HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

wash nagaji wallahi typing akwai wahala fans shiyasa bana iyawa da yawa kwana biyu ,in kuma na maidashi bayan kwana bibiyu to saiku dinga samu da yawa ,inkuwa kullum ne gaskiya sai dai kad’an ,ngd

Comment
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page6⃣3⃣to6⃣4⃣

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W )YACE “MA’ABOCIN AYYUKA BIYAR BAZAI SHIGA ALJANNA BA

1, MASHAYIN GIYA
2, WANDA YAYI IMANI DA SIHIRI
3, WANDA YA YANKE ZUMUNCI
4, BOKA
5, MAI YIN ANNAMIMANCI

AIKI ME FALALA????

DUK WANDA YACI ABINCI KUMA YACE (BAYAN GAMAWARSA)” GODIYA TA TABBATA GA ALLAH WANDA YA CIYAR DANI WANNAN ABINCIN KUMA YA AZURTANI DASHI BATARE DA DABARATA BA,KO KUMA K’ARFI NABA ,TO ANGAFARTA MASA ABINDA YA GABATA NADA GA ZUNUBINSA

  ***Sun dad'e a haka cikin maida numfashi da karad'ewar sanyin dad'i a jikkunansu ,kafin Hamma Sageer yad'ago kansa daga tsakiyar k'irjinta idanunsa a lumshe yana sakin ajiyar zuciya ,kunya me matuk'ar nauyi yakeji saboda abinda ya aikata baisan menene yajashi hakaba ,sai dai yasan zuciyarsa ce ta sarrafa kanta ta hanyar rayawa cewa kamar da sweetynsa yake tare ,a hankali ya kwantar da kansa saman kujerar idanunsa a runtse yana sauke numfashi gabad'aya a b'ace yakejin jikinsa kamar yadda yakejin yadda cinyoyinsa suke a b'ace saboda ambaliyar da Hussaina tayi masa ,ji yakeyi anya kuwa ba fitsarin tayi masa ba ....!?

Ya D’an jima a hakan itakuwa tana mak’ale a cinyarsa takasa motsi ,itama kunya ce da mamakin Hamma Sageer suka dameta, shiyasa takasa yunk’urin mik’ewa ,kamar daga sama taji maganarsa a hankali yace “keh d’agani ….” Sai ta D’an d’ago tana kallon kyakkyawar fuskarsa da dogon hancinsa Wanda yad’anyi fad’i kad’an daga k’asa ,ga sajensa da yaketa shek’i da walwali ,mak’wallaton wuyansa yanata kaiwa da kawowa ,maganarsa tasakeji inda yace “idan kin gama jik’amin jiki da fitsarin kuma kin gama kallon nawa ki d’agani nace ….” Wata kunyar tak’ara kamata amma haka ta daure tana d’agowa a hankali musamman da taga idanunsa a rufe ,ai da sauri tak’arasa mik’ewa da gudu tashige bedroom tana Jan towel d’inta zuwa sama .

Tana shiga toilet ta wuce don gyara jikinta ,wani irin Abu tagani yafita ta k’asanta duk ya b’atata me yauk’i ,lumshe idanunta tayi tana tambayar kanta menene wannan ….!?babu me bata amsa shiyasa ta tsuguna tayi tsarki da ruwan d’umi kawai ta fito .

Tana cikin saka kaya yashigo d’akin kansa a sunkuye ya wuce toilet ,wanka yasakeyi harda wankan tsarki saboda bai yadda da kansa ba kwata kwata ,sanda yafito takoma falon shiyasa yasake ya shirya cikin k’ananan kaya masu matuk’ar kyawu da burgewa ,nan da nan yafito fes dashi sai zuba k’amshi yakeyi kamar anyi b’arin turare .

A falon ya isketa kwance cikin kujera ta takure ,ya D’an dubeta fuska babu walwala yace “me zakici …!?d’ago kanta tayi ta kalleshi ganin sun had’a idanu tayi saurin d’auke kallonta daga garesa tace” duk abinda yasamu zanci ….”ya d’anyi jimmmm kamar zai magana sai kuma ya kad’a kansa yafice yana kulleta ta waje.

Tana nan kwance tunani iri iri ya dameta, ganin abun takeyi tamkar almara wai yau ita matar Sageer ce ,masoyin rabin ranta ,mutumin da babu wata alak’a me kyau tsakaninta dashi amma yazama mijinta ,tadinga tuno Hassanarta tun daga k’uruciyarsu har zuwa girmansu da irin son da sukewa juna ,ta tuno ahalin gidansu da irin shak’uwa da soyayyar da ke tsakaninsu da iyayensu ,ta tuno Ya Abdurrahman da son da sukewa juna da tattalinta da yakeyi a kullum bayason b’acin ranta ,wai yanzu komai ya kau tarasa komai ,babu Hassananta a fad’in duniya ,babu masoyinta Ya Abdurrahman ya barta ya gujeta ,babu iyayemta da y’an uwanta tayi nesa dasu ,wani irin kuka me bala’in ciwo ne ya kamata ????ta rushe da kuka ta mik’e tayi bedroom da gudu gudun kar Hamma Sageer yadawo ya ganta tana kuka ,tafad’a kan bed d’in hawaye na malala kamar anbud’e famfo .

Fad'awarta kan gadon sai taji kamar tafad'a kan wani ,shiyasa ta mirgina tasa hannu domin zaro abun saitaga hijabinta ne da k'ullin wani Abu ajikinsa daga gefe ,tayi niyyar cillar da hijabin sai zuciyarta ta umarceta tabud'e taga menene a k'ulle a jiki ,tana kuka tasa hannu ta kwance sai taga farar takarda ,tun abayan takardar taga anyi rubutu da manyan bak'i anrubuta SISINA ,wannan yasa gabanta fad'uwa saboda ta tabbatar wannan takarda daga hannun Hassanarta tafito .

A hankali ta warware takardar idanunta na zubda hawaye sai taci karo da kyakkyawan Rubutun rabin ran ta .

Aminci ya tabbata agareki ya ke Y’ar uwata abar so da k’auna a zuciyana

Nasan a lokacin da wannan takarda zata sameki tuni nadad’e da amsa kirani ubangijina ,idan har kika karanta ina rok’onki da kitemakeni kimin alfarmar abinda zan rok’a agareki ,bayan nida zuciya ta babu Wanda yasan irin son da nakewa Hamma Sageer sai ke, amma alamu sun nuna bazanyi rayuwa da Hamma Sageer ba ,babu wadda yakamata ta mayewa Hamma Sageer gurbina idan bake ba ,sisina lokacin da kika Shafa kikaji babuni a doran duniya to ki auri Hamma Sageer ,ki kulamin dashi kamar yadda zaki kula dani ,in kikaga zai kauce hanya kimasa nasiha karki kyareshi ,karki masa masifa ,kuma karki kirashi da D’an da ba ko D’an iska

k’addara ce tasaka Hamma Sageer aduk yanayin da kika ganshi bawai son ransa ba ,inason ki tattara duk soyayyar da kikemin kimik’awa Hamma Sageer ,ki soshi ,ki k’aunaceshi ,ki tarairayeshi ,karki bari yashiga damuwa ,karki bari yakoma shaye shaye ,ganinki kuma zai dingaji tamkar dani yake tare,zan barku badan inaso ba saidan lokacina yayi ,nasan zakuyi kuka Mara yankewa keda Hamma Sageer amma inason Ku rarrashi junanku ,a k’arshe ki k’ara nemamin afuwa agurin kowa ,kicewa Umma na da Babana su tausayamin idan nab’atamusu suyimin afuwa ko zan samu sauk’i cikin k’abari na ,ki jaddadawa Ya Abdurrahman godiyata da fatan alkairi agareshi ,kicewa Hamma Sulaiman shid’in wani jigo ne acikin komai nawa ,ki rik’emin Hamma Sageer amana kice yayi hak’uri da rashina yayimin addu’a ,kicemasa natafi da matuk’ar sons a da tausayinsa acikin k’irjina

Allah ya had’a fuskokinmu da alkairi ,INA sonki sisinah????

Tunma kafin tagama karantawa tuni takardar ta jik’e sharkaf da hawayenta ,jitakeyi tamkar ta mutu ta huta itama ,bazata dena kukan rashin Hassanarta ba har k’arshen numfashinta ,fad’uwa tayi a gadon tana birgima da kuka tana fad’in “don Allah Hassanana kidawo gareni na ganki ko zanji dad’i, mutuwa meyasa kikayi min haka ?meyasa kika rabani da Y’ar uwata …!?na karb’i amanarki da hannu bibiyu ,zan kulamiki da Hamma Sageer koda hakan na nufin rugujewar rayuwata ,bazan k’ara tsanarsaba ,bazan k’araimasa rashin kunya ba ,bazan k’ara kiransa da D’an daba ba ,zan zame masa mace tagari tamkar yadda zaki zame masa, zan kula da lamarinsa tamkar yadda zaki kula ,Hassanana zan hak’ura da duk wata soyayya da nakewa ya Abdurrahman kodan nacika miki burinki wajen kulawa da Hamma Sageer d’inki ????Allah ya jik’anki rabin raina ????Allah yasa kina cikin aljanna ….”

Surutan da taitayi kenan tanaji azuciyarta zatayi sukkan me yiwuwa wajen kula da amanar Hassananta ,ta hak’ura da nata farincikin har zuwa sanda zata iske Hassananta ta ,domin tasan tabbas itama zataje inda Hassananta take ko ba dad’e ko bajima .

  Motsin shigowar Hamma Sageer ne a falon yasata saurin b'oye takardar k'asan pillow ,sannan ta goge hawayenta ta runtse idanunta tamkar me bacci .

Da sallamarsa yashigo d’akin rik’e da Leda d’auke da abubuwanci da Sha iri iri ganinta kwance tana bacci yabashi mamaki daga fitarsa har tayi bacci kenan …!?ajiye kayan yayi ya matso inda take yana kallon fuskarta da ta nuna alamun tayi kuka fitarsa ,a hankali ya sunkuya yad’an Shafa wuyanta yajishi dad’an zafi ,lumshe idanu yayi a hankali ya furta cewa “da ni da ke kuka ba zai tab’a k’arewa agaremu ba ,hawayen mu bazasu dena zuba ba ,ko munyi alk’awarin sharewa juna hawaye dole watarana mu barsu su zuba idan muka tuna da sweety na ,a karo na farko inayi miki ta’aziyyar babbar masoyiyarki me tsananin k’aunarki ” hawayensa yad’iga akan fatar idanunta ,da hanzari yabar wajen yakuma ficewa daga bedroom d’in Dan kar ya tasheta ,baisan cewa idanunta biyu ba .

Ranar duk haka suka wuni jikinsu sukuku ,musamman Hussaina da idan tatuna wasik’ar Hassana hawaye kan zubo mata ,indai kuma Hamma Sageer yagani zai kai hannunsa fuskarta ya goge matasu ,har yagaji yace mata “kina wahalar da hannuna wajen gogemiki hawaye ,idan hannun ya gaji zan cigaba da goge miki da bakina ” tilas haka tayi shiru idanma hawayen ya ratso idanunta sai tafaki idanunsa ta goge .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button