa a cikinta Wanda dole zuwa gobe juma’a za’ayi mata aiki dan a magance matsalar ,sosai hankalin Baba yatashi amma bai fad’awa kowa ba illah Hamma sulaiman ,shima hankalinsa yatashi amma Baba ya kwantar masa da hankali yace babu komai za’ayi lafiya agama lafiya da ikon Allah mad’aukakin sarki me kowa me komai .

Da ciwon ya lafa mata da kanta tabada umarnin akaita toilet tayi alwala don bazata iya takawa ba ,Adda Nabeela da Aunty sakeena ne suka kaita ,har wanka sukayi mata suka sauya mata kaya acikin toilet d’in ,sannan ta d’aura alwala suka fito da ita, ta rama sallolin da suka tsere mata ,tadad’e tana addu’a mai yawa da yiwa Allah kirari sannan ta Shafa addu’arta .

Ya Abdurrahman kuwa shine yaketa hidima da Hussaina ,hatta abinci shine yake bata da magunguna ,Hamma sageer kuwa na lik’e da Hassana ,tana yawan kallonsa ta faki idanun mutane ta share hawaye a idanunta .

Da yamma ciwo yakuma ta’azzara ga Hassana ,har suma ta dingayi tana farfad’owa tsabar ciwon ciki ,hankalin kowa yatashi banda kuka babu abinda dangin keyi ,doctor yace kowa yabar d’akin zai dubata ,haka duk suka fice jiki a sanyaye ,Hussaina na jikin ya Abdurrahman yanata lallab’ata rungume a k’irjinsa ,Hamma sageer kuwa Babane ya rungumeshi da kansa a jikinsa ganin yarda jikinsa ke mugun rawa da karkarwa .

Doctor ya dad’e a d’akin sannan yafito yana yarfe gumi yace “wanene Abdurrahman ….!?kowa yabishi da kallo sai ya safwan ne ya nunashi yace ” gashinan doctor “doctor yace ” taso kazo Hassana nason magana da kai “a hankali ya mik’e Hussaina na jikinsa ya nufo doctor ,doctor d’in ya dakatar dashi yace ” tacemin kai kad’ai zakazo banda kowa ,Dan haka bawa wani Hussainar kazo “Hussaina tafasa kuka amma tilas haka safwan ya janyeta daga jikin Abdurrahman ,zuciyar kowa cike da tararrabin kiran me Hassana tayiwa Abdurrahman .

Tsawon lokaci Abdurrahman ya kwashe a d’akin shida Hassana ,ko me suka tattauna Allahu ya’alamu ,sai dai sunga Abdurrahman yafito yana tsananin kuka ko gabansa baya iya gani Dan zubar hawaye ,yana fitowa ya dubi Hamma sulaiman yace ” Kashiga kaida Baba zatayi magana daku “yana fad’in haka yafice yabar asibitin cikin tsananin kuka da tashin hankali .

Baba da Hamma sulaiman suka shiga inda suka tarar da Hassana a kwance ,Hassana tayi musu maganar da ta raunata zuciyar su ,duk dauriyar Baba saida ya zubda hawaye jin maganganunta ,hankalinsa yayi tsananin tashi amma tadinga kwantar masa da hankali ,a k’arshe tace ” Babana kar kayi kuka ,kar kabar Umma na tayi kuka ,kar kabar y’an uwana suyi kuka ,kar kabar kowa yayi kuka Babana ,idan suka fara kukan ka rarrashesu kacemusu kar su zubar min da hawayensu “takuma rik’e hannun Baban k’am tace ” Babana Hamma sageer da sisina akula da lamarinsu ,sannan acikamin burina don Allah “ta juya ta kalli Hamma sulaiman tace ” ko acikin y’an uwana kai na daban ne …ina sonka da gasken gaske Hamma sulaiman ,kai mutum ne nagari ,da Allah zai nunamin randa zan samu D’an kaina sunanka zansaka wallahil azeem “ta d’anyi shiru tana maida numfashi yayinda idanuwan Hamma sulaiman ke rufe yanajin duniya tayimasa tsananin zafi ,zuciyarsa k’una takeyi sosai amma hawaye yakasa zuba a idanunsa ko zaiji sanyi ,yana kallon yadda Baba ke hawaye yanaji a zuciyarsa inama shine yasamu wannan falalar.

Hassana ta buk’aci Hamma sulaiman yabata Biro da takarda zatayi rubutu ,da kansa yaje office d’in doctor yasamo ya kawo ,suka d’agata shida Baba suka jinginata da jikinsu ,ta yagi paper ta farko tayi rubutu me D’an yawa ajiki tanayi tana kuka hawaye na d’isa akan takardar ,bayan ta kammala ta ninke takuma yagar wata paper d’in takuma wani rubutun ta ninke ,ta kamo hannun Hamma sulaiman ta dank’a masa takardun tace ” wannan sak’on Hamma sageer ne da sisina ,aduk lokacin da kaga bana tare da su ka dank’a musu Hamma sulaiman “sai kuma ta lumshe idanu tace ” Babana kaci gaba da yimin addu’a kaida Umma ,addu’arku kawai nafi buk’ata a halin yanzu”

Daga haka batakuma magana ba ta runtse idanunta ,tanata ambaton Allah .

Zuwa dare ciwon ya tsagaita har akayi ta hira da ita ,hankalin kowa yafara kwanciya banda na Hamma sulaiman da Baba ,donsu maganganun data fad’amusu ya tada hankalinsu ,gashi tana yawan kallon Hussaina tace “sisina kiyi hak’uri ” ko kuma ta kalli Hamma sageer tace “Hamma sageer d’ina kayi hak’uri “

Ganin yadda jikin yayi sauk’i sai kowa yatafi gida cikin farinciki ,yayinda Hamma sulaiman yatafi cikin tararrabi da tsananin tsoro a zuciyarsa.


***Da asubahin ranar juma’a Hamma sulaiman yadawo daga masallaci sallar asuba ,sai yakasa komawa d’akin, ya zauna a falo kan kujera ya kifa kansa akan cinyarsa ,ya dad’e a haka Aunty sakeena batasan dawowarsa ba saida tafito falon zata Shiga ktcheen sannan ta Ganshi a haka,takowa tayi a hankali zuwa Inda yake , ta zauna a gefensa tace “Abban sadauki Ashe kadawo daga masallacin ..!?banji shigowar kaba ai ” taji shiru bai mata magana ba ,sai tasa hannayenta ta d’ago kansa tana kallon fuskarsa….hawaye tagani a fuskar ga idanuwansa da suka birkice gabad’aya,cikin tsananin rud’ewa tace “subhanallahi !Abban sadauki menene ya saka kuka haka …!?Hamma sulaiman yasa hannu a fuskarsa ya shafo hawayen ya kalla ,sannan yadubi sakeena cikin wata irin murya yace ” Ashe hawayen sunzo …!?tun shekaranjiya nake nemansu sunk’i zuwa sakeenan sulaiman …”wani mugun tausayinsa ya kamata ,ta jawoshi jikinta ta rungumeshi itama tana hawayen ,Hamma sulaiman yayi shiru a k’irjinta yana Jan ajiyar zuciya ,sai can Yakuma cewa”sakeenan sulaiman “tana Shafa bayansa ta amsa ,yace ” zuciya ta ciwo takemin, kuma inajin matsanancin tsoro “ta k’ara rungumeshi sosai tana hawaye tace” tsoran me kakeji Abban sadauki …!?Hamma sulaiman yakuma rufe idanuwansa k’irjinsa na matsanancin bugu har sakeena najin bugun acikin NATA k’irjin ,yace “inajin tsoran k’addarar da zata shigo ahalinmu ,inajin tsoran jarrabawar da zata sami dangin mu ,wata gagarumar k’addara tanason shigowa ta janye farincikin mu ” sakeena tace “k’addara ko jarrabawa daga ubangiji take ,kuma yadda da ita me kyau ko Mara Kyau tilas ne ,daman ba zaiyuwu kullum akasance cikin farincika ba ba tare da Allah ya jarraba bayinsa ba ,bawan da Allah keso shi yake jarraba ,idan yayi hak’uri yayi godiya ga Allah sai yasamu riba,kayi hak’uri ka k’arfafa zuciyarka ,kai namiji ne cikakke kuma Kaine Babba,idan mukaga kana hakan ni da sauran k’annanka ai saika karya mana zuciya” Hamma sulaiman yakuma manna kansa a k’irjin sakeena ,cikin k’aramar murya yace “nagode sakeenan sulaiman “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button