HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hassana tayi murmushin da ya k’ara fito da kyawunta tace “kudena godemin …Ku godewa Allah shine abin godiya “

“Alhamdulillah “mamma da Aunty Nafeesa suka ambata a tare …

      Mamma da Aunty Nafeesa suka mik'e da nufin tafiya ,a lokacin biyu saura y'an mintuna ...mamma nacewa " my daughter na b'ata miki lokaci da yawa ...Allah yasa baki makara ba " nace"ban makara ba mamma akwai sauran lokaci ay ,sallah zanyi nasa unifoam kawai mutafi ..." Suna fitowa tsakar gidan saiga Hussaina sanye da unifoam a jikinta har ta shirya ,hannayenta d'auke da babban tire an shirya Abinci da kunun zak'i akai ta tawo kawowa su mamma ,fuskarta babu yabo babu fallasa take duban su mamman ta karya wuya tace "Ayya ga abinci Umma tace akawo muku kuma naga kun fito zaku tafi...." Aunty Nafeesa ce tace "wallahi a k'oshe muke Hussaina ...mun gode" Umma da ke ktcheen tafito tana fad'in "haba Nafeesatu ai idan bakuci ba bazanji dad'iba ....idan ke bazaki ci ba kibar hajiyar taci to ....abin marmari ne fa ....yau Dambu nayi sha'awar yi " Mamma ta kad'a kai ta na murmushi tace "Maman twins kin San kuwa na dad'e banci Dambu ba ....nidai gaskiya zanci ...bari kawai natafi dashi gidan Nafeesa sai naci a can tunda mun fito ....Aunty Nafeesa ta Sosa k'eya tace " ah tunda Dambu ne nima zanci Umma "Umma tayi dariya da fad'in " ba kin tsaya fulako ba ...hajiya karki sammata ki cinye ke kad'ai "gaba d'ayansu suka kwashe da dariya .  Umma tayi kiran Usman tace ya karb'i abincin yabisu dashi ya kaimusu ,mamma nata godiya Umma na fad'in babu komai ....A gurguje Hassana ta shirya tayi sallah ...abincima d'an tsakura tayi kad'an saboda sun kusa makara ....sukayi wa Umma sallama suka fita..... Sun fara tafiya shiru kowa da abinda yake sak'awa a ransa ..ba zato ba tsammani maganar Hussaina ta daki dodon kunnen Hassana inda Hussainar ke cewa " me Maman d'an daba tazoyi a gidan mu yau ....!?da Hassana ta juyo sai taga ba ita Hussaina ke kallo ba wani b'arin take kallo tamkar ma ba itace tayi maganar ba ...hakan yasa tayi shiru bata amsa taba... sai da Hussaina takuma mai maita tambayar sannan Hassana ta kuma juyowa ta kalli sisinta tace "na'am ,wai magana kikeyi ne sisina ....!?me kika ce....!? Wata harara Hussaina ta gallawa Hassana ta gefen ido sannan tace " Au bakima ji abinda nace ba kenan ...!?toh Shafa kiji ...!?Hassana takai hannunta cikin nik'ab d'in Hussaina ta Shafa kumatun sisinta tana dariya tace "Ayya sisina na Shafa naji laushi .....ga wani guri kuma ya lob'a " ta cusa hannunta cikin dimple d'in Hussaina.


  Dariya sosai Hussaina tayi har saida Hassana ta matso kusa sosai tace mata "a hanya fa muke sisina ...kidena wannan dariyar kar kisa adinga kallonmu ....kin San me ...!?akwai labarin da zan baki ke da Umma da daddare insha Allah ....labari ne me cike da abubuwa iri iri Wanda nake buk'atar shawarar Ku akan labarin ...."   Isowar su k'ofar Makaranta yasa suka dakata da maganar ...sannan suka d'age nik'ab d'in fuskarsu, Asma'u Y'ar ajinsu ta hangosu daga nesa tanata d'aga musu hannu su tsayata ...Hassana ta lura da ita tace "sisina kinga ma'u can yau itama ta makara ...bari ta k'araso mu shiga tare ...." Kallon ma'u Hussaina tayi saikuwa ta kwashe da dariya harda sunkuyawa ,Hassana tabita da kallon mamakin metake yiwa dariya ...har Asma'u ta k'araso da sauri gabansu tana haki ...Hussaina na d'agowa ta kalli fuskar Asma'u sai takuma kwashewa da dariya ....ma'u ta dubi Hussaina tadubi jikinta tace "kefa Y'ar rainin hankalice hussy ...banda iskanci menene abin dariya a jikina ...!?Hussaina bata dena dariyar ba tasa hannunta a fuskar ma'u da keta k'yalli saboda man da ta lafka tace " Allah ma'u sai a tatsi mank'uli jarka guda a fuskarki ...kinga uban shining d'in da kike kuwa ...!?sai lokacin Hassana tagane abinda sisinta kewa dariya ...itama kasa rik'e dariyar tayi ganin yadda fuskar ma'u ke maik'o kamar an tsamo k'osai a cikin mai .  Da hanzari ma'u tasa bayan hijab d'inta tana goge fuskarta tana cewa "wallahi yau Umman muce bata nan aka barmin aikin gida komai ya rincab'emin....inata saurin gamawa karna makara shine fa na lafta mai da nayi wanka ,ban tsaya gogeshi nasa fowder ba na zabaro na tawo..." Tana bayani tana goge fuskar tata har maik'on ya ragu .


   Ta cikin get d'in Shiga makarantar Malam Huzaifa ya lek'o yayi gyaran murya ..duk suka waiwayo suna dubansa ...sai kuma suka durk'usa suna kwasar gaisuwa ...ya amsa yana cewa "me kukeyi a waje kuka kasa shigowa Makaranta ...!?Na tabbatar Hussaina da Asma'u kune kuka tsaida malama Hassana ko ...!?yafad'a yana yiwa Hassanar wani irin kallo ....murmushi sukayi gabad'ayan su Hussaina tace" ba ruwanmu Malam ,saboda ita bata laifi kenan ...!?yace"kin fad'i gaskiyar zance bata laifi ...ita d'in ai ta dabance ko ranki ya dad'e ...!?ya juya akalarsa ga Hassana da kanta ke sunkuye tana murmushi .

Jiyo karatun d’alibai a cikin Makaranta yasa suka shiga ciki ,Hussaina da ma’u sukayi gaba …Hassana nabinsu a baya inda Malam Huzaifa yayi k’ok’arin jerawa da ita yana magana a hankali “kink’i bani dama dai Hassana …na rantse sonki nake ba da wasa ba ….duk bugawar numfashina da sonki a cikinsa ….amma dai zansamu lokaci nazo gida muyi maganar …bazata yiwu a Makaranta ba ” Hassana dai jinsa takeyi har sukazo dab da ajinsu sannan ya waske ya shige office d’in malamai tamkar ba magana yakeyi da itaba …wai Dan kar agane.

Bayan sun tashi daga makaranta ne suka tawo duk agajiye suke saboda gwajin musabak’a da sukayi ,Dan Hussaina tun a hanyar take damun Hassana da cewar kanta ciwo yakeyi ….suna shiga layinsu Hassana tayi kyakkyawan gani …sageer zaune kan dakali da sigarin sa a hannu yana shan abarsa hankali kwance …wani mugun tsaki Hussaina tasaki da yasa sageer d’agowa ya zuba mata idanu …harara ta banka masa sannan ta motsa bakinta da fad’in”D’AN DABA KAWAI”a fusace kuma tayi gaba dajin sabuwar tsanarsa a ruhinta.

Yabita da kallo yana k'issima abubuwa da yawa a ransa ...a zuciyarsa yake jin ya kusa yayi maganin rashin kunyarta ....har shi zata kalla ta kirashi da d'an daba....!? Sigarin hannunsa da aka zare ita tabashi damar waigowa yana duban Hassana dake masa murmushi ....shima wani irin kallo yabita dashi zuciyarsa na bugawa da k'arfi ...saukar sassanyar muryarta yaji a kunnensa inda take cewa "yau dai nima bari nasha sigarin nan naji me Hamma sageer yakeji idan yashata ....nima naji wane kalar dad'i Hamma sageer keji idan yasha " tafad'a tana lumshe idanu da d'aga sigarin domin kaiwa bakinta ...da wani mugun hanzari sageer ya mik'e ganin da gaske sigarin zata kai bakinta ya kai hannu da nufin k'wacewa ....da sauri itama tayi baya tana b'oye sigarin a bayanta tace "Ayya Hamma sageer ba dai Rowa zakai min ba ....tunda naga kullum kana Shanta nasan zatayi dad'i...Dan Allah kabarni na d'and'an dad'inta nima...!kamar dolo haka yake kallon Hassana a gabansa ya kasa magana ....sai dai girgiza mata kai da yakeyi ....

D’an kawar da kanta tayi tace” kar nasha Hamma sageer …!?bakaso nasha ….”da sauri ya gyad’a mata kai …tayi murmushi me kyau tace “me yasa …!?ya d’anyi walai da ido ya langab’e kai yana d’an cizan lips d’insa …kamar an fizgi maganar abakinsa taji ya ambaci ” bata dace da keba “muryansa tayi mata zak’i matuk’a …a tsawon ratuwarta bataji muryar namiji me dad’in ta sageer ba ..shiyasa saida tsigar jikinta ta tashi saboda jin yanayin muryarsa ….da murmushin akan fuskarta tace” ai kaima bata dace da kaiba Hamma sageer…na rantse hanyar jirgi daban na mota daban …aini Hamma sageer nayi zaton cewa ba sai Abu yadace da mutum yake aikatawa ba …kamar dai yadda shan sigari bai dace da kaiba amma kuma kakesha …”

Kasak’e yayi yana dubanta ,wani Abu na Shiga zuciyarsa gameda ita ….bai tab’ajin mace tashiga zuciyarsa haka ba …ta kuma d’ago sigarin ganin yayi shiru tace “in sha….!?Hamma sageer ka yarda insha …!?girgiza mata kai yayi idanunsa na Tara ruwan da bai San na menene ba yace ” ah ah ,Don Allah karki sha …!?Hassana ta sunkuyar da kanta k’asa a hankali tace “toh ka yarda kaima bazaka kuma shaba ….!?na rantse idan naganka kanasha raina biyawa zai dingayi …Hamma sageer kacemin kadena sha…nima sai nadena sha’awar sha .

Sautin murmushinsa yasa ta d’ago tana kallonsa …kallonta kawai yake a gabansa yarinya da ita wai zatayi masa wayo…. Itama saita bishi da murmushin tana cewa ” Ai nasan Hamma sageer zai daina shan sigari ….ka daina ko ….!?sai kurum yasamu Kansa da gyad’a mata kai yana murmushi alamun ya daina…Hassana ta runtse idanu da fad’in “Alhamdulillah” Afili ..sannan tabud’e idanun akan fuskar Hamma sageer tace “Allah yasa da gaske kake Hamma sageer …Allah yasa idanuwana bazasu kuma ganin sigari a hannun kaba ….ta jefar da sigarin a k’asa tana takewa ..sannan ta Nuna masa get d’in gidan Aunty Nafeesa tana cewa” lokacin sallar magriba yakusa ..kaje kayi alwala Hamma sageer …idan kayi sallar ina rok’on addu’a a gareka …nima zan maka addu’a Hamma sageer….

Babu musu ko ja’inja yazura hannayensa a aljihun wandonsa yafara takawa yanufi gidan yana waiwayenta sunaiwa juna murmushi,sai da taga shigewar sa ciki sannan itama ta kad’a kanta ta nufi gidansu zuciyarta fes……

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

TYPING????

???????? HASSANA ????????

       *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page2⃣1⃣to2⃣2⃣

WATTPAD:hassana3329

DEDICATED TO

HUSSAINA D’AN LARABAWA (SISINA) BAZAN CE KOMAI A KANKI BA DOMIN KIN SAN K’AUNAR BA MAI YANKEWA BACE ,ZUCIYAR HASSANAR KI KULLUM CIKE DA K’AUNARKI TAKE,INAI MIKI ADDU’AR FATAN ALKAIRI HUSSAINA TA????????????

ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH(S W A ) MAD’AUKAKIN SARKI DA YA BANI LAFIYAR CIGABA DA RUBUTA MUKU WANNAN LITTAFI ,TSIRA DA AMINCI SU TABBATA GA SHUGABAN MU MASOYIN MU ANNABI MUHAMMAD (S A W ) NI HASSANA D’AN LARABAWA NA GODEWA ALLAH ,NA KUMA GODEWA IYAYE NA DA MIJINA DA YARANA DA Y’AN UWANA DA DANGINA DA K’AWAYE NA DA MAK’OTA NA DA MASOYA NA A DUK INDA SUKE ,LALLAI RUBUTU BAIWA NE WANDA BAZAKA SAN HAKABA SAI IDAN KANA RUBUTU WANI ABU YAFARU DA KAI NA FARINCIKI KO AKASIN HAKA ,ANAN ZAKA TABBATAR DA CEWA KANADA TARIN MASOYAN DA BAKASAN YAWANSU BA ,A KARO NA K’ARSHE INA K’ARA CEWA NAGODE MASOYANA????????????

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W )YACE “DUKKAN WANDA KUKA YABESHI DA ALKAIRI ,TO ALJANNA TA TABBATA A GARESHI,KUMA DUK WANDA KUKA AMBACESHI DA SHARRI ,TO WUTA TA TABBATA A GARESHI,KUMA KU SHAIDUN ALLAH NE A BAYAN K’ASA

ALLAH MUNA ROK’ON KA KASA A YABEMU DA ALKAIRI A LOKACIN RAYUWAR MU DA BAYAN MUTUWARMU????

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W )YACE ” DUK WANDA YA LAMUNCE MIN ABIN DA KE TSAKANIN HARSHEN SA DA ABIN DA YAKE TSAKANIN FARJINSA ,TO NA LAMUNCE MASA GIDAN ALJANNA

Shigar ta gida da sallamarta yabawa Umma damar amsawa ,wadda tafito daga bayan gida d'auke da buta a hannunta ,Hassana tace "Umma sannu da gida " kallon ta Umma tayi tace "yauwa Hassana ,menene ya tsayar dake har Y'ar uwarki tariga ki shigowa gida yau ...!?bayan kullum tare kuke dawowa ....!?kafin Hassanar tayi magana wuf Hussaina ta d'aga labulen d'akin su ta lek'o tace " Umma kin san ta da lak'ai lak'ai nikuma kaina na ciwo shiyasa na barta a hanya nayi saurin dawowa Dan nasha magani "a b'oye Hassana ta sauke ajiyar zuciya saboda yadda sisinta ta cetota ,Dan batasan me zata gayawa Umman nasuba ,Umma tace " Ayyah ,toh kin sha maganin dai ko . .!?eh nasha Umma ...munada ragowar paracetamol daman ...!inji Hussaina da ke hararan Hassana ta gefen ido ,"toh Allah ya sawak'e yabada lafiya "cewar Umma tana janyo butar gabanta Dan gabatar da alwala .

Daga hakan Hussaina takoma d’akin yayinda Hassana tabita ciki ,Umma tad’aga murya tana fad’in” Ku fito kuyi haramar sallah ,kun San magriba da saurin wucewa …karku bari ta kufce muku….!

   A tsawon Daren Hussaina tak'iyiwa Hassana magana ,duk yadda Hassana taso ta saurareta tak'i yarda, ba k'aramar damuwa tashiga ba ganin fushin da sisinta takeyi da ita..... Har zuwa sanda suka hallara gabad'ayansu a falon Baba ...inda Hamma sulaiman yakawo musu sababbin wayoyin su masu azabar kyau ...sunyi murna da godiya sosai ...inda Hassana ta matsa jikin Hussaina tana nuna mata tata wayar tana cewa "sisina kinga nawa wayar ...bani naki nagani kinji "sai Hussaina tayi mata banza ta juyar da kanta gurin ya safwan tana cewa " ya safwan duk gidannan Kaine d'an birni bari nazo ka koyamin yadda zanyi amfani da wayar nan "jikin Hassana yayi sanyi hawaye yaciko idanunta ganin abinda sisinta ke mata ...cikin dabara tasaka hannu tana goge hawayen yadda baza'a kula ba ..amma ina tuni Hamma sulaiman yagani ...ji kawai sukayi Hamma sulaiman da muryar b'acin rai yace " ke Hussaina. ..."Hussaina dake dab da safwan ta zura kanta ta kafad'arsa tana ganin yadda yake sarrafa wayarta cikin k'warewa ta d'ago kanta a tsorace jin yanayin muryar Hammansu tace "na'am Hamma" yayi mata wani kallo yace "zo nan " duk gurin ya d'auke wuta ana son sanin me yafaru ...ita kuwa da batasan laifin da tayiba saita taso sumu sumu tazo ta tsuguna gaban Hamma sulaiman tace "gani Hamma"


    "Me ke tsakaninki da Y'ar uwarki ...!?abinda yace kenan idanunsa a kanta "Hussaina ta d'anyi Jim ,sai kuma tace " Y'ar uwata kuma ?Hamma bangane ba ...."ya wani k'ank'ance idanu yace "zan mareki fa ...wallahi zan mareki Hussaina ...nasan idan na mareki zaki gane ai ko ...!?

“Jin abinda Hamma yace ya tsorata Hussaina ,tayi saurin b’oyewa a bayan Hamma Aminu jikinta na rawa …Dan bazata manta zafin hannun Hamma sulaiman ba …akwai sanda ya tab’a marinta tana yarinya da sukayi fad’a da wata Y’ar mak’otansu tazane yarinyar ..shine yarinyar takawo k’arar Hussaina lokacin Hamma sulaiman na zaune yana cin abinci …kuma akai akai Hussaina tafad’i dalilin dukan yarinyar amma tak’i ,hakan ya fusata Hamma sulaiman ya mareta ,Marin da ba Hussainar ba hatta Hassana saida ta d’auki fushi dashi saboda ya tab’a mata sisinta .

“Baba ne ya katse maganar da cewa ” me yafaru ne sulaiman …!?me Hussainar tayi ne !?Hamma sulaiman yayi ajiyar zuciyar b’acin rai yace”Baba tunda suka shigo nake lura da yanayinsu kamar akwai wani Abu a tsakaninsu ….ban tabbatar da hakan ba sai Dana lura Hassana tanai mata magana itakuma tak’i kulata ..Baba har hawaye fa Nagani a idanun HASSANAr ,ka santa da k’awa zucin Y’ar uwarta ….nakuma San tabbas ko menene yafaru tsakaninsu Hussainar ce batada gaskiya “ya d’anyi shiru yana maida numfashi ..sai kuma ya kalli Hamma Aminu yace ” kai Aminu mik’omin ita nan …na rantse sai tayi bayani ko jikinta ya gayamata “da sauri Hassanar ta matsa jikin Hamma sulaiman ta rik’e hannunsa tace” Hamman mu nice da laifi fa …na rantse laifi nayi mata Hamma …Dan Allah karka daketa kaji …”Hamma sulaiman ya k’urawa Hassana ido yace “laifin me kikai mata …!?ta d’an sunkuyar da kai k’irjinta na bugawa …ji takeyi da adaki sisinta gara tafad’i gaskiyar abinda yasa Hussain a ke fushi da ita …hakan yasa tad’ago ta kalli Hamma da idanuwansa ke kanta tace” daman akan….

Da sauri Hussaina ta rarrafo tayi wuf ta rufewa Hassana baki ganin zata fad’a …jikinta babu Inda baya rawa take fad’in “yaseen babu laifin da tayi min Hamma sulaiman ….kawai fa wasa ne tsakanin mu hakan da ka gani …” Sai kuma tajuya tana kallon Hassana tace”Rabin raina ai babu komai ko …!?Dan Allah ai babu laifin da mukaiwa juna ko …!?ita dai Hassana tsuru tayi tana kallon sisinta da alamu batason tafad’i abinda yake faruwa …Hamma sulaiman a fusace yace da Hussaina “sakar mata baki malama ” a hankali Hussaina ta janye hannunta akan bakin Hassana cikin dabara ta kad’awa Hassana ido akan kartafad’i komai …. Sai Hamma ya maida kallonsa kan Hassana fuska babu fara’a yace “tunda ita tak’i fad’a ke ki fad’amin menene ya faru …!?cikin in ina Hassana tace” babu komai Hamma …kamar yadda sisina tafad’a maka wasa nefa ….!?kawai Hamma sulaiman sai ya zura musu idanu yana dubansu…shi zasu rainawa hankali kenan …da b’acin rai yace “au ni zaku nunawa had’in kai Ku rainawa hankali ….!?Ku tashi a gabana kar nayi ball daku …na rantse kar Ku sake second d’aya a gabana …kuje Ku cinye kanku ma” Ya fad’a a fusace .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button