HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Lokacin sageer yazo dab dasu ,maganar da matar tayi shine yasaka Hassana hanzarin tare wa sageer hanya ,duk da fad’uwar da gabanta yakeyi …..yayinda Hussaina taja baya da sauri tana watsawa sageer mugun kallo ,a zuciyarta fad’i take “Au bacin DABA wannan mutumin har a iskanci ya k’ore kenan ?kalli yanda yafito ba cikakkun kaya a jikinsa kusan komai a bayyane ….k’irji duk gashi abin k’yank’yami ……..shikuwa Usman da ya fuskanci abinda ke faruwa zagayawa baya yayi ya rik’e bayan sageer ya rungume k’ugunsa ya zagayo da hannunsa ta saman cikinsa ,sannan yad’aga murya yana cewa ” yeee nakama mikishi Umma …..yi sauri kizo ki karb’eshi kar ya gudu ……Umma yi sauri gashi nakama shi ……

Shikuwa sageer ganin Hassana a gabansa k’ik’am ta tare masa gaba shine yabashi damar k’are mata kallo tun daga k’asa zuwa sama ,inda ya dire a kan kyakkyawar fuskarta ,ya k’urawa tusar jakin fuskarta idanu yana kallo a marairaice ,itama Hassana kallonsa take tanajin wani Abu na katantanwa da ita, wani sanyi sanyi takeji na shigarta ,idanuwan sageer na karad’e jikinta yayinda idanuwanta har wani ruwa suka fara tarawa saboda yadda taji gaba d’aya sageer ya kankane mata zuciya .

Isowar matar gurin itada Aunty Nafeesa ,da kuma wani mugun tsaki da Hussaina taja shine yadawo dasu hayyacinsu ,inda matar da hanzarinta ta rik’e kafad’un sageer ,yayinda sageer ya waiwaya inda yajiyo tsaki ,karaf suka had’a idanu da Hussaina dake faman jifansa da harara ……..gabansa ne ya yanke ya fad’i ganin halittu guda biyu iri d’aya a gabansa ……….

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

TYPING????

???????? HASSANA ????????

      *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page 1⃣1⃣to 1⃣2⃣

WATTPAD :hassana3329

DEDICATED TO ALL MY FAN’S????????????

INA TAYAKI MURNAR SAMUN K’ARUWA K’ANWATA RAMLAT IBRAHEEM (HAJJA K’ARAMA)ALLAH YAYIWA BABY ABUBAKAR SADIK’ ALBARKA YA RAYASHI BISA TAFARKIN MUSULUNCI DA IMANI TARE DA SAURAN YARAN MUSULMI ,KE KUMA ALLAH YA K’ARAMIKI LAFIYAR JIKI DA TA SHAYARWA????????????????????????

   ****Sosai sageer yake wani irin kallonsu ,idan ya kalli Hassana sai ya juya ya kalli Hussaina ,tunaninsa ya katse lokacin da yaji muryar Hassana me sanyin dad'i na gaida matar kusa dashi ......ta amsa tana cewa "nagode muku y'ammata " sannan tadubi Usman ta Shafa kansa tace "kaima nagode maka samari da ka rik'emin Muhammad d'ina .....may I know your name .....?ta tambayeshi cikin harshen turanci .


  Usman is my name " amma ana kirana autan Umma..... "yabata amsa yana mata murmushi ......sosai taji Usman ya kwanta mata a ranta shiyasa tai masa jinjina tace " good boy" ,you are a cleaver boy .

Aunty Nafeesa ce ta matso kusa ,sai Hassana ta gaisheta ,tayiwa sisinta alamun ta gaishesu itama ,……Hussaina ta matso ta gaidasu tanata hararar sageer ta k’asan ido ,yayinda sageer har lokacin bai fita daga mamaki ba …..

Hala Ku twins ne ….!?inji matar tana tambayar Hassana …….!naga kamar taku har ta b’aci wannan ai ba za’a iya bambance Ku ba …

Usman ne ya amsa yace “eh twins ne ,ga Adda Hassana ….ya nuna Hassana ……” Ga kuma Adda Hussaina “ya nuna Hussaina da tafara gajiya da tsayuwar gurin sosai ….tun tana hararar sageer har tadawo hararar Hassana da Usman ….a ganinta duk sune suka tsaidasu …..

Masha Allah !abinda matar ta fad’a kenan tana dubansu …..Ai kuwa zan k’ulla zumunci daku ….naji ina sonku a raina ……ni mahaifiyar sageer da Nafeesa ce …..Anan kusa kuke ne ….!?

“Eh mamma ” Kinga kidansu can fa …..anan layin suke…. Cewar Nafeesa tana nunawa mamansu gidan da hannunta .

Basu Ankara ba sai gani sukayi sageer yasaka kai zaiyi wucewar sa ,nan mamma tasaka baki tayi kiransa “Muhammad karka tafi …..pls kadawo Dan Allah ……..Muhammad “

Ko kulata baiyi ba illah k’ara d’aga k’afa da yake Neman yi …..ba zato babu tsammani gaba d’aya sukaji muryar Hassana tace ” Hamma sageeeeeeerrrrrr……..”tawani ja sunan tamkar babu Wanda ya kaita iya ambatar sunan .

A wani irin slow ya juyo saboda muryar Hassana da ta zagaye jininsa ,kallonta yake idanunsa na lumshewa ,gaba d’aya fuskarsa babu annuri ,k’irjinsa na sama da k’asa alamun yana cikin b’acin rai sosai …….Hassana bata cikin irin matan nan masu yiwa maza k’urulla ,amma batasan meyasa takasa dena kallon sageer ba ,wani dad’i takeji idan tana kallonsa .

Idanunta na kansa tabud’e baki da k’yar tace masa “Bakaji mamma na kiranka bane ….!?tundaga cikin gida fa tabiyoka tana faman kiranka kanak’in amsawa ….mahaifiyar kacefa …..haba Hamma sageer ….babu kyaufa mahaifiya na kiran d’anta yak’i amsawa ….kanason fad’awa cikin fushin Allah ne …..!?kasan kuwa aduk duniya idan kacire Allah da manzonsa bakada tamkarta a rayuwa …..ka amsa kiranta Hamma sageer ….kaje ka saurari batunta kaji …….kadena sakata cikin b’acin rai Hamma sageer pleaseeeee…

Tunda tafara magana a gurin kowa yayi tsit ana kallonta ,gaba d’aya jikin sageer yayi mugun sanyi tamkar ya narke agun yake jinsa …..tunda tafara magana har ta kammala kallonta kurum yakeyi …..ita kuwa Hussaina tsananin mamakin Rabin ranta takeyi da k’arfin halin da ta nuna ……ga takaicin sageer da yakuma rufeta ganin Ashe mahaifiyarsa yakewa wannan iskancin ….

Hassana ce ta kuma nunawa sageer hanya tana fad’in ” shiga gida ka amsa kiran mamma … …ka kuma tsaya ka saurareta kayi mata biyayya akan duk abinda ta fad’a …..”ta juya ta dubi aunty Nafeesa dake kallonta da murmushi tace ” Aunty Nafeesa nabaki amana …..idan har yayi gardama ki fad’amin ……nikuma sai nasa kamfanin sigari sun tafi yajin aiki …..Kinga zai rasa abokiyar hira ko Aunty Nafeesa,tun da na lura bashida abokiyar hira irin ta …..!?

     zuciyar Hassana sai da ta kusa bugawa saboda wani irin murmushi da sageer ya saki jin maganarta ,a ranta take cewa daman haka murmushi ke masa kyau......!?idan nice sageer ai ko yaushe da murmushi fuskata zata kasance .....ko Dan kyawuna ya razana mutanen da suke katarin ganin fuskar.   Yana murmushin bai San dalili ba yafara takawa a hankali domin bin umarnin Hassana ....... Sosai yakeji a zuciyarsa yadace yabi umarninta ,duk da babban laifin da yake ganin mahaifiyar tasa tayi masa....... ,idan da akwai masu tsananin mamaki a gun bazai wuce mamma da Aunty Nafeesa ba .....bazasu iya tuna rabon da suga murmushi a fuskar sageer ba ......ba zasu iya tuna randa suka bashi umarni ya biba ......amma tashi d'aya cikin y'an mintuna Hassana tayi aikin da suka kasayi ......menene dalilin hakan ...!?me sageer yagani a Hassana da tashi d'aya yabi umarninta ....!?toh kodai Allah ya turo Hassana cikin rayuwar sageer ne Dan yadawo mutum kamar kowa ......!?wad'annan kad'an ne daga cikin tambayoyin da suka dami zuciyar mamma da Aunty Nafeesa .

Sai da sageer yasaka k’afarsa a harabar gidan sannan ya waiwayo a hankali yana duban Hassana dake rungume da hannu a k’irji tana kallon takunsa …..yayi mata kallo me ma’anoni da damage,sannan ya kawar da idanunsa a kansa,ya dubi Usman dake gefe ya sak’alo hannayensa ta k’ugun Hassana ya rungumeta ya jingina da jikinta ….sai Hussaina dake gefe tana faman harare harare da buntsure buntsure…….bai San lokacin da ya saki murmushi ba sannan ya d’agawa Usman yatsunsa guda biyu ……da hanzari kuma ya shige gidan da sassarfa …..

A zuciyar mamma taji dolema ta k’ulla alak’a da Hassana ganin abinda yafaru ,ji takeyi zata cimma muradinta idan har tasaka Hassana cikin al’amarinsu …..mamma tayiwa Hassana godiya me d’umbun yawa da taimakon ta garesu …haka ma Aunty Nafeesa tayi godiya …..sannan mamma ta karb’i number wayar Hassana da fad’in zata kirata akwai maganar da zasuyi .

Haka sukayi sallama suka wuce bakin titi ,sukuma mamma suka shige gidan …..mamma farinciki takeji Mara misali yau Muhammad d’inta zai saurareta …..tana murna yau sageer zai fuskanceta …..k’aunar Hassana tuni tafara ginuwa a zuciyarta ….ganin alamun Hassanar zata zama tsani na daidaituwar al’amura tsakaninta da d’anta da tafiso fiye da komai a duniya .

Gogar taku kuwa wato Hussaina har suka hau napep tana surfa mita da masifa ,harda murd’e kunnen Usman tana fad’in “waye yacema ka rik’e wannan mutumin ….!?saboda kinibibi wani ya saka ka rik’eshi …!?wallahi ka kiyayeni autan Umma banason shisshigi da cusa kai ….. Ke kuma nadawo gareki Rabin raina …..Ashe bayan DABA da shaye shaye da iskanci har raina iyaye ya k’ore akai …..!?banga abinda ya burgeki da wannan abun ba …..kifita hanyarsa banason alak’ar Ku …..na rantse Baku daceba ….ko kusa ko alama Sam Sam .

Murmushi Hassana tayi ,sannan tacire hannun Hussaina dake kunnen Usman tana murd’ewa ,Usman zafi ya isheshi kamar yayi kuka…. Hassana tace da Hussaina ” sisina babu kyau aibata musulmi ….ko da musulmin ya kasance yana aikata munanan halaye bai halatta ka aibatashi ba ….sai dai kanema masa shiriya gurin Allah …..kidena jifan sageer da wad’annan mugwayen kalaman …..a jikina nakeji akwai alak’ar da zata shiga tsakaninmu dashi …..sai dai ban San wace iri bace ….ina rok’onki kirage tsanar sageer …..kiyi masa addu’a da fatan shiriya don Allah …..wallahi banajin dad’in aibatashi da kikeyi …..inaji ajikina akwai gudummawar da zamu bawa rayuwar sageer sisina “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button