HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Comment
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page8⃣1⃣to8⃣2⃣

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

TUNASARWA????

ANYI HANI AKAN D’AN BIRNI YA SAYAR WA D’AN K’AUYE KAYA WATO DILLANCI TA HANYAR TARBA A WAJENSA DAGA WAJEN GARI ,KUMA ANYI HANI AKAN YAUDARA CIKIN CINIKI KUMA DA YIN CINIKI A KAN CINIKIN WANI

AIKI ME FALALA????

FAD’IMATU Y’AR MANZON ALLAH (S A W ) TA TAMBAYI ANNABI CEWA TANA BUK’ATAR WADDA ZA TA RINGA YI MATA HIDIMA ,SAI ANNABI (S A W ) YACE MATA TARE DA MIJINTA ALIYU ALLAH YAK’ARA MUSU YARDA “BA NA SANAR DAKU ABINDA YAFI ALKAIRI DAGA ABINDA KUKA ROK’ENI BA ,IDAN KUKA TAWO WURIN KWANCIYARKU SAI KUYI KABBARA SAU TALATIN DA HUD’U ,KUMA KUYI TASBIHI SAU TALATIN DA UKU ,KUMA KU GODEWA ALLAH SAU TALATIN DA UKU (ALHAMDULILLAH)TO WANNAN SHINE MAFI ALKAIRI AGARRKU DAGA MAI HIDIMA
GA YADDA SIGAR TAKE????

1, SUBHANALLAH 33
2, WALHAMDULILLAH 33
3, WALLAHU AKBAR 33

SADAUKARWA GA

FEJIN K’ARSHE SADAUKARWA NE GA MAHAIFIYATA BANGONA MAJINGINATA INUWATA,TARE DA MIJINA ABIN K’AUNA TA MASOYINA ME SHAREMIN KUKANA,DA KUMA YARANA Y’AY’AN ALBARKA????????????

????????????????????????????????

INAI MUKU BARKA DA WANNAN RANA TA JUMA’A ,ALLAH YABAMU ALBARKACIN WANNAN RANA????????????

Har su Ya Abdurrahman suka isa gidansu da ke unguwar (oji quarters) Hussaina bata dena kuka ba ,yayi matuk’ar k’ok’ari wajen k’in kulata duk da kukanta na damunsa sosai ,da kansa yabud’e get d’in yadawo yashiga da motar cikin harabar gidan ,Yakuma fitowa ya kulle get d’in yana kallon yadda hasken fitilu ya haskake wajen ,zuciyarsa na cikin tsananin farincikin wai yau shine a gidansa na kansa tare da masoyiyar da babu kamarta a fad’in zuciyarsa.

Ya koma wajen motar yabud’e mata k’ofar ,sannan yad’an d’aure fuska kad’an idanunsa kan fuskarta yace “fito ….” Tana shasshek’an kuka ta kalleshi fuskarta har tafara kumbura tayi jajir, ya D’an d’auke kallonsa daga gareta saboda yaji tsigar jikinsa na mik’ewa ,ganin tak’i fitowa yakuma yin magana da D’an k’arfi fuskarsa babu walwala yace “in kika bari na k’irga uku baki fitoba ranki zai b’aci …” Tsoro ya kamata ganin yadda ya tamke fuska sosai babu walwala ,da k’yar ta karkata tafito yad’an matsa ta wuce Sai kuka takeyi ,yabita da kallo yana kulle motar sannan yazo dab da ita Yakama hannunta yajata cikin gidan ba tare da yayi magana ba ,ita kam tamkar wadda za’a yankata saboda gurshek’en kukan da takeyi,zahiri kukan ta na tab’a ruhinsa kannewa kurum yakeyi .

A k’ayataccen falonsu yayi mata masauki akan kujera ,shikam bedroom d’insu yashige bai tsaya daka ta tata ba ,yafi minti 20 bai fitoba hakan yasa ta zame daga kan kujeran zuwa carpet d’in tayi male male tanajin kanta tamkar yarabe biyu saboda ciwo amma tak’i dena kukan ,a haka yafito ya sameta yad’an tsaya Jim yana kallonta tamkar ya k’arasa ya rungumeta ya rarrasheta sai zuciyarsa ta hanashi hakan ,yasan halinta da yawan rigima gara yad’an horata kad’an Dan tasan ba koyaushe ake kwana a gado ba ,

Sai ya kad’a kansa yafad’a ktcheen ,kamar yadda Adda Nabeela ta Sanar dashi hakan yagani ,tuni ta tanada musu kayan ciye ciye da shaye shaye masu armashi da dad’i, ya had’o komai a babban tire ya d’auko ya fito dasu zuwa gabanta .

Idanuwanta a rufe amma hawaye basu bar zubaba ,yana ajiyewa yasa hannu ya d’agota zaune amma bai d’orata a jikinsa ba ,saida ya zaunarda ita sosai shima ya zauna yafara had’a mata abinda yake ganin zatafi ci ,bai yarda ya kalleta ba saboda yasan muddin yana kallonta zaiji tausayinta yakasa gudanarda komai ,

Ya d’iba yanufi bakinta dashi sai ta girgiza kai takuma fashewa da kuka ,ya dafe kansa yana fad’in “kai subhanallah !na rantse zan mareki fa !karb’i ko na mareki yanzun nan …” K’irjinta na bugawa saboda tsorata tayi maza tabud’e bakin yafara bata ,da sauri Sauri ya ke cusa mata duk yabi ya harhad’e fuskarsa, tanata hawaye take karb’a tanaji tamkar tayi amai ,saida yaga tabbas ta k’oshin sannan yarabu da ita ya janye ragowar yafara ci ba tare da ya dubeta ba ,yana satar kallonta lokacin har tafara gyangyad’i ,amma da yake rigimar na cinta da tafara gyangyd’in sai tayi firgigit ta farka tacigaba da kukanta ,shi abin ma dariya yabashi amma ya gintse ….har ya kammala ci yatake cikinsa tsaf saboda yasamu k’arin k’arfin gudanarda sharafinsa a ranar ,sai da ya kammala sannan ya maida komai ktcheen ya ajiye .

Jin ankuma yin sama da ita yasata bud’e idanu daga gyangyad’in da tafara ,tabud’e baki zata kurma ihu sai idanunta yafad’a cikin nasa, yawani wulk’ita idanu bai yadda ba waishi hararanta yayi ,sai takoma tayi lamo a jikinsa zuciyarsa na rawa da tsinkewa ,tana jikinsa har cikin toilet d’in bedroom d’insu sannan ya direta ,da kansa yasa makilin ajikin brush ya mik’amata yace “wanke bakinki ….” Hannunta na rawa ta karb’a Dan ita yau d’in tsoran Ya Abdurrahman d’in takeyi gabad’aya ya sauya mata,

Yana tsaye jingine da bango yana kallonta har ta wanke ,sannan yace tayi walwala ,batayi musuba tafara alwalan jikinta na rawa tamkar mejin zanyi ,idanunsa na kansa yana kallon yadda hawayen idanunta ya had’e da ruwan alwalan fuskarta ,

Tana kammalawa ya nuna mata hanyar fita da sanyin murya yace “jeki kirani INA zuwa …” A hankali ta taka tabar toilet d’in kanta a sunkuye yabita da kallo yana girgiza kansa .

      Saida yak'ara wanka sannan ya d'aura tasa alwalar yafito,tana mak'ure zaune a bakin gado kanta akan cinyarta bata d'agoba ,yasamu damar saka kayan baccinsa masu D'an kauri da rashin bayyana jiki ,jikinsa kuwa yashafa kalolin turaruka har sai karasa k'amshin da yakeyi ,ya d'auko mata hijab d'inta a wardrobe yazo har Inda take ya d'agota ya sanya mata sannan ya mik'ar da ita tsaye yajata har kan sallayar da ya shimfid'a,tunda taga haka tagane yanaso suyi sallah tare ne ,

Sunyi sallah raka’a biyu me cikeda nutsuwa ,bayan sun idar yayi musu addu’o’i masu yawa na Neman zaman lafiya da samun zuri’a d’ayyiba ,
Yana juyowa gareta yaga still har lokacin hawaye nafita a idanuwanta ,sosai yaji a zuciyarsa yagaji da ganin hawayenta ,hannu yasa ya fizge hijabin jikinta yana dank’o wuyan rigarta yajawota gabansa ,ya runtse idanunsa da wata iriyar murya me rawa yake girgizata yana fad’in”nagaji ,nagaji da kukan nan wallahi ,menene …!?me kikeso …!?

Takuma fashewa da kuka har muryarta na dashewa ,sai yabud’e idanunsa yak’ura matasu ,tare da jawota jikinsa ya rungumeta k’aunarta naratsa jinin jikinsa ,a hankali ya kife fuskarsa akan tata yana shak’an numfashin da take saukewa ,ya lumshe ido yace “tawan! Don Allah kiyi shiru kifad’amin menene yake damunki …!?na rantse zakisa zuciya ta ta tarwatse da wannan kukan naki…..” Da k’yar take fizgo numfashi jin hannayensa na yawo a jikinta ,takuma fashewa da kuka mutyarta bata fita sosai tace”Hassanatah !Ya Abdurrahman karka bari a tafi da Hassanatah ….kaji abinda Hamma Sulaiman yace ko …!?yasa bakinsa yana wasa da tsinin hancinta yana D’an tsotsa yace “Hamma Sulaiman wasa yake muku babu inda Hassana zataje ,yayi hakan ne Dan kusaki junafa …!

Ta yunk’ura tana afkawa k’irjinsa ta rungumeshi tsananin murna ta baibayeta ,cakumar da tayi masa saida numfashinsa yakusa d’aukewa Dan dad’i ,fad’i takeyi ” wayyo naji dad’in maganarka Yayana,inason HASSANA ta banason rabuwa da ita”rik’eta k’ak’am yayi ajikinsa yana karkarwa da fad’in “nikuma ke nakeso tawan…. Nidai nafad’a miki ina sonki ” Hussaina babu bakin magana saboda yadda Ya Abdurrahman yafara gigita duniyarta ,akan carpet d’in d’akin yafara tumurmusar matarsa yarabata da komai na jikinta ,biji biji yayi da ita yana karad’eta da soyayyarsa me gard’i ,sosai Hussaina tafara raina kanta jin Abdurrahman zai cinyeta d’anyarta ,saida yagama gigita ta ya tsotseta tas kafin shima yazare komai na jikinsa ,d’aukanta yayi cak ya maida ita kan bed d’insu na alfarma yabita ya danneta yana suburbud’arta da soyayya ,tun tanajin dad’in soyayyar da yake Nuna mata har tafarajin tsananin zafi da rad’ad’i ajikinta a sanda Ya Abdurrahman yake karanta addu’ar saduwa yana tura kansa cikin jikinta cikin kuka da surutai na fad’ar kalaman soyayya,
Ranar Hussaina ta raina kanta ,taji inama ba’a halliceta ba balle har tayi aure taga wannan azabar,sumanta biyu saboda wahala amma Ya Abdurrahman bai saurara mataba bayama cikin hankalinsa yatafi duniyar Maji dad’i ….har zuwa sanda yasamu nasarar biyan buk’atarsa gabad’aya ya maida Hussaina cikakkiyar matarsa…….!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button