HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kamar daga sama sukaji sallama ….suka d’ago da Kansu suna amsawa a tare…Gaban Hassana ne yayi matuk’ar fad’uwa ganin mamma da Nafeesa cikin tsakar gidansu suna doka musu murmushi…..har alokacin da suke zaune suna wanke wanken bata yardarwa zuciyarta cewa mamma zatazo gidansu ba ….tayi zaton mamma d’in tafad’ane kawai …..sai gashi tayi mata bazata .

  Hussaina kam wani sandarewa tayi bakinta a bud'e tana duban su mamma da tsananin mamaki ....hakanan takewa Rabin ranta duban tuhuma ......da son Sanin menene yakawo wad'annan mutanen cikin gidansu...........!?"

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

TYPING????

???????? HASSANA ????????

              *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page 1⃣5⃣to 1⃣6⃣

WATTPAD:hassana3329

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W )YACE “NA HANEKU DA YIN HASSADA ,SABODA HASSADA TANA CINYE AYYUKAN K’WARAI ,KAMAR YADDA WUTA KE CIN ICE KO KUMA CIYAWA

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W ) YACE “DUK WANDA YAYI MIN SALATI SAU D’AYA ,ALLAH ZAIYI MASA GUDA GOMA ,KUMA ZA’A GOGE MASA KURA KURAI GOMA ,KUMA ZA’A D’AGA DARAJARSA SAI GOMA,A WATA RUWAYAR MA ZA’A RUBUTA MASA LADA GOMA

Ganin irin kallon da y’an biyun ke musu yasa mamma bud’e baki tana murmushi tace “mamakin ganin mu ne yasa kuka kasa magana sai kallo da ido ….!?habawa ai sai kunya takama Hassana …ta janye idanunta da fad’in” mamma sannunku da zuwa ….Aunty Nafeesa barka da zuwa Ku shigo mana ….”tsam ta tsame hannunta daga kumfar wanke wanken ta mik’e domin yi musu iso d’akin Umma .

    Ganin zasu shige yasa Hussaina ta gaishesu ...suka amsa mamma nacewa "sannu da aiki Hussaina" sannan sukabi Hassana da ta tsaya tayi sallama k'ofar d'akin Umma da fad'in "Umma munyi bak'i nefa" Umma tace "bak'i kuma....? Toh sannunsu da zuwa ....kai usmanu d'auki kwanan zogalen nan ka kai min kitchen ka Adana ....Hassana kice su shigo "inji Umma da ke k'ok'arin gyara zamanta .



    Hassana ta juya tana cewa " Ku shigo mamma "mamma tace " to madallah "sannan suka shiga d'akin Umma da sallamar su .....Umma ta mik'e tanayi musu maraba lale ,sosai Umma ta tarbesu duk da batasan mamma ba amma tasan Aunty Nafeesa ....kuma ganin Nafeesa tare da mamma ta tabbatar akwai wata alak'a tsakaninsu ko Dan kamar da taga sunayi .



  Bayan sun zauna suka gaisa da Umma ,Hassana ma ta gaishesu tare da zuwa takawo musu ruwa .....basajin k'ishirwa amma Dan kar aga kamar sun raina sai suka sha ruwan tare da godiya .....Hassana tashi tayi tafita domin cigaba da Aikin da sukeyi ....Usman kuma yazo ya gaidasu mamma yanata yimata murmushi alamar ya ganesu ....mamma harda kawo masa tsarabar chocolate da biscuit masu dad'i ....usaman yak'i karb'a yana kallon Umma yana sunkuyar da kai yace" ah ah kibarshi "mamma tace " haba yaro me wayo ka karb'a mana ainima mamanka ce ko...!?saida Umma tasa baki sannan Usman ya karb'a yace "angode Allah yasaka da alkairi"

Bayan Usman ya fita daga d’akin ne Aunty Nafeesa ta gyara zamanta tadubi Umma tace “Umma wannan mahaifiyata ce….ta haifemu mu biyu nida k’anina sageer …to maganar gaskiya akwai wata matsala da ta shiga tsakaninta da sageer d’in wadda tazame mata k’alubale …kullum cikin Neman hanyar gyara lamarin muke Allah baisa andace ba ….sai yanzu ne muke ganin kamar maganin matsalar tazo …..Umma bawani abune maganin matsalar ba face Hassana …..itace muke ganin zata taimaka mana ta shawo mana kan matsalar nan …..shine mukazo gareki Umma Dan Neman taimakonki akan mamma zata tattauna wasu maganganu da Hassana d’in ….ta hakane kawai muke ganin za’a samu maslaha insha Allah “

    Umma tacika da mamaki a zuciyarta sai dai bata bayyana a fuskarta ba ....mamakinta bai wuce a ina sukayiwa Hassana sanin da har suke mata kallon maganin matsalarsu ....!? Ita kanta Naffesar bawani sabo sukayi da itaba dalilin su ba masu cusa kai bane ....balle mahaifiyarta da yau kad'ai ta tab'a ganin kalarta ma .....Umma tanada tabbacin yaranta basuda shige shige da cusa Kansu a gun mutane ....to amma ya akayi aka haihu a ragaya ..... !?

Ta barwa ranta tambayoyi da dama….. Sannan tayi murmushi tadube su tace “Allah ubangiji yasa k’arshen matsalar ne yazo ….babu damuwa Nafeesa ai Hassana kamar k’anwarki ce ….yaushe kuke son magana da ita ….!?inji Umma kenan da zuciyarta ke San sanin me za’a tattauna ne …..amma tasan tambayar hakan ba huruminta bane ….bai kamata tayi katsalandan ba “

Aunty Nafeesa tadubi mamma tana murmushi ,sannan ta juya ta dubi Umma da fara’a a fuskarta tace “Ai Umma ko yanzu kika bamu damar zamuji dad’i…. Mamma ta damu da son maganar da Hassana tunda ta hangi taimakon da take ganin Hassanar zatayi …..Umma idan babu takura don Allah mamma zatayi magana da Hassana yanzu ….kuma anan gidan koda na awa d’aya ne Umma “

Sai Umma taji abin ya kwanta mata a ranta musamman da akace tattaunawar a gidan za’ayi …..a yadda kuma taga fuskar mamma d’in cikin damuwa ta tabbatar abinda ke ranta na damunta sosai …..tasan kuma duk Wanda ya taimaki wani Allah zai taimakeshi ne duk da batasan akan me Hassana zata taimaka musu ba ……”Umma tace “babu komai Nafeesa…bari na turo muku ita …Allah yasa a dace ” sai a lokacin mamma tasaki wata ajiyar zuciya me k’arfi ,fuskarta ta bayyanar da fara’a sosai ,ta dubi Umma da ke k’ok’arin mik’ewa Dan ta turo Hassana tace “banida bakin godiya a gareki Maman twins …..baki sanniba amma gashi kin bani dama a cikin gidanki ….lallai yau nashigo gidan karamci da tarbiyya …..na tabbatar su Hassana gadon karamcin sukayi ….hakan yakuma tabbatar min Hassana ta dace da abinda zuciya ta take nunamin a kanta …..nagode Maman twins ….Allah yasaka da alkairi ya k’ara girma …..” Da murmushi Umma ta amsa da cewa “Ameen ya Allah ….ai babu komai yiwa Kaine ” sannan tasa kai tafito daga d’akin ….tabar mamma da ta juya ta dubi Nafeesa tana fad’in “munzo gidan karamci ….Nafeesa gidan nan gidan mutunci ne …..Allah yacika min burina na samun iri daga gidan .

A can tsakar gida tun bayan fitowar Hassana ,sisinta ta tsareta da kallon tuhuma ….hure idanun Hassana tayi tana dariya a hankali kuma tace ” wannan kallon na menene….!?Hussaina ta k’ifta idanunta sannan ta runtse idanun ta saki numfashi tace “Rabin raina kin canza gaba d’aya …..me yake shirin shigowa rayuwar mune….. Menene yakawo wad’annan mutanen gidanmu ……!?nasan da saninki sukazo ……menene alak’arki dasu ne ….bafa kya b’oyemin komai kissanar dani ….zuciyana tanata kai komo da k’issima abubuwa iri iri Rabin raina ……don Allah kifitar dani daga kokonto …..”

Hassana kallon sisinta take da idanuwanta ke runtse tana zaro magana ….ta bud’e baki Dan bata amsar tambayarta saiga Umma tafito …..sai da gaban Hassana ya fad’i ganin kallon da Umma ke mata ….Umma tak’araso gabansu tana cewa”amma dai hira da surutu kuka tsaya yiko ?wanke wanken nawa yake da har yanzu Baku k’arasa ba …. !?ina Usman ya shiga ne ?

 Usman dake ktcheen yana k'arasa gyaran zogale yalek'o jin Umma na nemansa yace "Allah Umma gani anan inayi miki aiki, bafa fita nayi ba " Umma tayi dariya tace "ai daman bance ka Fita ba  autana ....bar wannan aikin kazo " Usman yafito yana karkad'e hannayensa yazo gaban Umma .....Umma ta dubi Hassana da kanta ke sunkuye duk tsoro ya cikata ,ga kuma Hussaina dake rarraba ido ta kalli wannan ta kalli wancan....Umma tace da Hassana "d'auraye hannunki kije ki saurari bak'i zasuyi magana dake ....ki kuma kama kanki ....duk da nasan ke me kamun kan ce.... Ki taimaka musu da abinda kike ganin zaki iya ....naji hankalina ya kwanta dasu ne shiyasa ma har nabasu Damar magana da ke .....Allah yasa abinda duk zaku tattauna yazama alkairi da maslaha a rayuwa ....tashi kije Hassana " kai kuma Usman zauna ka karb'i d'aurayar kataya Hussaina kuyi saurin gamawa ...ita saita karb'i sab'in ...."Usman yafara murna zaiyi wanke wanke danshi akwaishi da son taya aiki irinna mata"



Jikin Hassana a sanyaye ta mik'e ta wuce zuwa d'akin ....yayinda aka bar Hussain a tana zazzare idanu da yiwa Umma kallon mamaki ....Umma talura da ita amma sai bata tsaya gareta ba Dan tasan zata dameta da tambayoyi ne akan abinda bata saniba itama ....shigewar ta kitchen tayi tabar Hussaina da sakin baki galala tana binta da kallo har Umman tayi shigewarta ....Usman ne yakama jijjiga hannunta da fad'in "Adda Hussaina kicigaba da wankewa mana sonake nafara d'aurayewa...."

Hassana zaune k’asa wajen k’afafun mamma dake zaune kan kujerar falon Umma ,Aunty Nafeesa na gefensu a zaune itama …..kan Hassana a sunkuye yake tana sauraren mamma dake cewa “My daughter ki bud’e kunnanki da kyau yau zanbaki labarinmu da kuma dalilin da yasa sageer shiga wannan hali… Da kuma irin taimakon da nakeso kimin …..” Tayi ajiyar zuciya sannan tafara …

Da farko dai sunana shine hajiya lubna ,mahaifina shahararren mai dukiya ne a garinnan a lokacin da yana Raye …..ni kad’ai ya mallaka a duniya shiyasa yake tsananin k’aunata ,ya sangartani sosai babu kwab’a babu harara ,babu kuma Wanda yake ragawa a kaina hatta mahaifiyata ….shiyasa nafi shak’uwa dashi sosai fiye da mahaifiyar tawa …..tun daga yarinta ta har zuwa girmana nayishine cikin sangarta da girman kai da d’agawa saboda arzik’in da Allah yayiwa mahaifina da shagwab’anin da yayi ….ko a school malami bai isa ya tab’ani ba sai Abbana yaje school yaita fad’a …wani lokacin har police yake d’akkowa malami idan har aka dokeni a school …..haka nagama Makaranta a daddafe har zuwa jami’a inda na karanci b’angaren business domin na dinga taimakawa mahaifina dalilin shi d’an kasuwa ne ….

A jami’a Allah ya had’ani da mustafa Wanda ya mato a kaina ….mustafa na sona kuma bayason laifina ….naci sosai ya dingayi min wajen ganin ya kafa soyayyarsa a zuciya ta …..samari da yawa suna son tunkarata da Kalmar so amma suna jin tsoron wulak’anci na saboda yadda sukaga ina wulak’anta maza ….amma duk da haka mustafa ya jure wulak’anci na …baya fushi dani duk abinda nayi masa ….ko fushi nayi dashi haka zai durk’usa gabana yana kuka da Neman afuwata ….Allah ya jarrabi mustafa da matsanancin sona ta yadda yake ko mai nace masa tofah ya zauna kenan …..ganin hakan sai nayi tunanin gara na auri mustafa tunda yana soma ta yadda zan juyashi son raina…. Zanyi abinda naga dama bashida bakin magana ….nima inason mustafa ,sai dai son da nake masa ko Rabin Wanda yake min bai kai ba ….mustafa na gabatarwa mahaifina a matsayin Wanda zan aura ….mahaifina yaji dad’i sosai ,amma yakafawa mustafa sharad’in bayason ya dinga b’ata min rai …duk abinda nakeso shi zaiyi min ….babu tunanin komai mustafa yace ya amince saboda son da yakemin .

  A kayi bikinmu nida mustafa ,bikin da saida gombe state tasan anyishi saboda kashe kud'in da mahaifina yayi ....babu abinda bai manaba nida mustafa .....a cikin amarcinmu mustafa ya d'anji dad'in zama dani kuma yana lallab'ani kamai k'wai ....duk abinda nakeso shi akeyi ....mustafa ne kemin biyayya kamar ya kwanta na takashi ,sai yazama kamar nice mijin shine matar ......sosai mustafa yake hak'uri dani ko ajikinsa .


 Haihuwar fari da nayi mace na Haifa wato Nafeesa ....a lokacin shekara biyu da aurenmu ...kuma ina Aiki a k'ark'ashin mahaifina ....shekarar Nafeesa uku nasamu wani cikin ,naji ina bala'in k'aunar wannan cikin fiye da na fari tun baizo duniya ba ....watan cikin biyar mahaifina da mahaifiyata suka rasu rana d'aya sakamakon had'arin jirgin sama ......nashiga tashin hankali me d'umbun yawa a wannan lokacin ....gani nake tunda gatana ya mutu wato mahaifina to banida wata walwala kuma ....mustafa yasha wahala a wannan lokacin ganin yadda na zabge ,ga bala'in kuka da masifar da nake masa tamkar shine ya kashemin su ...haka zansa shi gaba inta kuka shima yana tayani ...a haka har nayi bacci shikuma ya lallab'o ya rungumeni ....a lokacin ko kula da Nafeesa dainawa nayi ...sai y'an aiki ke kula da ita da kuma mustafa .

Wata hud’u da mutuwar na haifi sageer …haihuwar da ta tafi da dukkan bak’in cikina saboda jarabar son jaririn da Allah ya d’oramin ….naji a duniya inason wannan d’an fiye da komai …lokacin mustafa yaji dad’in kwantar da hankali na da nayi …kasancewar ni kad’aice a wajen mahaifina shiyasa nagaji dukiya mai tarin yawa ,mahaifina ba wasu dangi ne dashi masu yawa ba kuma basu cika zuwa garemu ba kodan ganin halayyarmu ta wulak’anci da d’agawa ,mahaifiya kuwa bama Y’ar Nigeria bace ,a can yawon kasuwancinsa ya Aurota yatawo da ita….shiyasa banida wasu cikakkun dangi na azo a gani ….mustafa kuwa d’an dangi ne …kuma sosai danginsa suke bak’inciki da halin da ya tsinci kansa na samun mace Mara kirki wadda take wahalar dashi .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button