HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

SANNAN LABARIN NE DAKE TAFE DA TARIN SAKONNI MASU MATUKAR MAHIMMANCI GA ALU’MMA GABAD’AYA,LABARIN MUWADDAT LABARI NE MAI MATUKAR D’AGA HANKALI FIRGITARWA TSOROTARWA ,TATTARE DA TAKAICI DA BAKINCIKIN, TARE DA FADAKAR DA WASU IYAYE MASU AIKATA ABUBUWAN DA BAI KAMATA BA AGABAN YARANSU MASU K’ARANCIN SHEKARU, SANNAN DA D’AUKA BURI MARA MARAMA’ANA AKAN YARANSU , WANDA DAGA KARSHE HAKAN ZAI HAIFAR MUSU DA DAMUWA TSANTAR NADAMA DANASANI TARE DA ALLAH WADAI DA IRIN D’ABI’UNSU ,SHIYASA LOKACIN DA LABARIN YAZO MIN NA HANGA NA HANGO NAGA BAI KAMATA NA BARWA ZUCIYATA NI KADAI BA, SAKAMAKON MATSALAR DAKE TATTARE DA LABARIN ,WANDA MAFI AKASARI ABINDA LABARIN KE TATTARE DASHI YANA FARUWA ACIKIN RAYUWARTAMU NA YAU DA KULLUN WANNAN DALILI YASA NAGA YAKAMATA NA ISAWAR ALU’MMA ,DOMIN MUGU TARE MU TSIRA TARE DAN MU INGANTA RAYUWAR YARANMU TA HANYAR DATA DACE, DA KU’BUTAR DASU DAGA HALAKAR RAYUWA ,BUGU DA KARI LABARIN MUWADDAT DAUKE YAKE DA TSANTSAR SOYAYYA MAI NISHADTARWA DA TSAYAWA ARAI .

DOMIN BUKATAR KARANTA LABARIN MUWADDAT, ZAKI BIYA 300 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN AISHAT ABDULLAHI 2175076611 ZENITH BANK, SAI A TURAWA WANNAN NUMBER ????????08032384602 ALERT DOMIN *TABBATARWA,KAR AMANTA BA’A KIRAN NUMBER TABBATARWA SANNAN BA’A TURA VTU TA NUMBER, KAWAI ITA NUMBER AN TANADAITA NE DAN TABBATARWA GA MASU TURO KUDI TA BANK NE,GA MASU BUKATAR TURO KATI ZASU TURAWA WANNAN NUMBER 08059623096 KATIN MTN KO GLO INA MARABA DA MASOYANA ABUN ALFAHARINA ..

    Da k'yar mamma ta dakata da kukan da takeyi tana kallon Hassana da hawaye ke zuba a idanunta ....sannan ta rik'o hannun Hassanar ta matse a cikin nata hannun tacigaba da bata labarin kamar haka......

“Wannan rana itace mafi munin ranaku a gurina …Dan daga itane nake fama da wani irin son mustafa da Allah ya jarrabeni dashi tamkar na zauce…… Nayi kuka Mara misaltuwa ….nayi Dana Sani Mara amfani alokacin da komai ya k’uremin …..dalilin abinda yafaru nakamu da hawanjini Hassana ….duniya taimin zafi banajin dad’inta ko kad’an komai ya tab’arb’aremin ….banida aiki sai kuka da nadamar abinda na aikata da nasan mutuwa mustafa zaiyi ya barni da ban aikata abinda nayi ba……a gefe guda ga matsanancin halin da sageer ya shiga ….sageer yadena walwala ko abinci bayaci …bayason yaga na kusanci inda yake ko kad’an ….ya rame ya fita daga hayyacinsa …tsoran mata yake sosai da tsanar su a ransa ,illah yayarsa Nafeesa da ya tabbatar halinta me kyau ne …..A wannan lokacin sageer ko school dena zuwa yayi gaba d’aya kullum abokansa na k’ok’arin rarrashinsa Dan yakoma school amma abin ya gagara ….nikuwa har tsoran tunkarar sageer nakeyi saboda banason naga kallon tsanar da yake bina dashi …..har zuwa yanzu kuma babu Wanda sageer ya fad’awa ainihin abinda yasa zuciyar mahaifinsa ta buga …illah Nafeesa da ya fad’awa itama Dan yana ganin yadace ta sanine….

Kwata kwata sai sageer ya k’auracewa gida …baya zaman gidan ko Dan kar ya ganni ….a cewar sa kallona yanasa ya tuna abinda yafaru …idan ya kalli fuskata yana tuna randa nakewa daddynsa hargowar ya sakeni Wanda shine yazama ajalinsa .

 D'akin abokinsa yakoma da zama me suna faruk ....faruk abokin sageer ne sosai tare sukayi secondary school har zuwa jami'a ....faruk yanada halaye nagari sosai ,sai dai yana shaye shaye a b'oye ba tare da wasu mutane sun saniba ...amma sageer yasani kuma shine ma yake masa nasiha kullum akan yadena, babu kyau ...kullum faruk yakan ce "sageer katayani addu'a insha Allah nakusa dainawa ....idan ina cikin damuwa idan ban shaba banajin dad'ine "  Komawar sageer d'akin faruk da zama shine musababbin fara shaye shayen sageer ...mahaifin faruk babban d'an shiyasa ne, shiyasa faruk yake abinda yakeso ma ,saboda akwai kud'ad'e a hannunsa ...kuma iyayensa basu damu da lura da halinda yake cikiba ,shiyasa ma basu cika shiga b'angarensa har su iske shaye shayen da yake ba .

“Wata rana sageer kwance akan kujerar falon faruk yayi rigingine ya rufe fuskarsa da hannayensa ,tunani ne fal a ransa da kuma matsananciyar damuwa …yakasa cire komai a ransa …gashi dai yaci gaba da zuwa school amma baya fuskantar komai a karatun …yana wannan yanayin faruk yafito daga d’aki hannunsa rik’e da taba yana zuk’a yana fesarwa ….yazo ya janye k’afafun sageer ya zauna a kusa dashi sai ya d’ora k’afafun sageer d’in akan cinyar sa …warin tabar ne yasa sageer mik’ewa zaune yana yatsuna fuska da kautar da kai …murmushi faruk yayi ya dafa kafad’ar sageer yace “Abokina tun bayan rasuwar daddy kak’i ka saki jikinka ka koma normal …me yasa hakane ….!?sageer ya d’an juyo ya lumshe idanu yana fesar da numfashi cikin miskilar murya yace ” faruk damuwa tayi min yawa …..banajin dad’in rayuwata ….don Allah faruk idan kasan maganin da zai ciremin damuwar zuciya ta kayi hanzarin taimakona kabani ….k’irjina da zuciya ta sunayi min zafi a koda yaushe faruk…..narasa ya zanyi ….”

Yana kammala magana faruk yayi wani murmushin gefen baki yace “nikuwa nake da maganin damuwa sageer .. Shi nake sha shiyasa kullum kake ganina fresh babu damuwar komai a raina ….na…..!kan ya k’arasa sageer ya rik’e kafad’un faruk ya katseshi da cewa ” bani nima nasha…. Na rantse inaso zansha faruk ….kabani ko damuwata zata yaye “yana rufe baki faruk na manna masa tabar hannunsa akan bakinsa yana fad’in” ga maganin damuwa sageer …idan kasha ta zakaji sauk’in damuwar zuciyarka “a salub’e sageer ya kawar da kansa yana goge bakinsa inda sigarin ta tab’a yanayiwa faruk wani kallo yace ” sigarin ce maganin damuwa …!?ta ina zata zama magani ….ai sai dai tak’arawa mutum ciwo da damuwa…..!

Da hanzari faruk yaci laya yana rantsuwa.

"Wallahi magani ce.... Maganin damuwa ce ....idan har kasha bakaji dad'in zuciyarka da k'wak'walwar ka ba karka kuma yarda dani Abokina ....sha kaji ..d'an zuk'i kad'an kaji ..."sageer na kallon faruk zuciyarsa na kai komo ...wani b'arin nacewa "karka sha sageer "...wani b'arin nacewa ..."sageer kasha ...ka gwada k'ila kasami sauk'in damuwar ....runtse idanuwansa yayi kansa yayi masa nauyi ,ba tare da tunanin mezai faru ba sageer ya karb'i sigarin hannun faruk yasa a bakinsa ido a lumshe yayi mata kyakkyawar zuk'a ....garin fesar da hayak'in sai numfashinsa ya sark'e, yashiga tari ba k'ak'k'autawa .....idanunsa sukayi jajir yayinda faruk ke d'an bubbuga bayansa da shafawa yana cewa"rashin sabo ne yasaka k'warewa sageer ...a hankali zaka saba ...d'an kuma zuk'a kagani ..."sageer yana girgiza kansa alamar bayaso amma da magiya da hilata da dad'in baki saida faruk ya koyawa sageer shan sigari a wannan ranar ....bayan ya shanye faruk ya d'auko wani kayan maye a wata kwalba me kama da ta magani ya tilasta sageer saida ya shanye abin cikinta tsaf ....minti biyu tsakani sageer yafara ganin hurhud'u gari najuya masa ,kansa ya d'au caji ,yana layi yafad'a kafad'ar faruk bacci ya kwasheshi ....faruk yayi murmushi sannan yacireshi a jikinsa ya gyara masa kwanciya....saida sageer yayi baccin awa biyar cif sannan ya farka ...yana farkawa sai yajishi garau babu damuwa a ransa ...sakayau yakejin zuciyarsa ...kansa yayi sawai babu nauyin da yakeji ....sosai yaji dad'i yana ganin ai faruk ya taimakeshi ne ...bai San cewa illah faruk yayi masa ba ....tun daga ranar sageer yazama bashida aiki sai shan sigari ,da sauran abubuwan sa maye ...daga Zarar yaji damuwa a zuciyar sa ...to fa saiyasha hankalinsa zai kwanta .Nasha zuwa gidansu faruk na tarar da sageer a wannan yanayin ....nayi kuka Mara misali ganin na lalata rayuwar sageer da kaina ...nasan nice silar jefa sageer wannan halin ....gashi sageer baya saurarona nayi ban hak'urin iya yina yak'i fuskanta ta ...Alokacin Nafeesa tayimin waya cewar zasu dawo k'asar nan ...Dan suna can k'asar waje mahaifinta ya rasu ...sai waya akayi mata ....batun dawowarta yasa naji dad'i a raina ina ganin ko babu komai ita zata temakamin gurin shawo kan sageer .


 Randa suka dawo a ranar na raka Nafeesa gidan su faruk taga halinda sageer yake ciki .....yana ganinmu da gudunsa ya rungume Nafeesa yana kuka ....Nafeesa ma ta fashe da kuka suna tuna daddynsu da kewar rashinsa ....ba k'aramin mamaki Nafeesa tayi ba ganin sageer ko kallon Inda nake baiyi ba ....da nayi masa magana ma k'in kulani yayi ....nan Nafeesa tayita yimasa fad'a akan meyasa yasaka kansa a wannan hali na shaye shaye kuma meyasa yake wulak'antani a matsayina na mahaifiyarsa .....anan yaja hannun Nafeesa suka shige can cikin d'akin faruk suka barni a falo, daman faruk d'in bayanan .Ban San me sageer ya fad'amata ba ,k'ila dai ya sanarda ita dukkan abinda yafaru ne ....kawai dai naga tafito fuskarta da hawaye tanai min wani irin kallo me firgitarwa ...hannunta rik'e da na sageer da kayansa a trolley tana ja ....sukai min wani irin kallo suka yi tafiyarsu suka barni a gun .

Na kuma Shiga wani tashin hankalin, yarana duka sunyi fushi dani sun juyamin baya ….dalilin hakan yasa na kwanta rashin lafiyar da nakusa mutuwa nabi mustafa nima ,jin labarin hakan yasa Nafeesa tazo gareni …kunsan zuciyar mace da rauni …a wannan lokacin nadinga kuka ina Neman afuwar Nafeesa …Nafeesa tafad’amin maganganu akan abinda nayi bai daceba ….tayi kuka sosai akan hakan da addu’ar samun Rahama ga mahaifinta…daga baya kuma ta yafemin ,tace nima inta istigfari ko Allah zai dubeni ya gafarta min laifukana ….tundra Allah sami’uddu’ai ne ….”

A lokacin komai nawa ya tsaya cak na harkar kasuwancin…dukiyar kanta lalacewa tasoma yi …asara iri iri haka na dingayi ….kullum ina addu’a da rok’on Allah akan ya yafemin laifukana ….nayi abubuwa da yawa na sadak’atul jariya zuwaga mustafa ,Dan ladan ya iskeshi har k’abarinsa ….haka nan nasha mafarki da mustafa yana shaidamin ya yafemin duk abinda nayi masa…yanayi min murmushin da yasaba yimin…ta nan nakejin sauk’i …hakanan nake adduar Allah yasa mafarkin yazamemin gaskiya ,naje lahira na tarar da mustafa a matsayin me yafiya a gareni….”

  Nafeesa na iya k'ok'arinta na ganin ta shawomin kan sageer da Yakoma gidanta da zama ,amma abin yaci tura ...kuma tana bakin k'ok'arinta na ganin sageer yadena shaye shaye ...amma duk bata samu nasara ba itama ..... 

Mamma ta numfasa tace”

“My daughter wannan shine tak’aitaccen labarinmu … ..!”

 Sannan takuma share hawayenta ,ta dubi Hassana da idanunta sukayi jajir tace "HASSANA kinji tarihinmu da abinda ya k'unsa .....taimakonki nake nema my daughter ....Dan Allah kitaimaka min na ganin an samu maslaha ....so nake sageer yafita daga 

Wannan halin ….. Nasan kema zakiga bak’ina k’o ….!?toh amma sai dai k’addara tariga data…” Please kiyimin magana Hassana …shin zaki iya taimako na ……!?

    Hassana ta k'urawa mamma idanu da kallon fitar hayyaci a hankali ta bud'e bakinta da yayi mata nauyi tace" BAZAN IYA BA MAMMA ......!

comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

TYPING????

???????? HASSANA ????????

       *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page 1⃣9⃣to2⃣0⃣

WATTPAD:hassana3329

GODOYA ME TARIN YAWA ZUWA GAREKU????

NAGODE DA ADDU’AR KU MASOYA NA ,YAWAN ADDU’AR KU DA FATAN ALKAIRI HAR HAWAYEN MURNA YA SAKANI ,INAJI DAKU A RAINA DA WANDA NASANI DA WANDA BAN SANIBA ,ALLAH YACIGABA DA DAFA MANA AKAN AL’AMURAN MU NA KO YAUSHE

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W ) YACE “LALLAI NAGA WANI MUTUM YANA JUJJUYAWA (WATO YANA KAIWA DA KAWOWA)A CIKIN GIDAN ALJANNA ,SABODA WATA ITACIYA DA YA D’AUKE TA DAGA KAN HANYA ,WACCE TA KASANCE TANA CUTAR DA MUTANE

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W ) YACE” MALA’IKU SUNA YIN SALATI GA D’AYANKU ,MATUK’AR YANA WURIN DA YAYI SALLAH ,KUMA MATUK’AR BAIYI HADASI BA (WATO BAI KARYA ALWALARSA BA ,SUNA CEWA “YA UBANGIJI KA GAFARTA MASA ,YA UBANGIJI KAYI MASA RAHAMA

      Ba mamma ba hatta Aunty Nafeesa saida ta razana jin maganar Hassana ...gabad'aya suka zuba mata idanu jikinsu na rawa ....Aunty Nafeesa ce tayi k'ok'arin matsowa ta dafa kafad'ar Hassana a hankali tace" yanzu bazaki iya taimakon mu ba Hassana ...bazaki share mana hawayen mu ba ...!?a hankali Hassanar ta d'ago da kanta ta kalli mamma da gabad'ayan ta takoma kalar tausayi ...sannan ta juya ta dubi Aunty Nafeesa da ke faman kallonta tace "ba nufina bazan taimaki mamma ba ....ah ah ...ina nufin bazan iya barin Hamma sageer cikin wannan halin ba ....zanyi k'ok'ari da jajircewa da addu'a Dan ganin yafita daga wannan halin .....labarin yak'ara tabbatar min da ingancin Hamma sageer ....kuma insha Allahu zan kasance sila wajen juyo da akalar Hamma sageer da taimakon rabbil izzati Aunty Nafeesa ...." Sannan tajuyo ta dubi mamma da furucin Hassana yasata shauk'i a ruhinta ta yadda fuskarta ta kasa b'oye murnar ta ...sosai Hassana ta duk'ar da kanta ta na wasa da yatsun k'afarta sannan ta bud'e baki a hankali tafara magana "Mamma naji labarinku me cike da abubuwa iri iri ....labarinku yana d'auke da darasi da tsoratarwa da tausayi da kuma raunata zuciya ....na rantse banta b'a cin karo da labari me kama da shiba ....a sanda kike bani labarin tamkar almara nake jinsa ....bantab'a tunanin zaki iya aikata hakaba ...Ashe dai mutanen cikin duniyar halayensu mabambanta ne .....!?Ashe da gaske akwai mata masu wulak'anta mazajen auren su .....!?Dole ne sageer ya tsani mata ya dinga kallon mu a bai bai ....Mamma kinyi kuskure ba k'arami ba ....sai dai baki makara gurin tuba ba idan har ya kasance taubatan nasuha zakiyi .... Manzon Allah (S A W ) yace " kowane d'an Adam yana kuskure ,amma mafi alkairin masu kuskure sune masu tuba "    Idan mukayi duba da wannan hadisin zamuga Allah yana sonki da Rahama mamma shiyasa har yasa kika gane kuskurenki kika tuba kike Neman gafara a gurin Allah ......amma fa kisani Mamma Allah baya yafe laifin bawa akan bawa ,matuk'ar ba bawan ne ya yafe laifin ba ...duk da ina kyautata zaton daddy ya yafemiki kodan mafarkin da kikeyi dashi ....shawara ta agareki mamma itace kidage da yiwa daddy sadaka da addu'ar samun rahama.... Ki kuma k'ara kyautata tubanki ta hanyar istigfari da salatin Annabi da ambaton Allah a ko yaushe .....Batun Hamma sageer kuma kibar komai a hannuna .....amma dai ina buk'atar addu'ar Ku wadda zata zamemin jagora gurin tunkarar sa ....."

Mamma da hawayen ta ta sakko k’asa ta rungume Hassana …godiya kuwa saida Hassana tasa hannu ta rufe bakin mamma sannan mamma d’in tayi shiru ….Aunty Nafeesa ma kallon Hassana takeyi da wata irin k’auna …da hawayen ta ta furtawa Hassana cewa “Na rantse kinada kirki da mutunci Hassana …ilimin ki da halayenki sun dace dake ….godiyar mu GAREKI bazata yanke ba ….mungode Hassana “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button