HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

        Hussaina shiru tayi tana numfarfashi ,batasan me zata gayawa Hassana ta yadda ba ....ita dai tasan bazata tab'a ganin girman sageer da mutuncin saba ....tsanarsa takeji sosai a ranta .....musamman da tak'ara tabbatarda rashin d'a'arsa akan abinda tagani tsakaninsa da mahaifiyar sa da yayarsa yau.....sageer ba mutumin da za'a damu da lamarin sa bane ....sageer bai cancanta a tausaya masa ba .... 

                   Har suka isa gidan Aunty sakeena Hassana nata nusasshe da Hussaina ,yayinda take jinta da kunne kawai ....sosai Aunty sakeena tayi murnar ganinsu ,nan suka tarar da Zahra k'anwar Aunty sakeena ce kuma sa'arsu ce .....Zahra tana bala'in k'aunar su shiyasa takes on aminta dasu, yayinda su d'in bawasu k'awaye ne da suba ,sune k'awayen Kansu da Kansu .

Da sukabawa Aunty sakeena sak’on Umma tayi murna sosai tace “kayan yin miyar tuwon ne ….!?nifa dolema inje Umma ta koyamin yadda take tuwo da miya …shekara da shekaru nakasa iya irin nata….. Kullum idan nayi tuwo sai Hammanku yace wai baiyi dad’in na Umma ba …..nikuma inason iya irinna Umma “

Zahra tayi wuf tace “gaskiya Aunty sakeena ai Umman twins ta iya tuwo ,rannan da mukaje dake naci kamar kunnena ya cire don dad’i fa …..” Su Hassana sukayi dariya suna jin dad’in yabon da akewa girkin mahaifiyar su .

Yini zir sukayi a gidan Hamma sulaiman Dan ko gidan Hamma Aminu basu samu lek’awa ba ,saboda yawan Aikin da suka taya sakeena ,ranar sanateshan Aunty sakeena tayiwa gidan ,komai saida suka sauya masa muhalli da share share da goge goge ,Aunty sakeena da Zahra duk da mahaifinsu me kud’ine amma basu sangarce da son jiki ba ….don Aunty sakeena ko Y’ar aiki bata da ita .

Bayan sun kammala komai sukayi girki sukaci ,sannan kowacce tasake wanka saboda k’urar da sukayi ,Usman kam ansamu wasa yana can d’akinsu sadauki suna wasanninsu .

         Sai yamma lik'is Hamma yadawo gidan da sabuwar motarsa dake d'aukar ido tamkar glass ,sosai motar tayi masa kyau tamkar wani babban k'usa ,daman gashi da kyawun ,gabad'ayan mu muka fita don ganin motar mukaita shafata munasa albarka ,nan Hamma kecewa ai d'azu sunje an siyawa Hamma Aminu tasa motar shima ,ankuma siyo keken Usman ,mu kuma gobe wayarmu zata iso insha Allah .....mukaita murna muna godiya Aunty sakeena na tayamu .



Tunda Hamma sulaiman yadawo sai Aunty sakeena ta barmu takoma d'akinsa ,tanata hidima dashi wajen had'a masa ruwan wanka da sauransu ,wankan ma kusan saida ta tayashi ,don Aunty sakeena badai kula da miji ba .....sosai take matuk'ar k'aunar Hamma da sonsa tamkar ta lasheshi .

Har ya kammala wankan Aunty sakeena na biye dashi …yakoma gaban dressing mirror Dan ya Shafa mai nan ma tabishi kamar jela zagwai zagwai, sai faman nanuk’arsa takeyi kamar takoma cikinsa …..da Hamma sulaiman ya fuskanceta sai kurum ya ajiye cream d’in hannunsa ya jawo sakeena ya zauna bakin bed ya d’orata akan cinyoyinsa ….lokacin rigar wanka ce kurum a jikinsa,k’amshin sabulun da yayi wanka yacika d’akin …..tallafo hab’arta yayi yasaka idanunsa acikin nata ya d’an lumshe idanun a hankali kamar Wanda bayason magana yace “menene sakeenan sulaiman ….!?me kikeso ….!? Saboda indai yaga tana haka to yasan akwai magana .

Kunya ce ta kamata ,sai tayi saurin fad’awa jikinsa ta k’ank’ameshi tana ajiyar zuciya …..tun daga nan Hamma sulaiman ya k’ara tabbatar da zarginsa ……saida yak’ara rungumeta yana shafa bayanta da hannayensa masu taushi tamkar auduga sannan ya furta cewa” kina cikin buk’atar mijikinki ko sakeenan sulaiman ….!?ya tambayeta …

Wata kunyar ce tak’ara lullub’eta ganin ya d’agota ….shiyasa ta k’ara cusa kanta a k’irjinsa tana k’aramar dariya ….ya kuma rungume abarsa har tana jiyo bugun zuciyarsa .

Da dabara ya d’agota saboda yadda ta k’ank’ameshi ….ya d’ago fuskarta yana kallon kyakkyawar fuskar matarsa …ganin yadda jikinta ke rawa da yadda lips d’inta ke karkarwa yasan kwanan zancen …idanunta Kansu sun sauya kala ….sosai jikinta ya nuna buk’atar mijinta “

“Kimin wata alfarma mana sakeenan sulaiman …..kid’an barni na mik’a yaran can gida ,Baba baicika son suna kaiwa magariba a waje ba …..nayi alk’awarin yau ko tuwon Umma bazan zauna ci ba …..Daren yau da lokacin cikinsa duk nakine sakeenan sulaiman …… Na rantse nimafa yau ina mararinki ….kuma daman kullum cikin mararin naki nake ……ya dai sakeenan sulaiman..!?zaki iya daurewa zuwa Daren ko zan d’au hak’k’inki …..!?inji sulaiman kenan dake aikawa sakeena rud’ad’d’en sak’o ta idanunsa da hannayensa ….da kuma bakinsa da ke dab da nata ….

Yunk’urawa tayi cikin matsanancin son mijinta da k’aunarsa ,ta kai bakinta dab da kunnensa ,a hankali ta rad’a masa maganar da ni kaina banji ba …..nadai hangi kyakkyawar fuskar Hamma sulaiman tana murmushi ,hannayensa zagaye da k’ugun matarsa …..a hankali ya kuma cusata a jikinsa yana k’ok’arin rage mata zafi kafin Daren …….Hamma sulaiman yasan hak’k’in matarsa da lura da yanayinta akan dukkan abinda take so ….hakanan ya iya wanke zuciya da soyayya me sanyin dad’i… “


Ana kiran sallar magariba a sanda Hamma sulaiman ya saukemu a k’ofar gida ,sanda za’a wuce k’ofar gidan Aunty Nafeesa kuwa Hassana har lek’e takeyi ko zata hangi sageer sai dai batayi nasara ba ,domin get d’in gidan a kulle yake ma ….duk sai taji wani b’acin rai ….taso k’ara tozali da fuskarsa ko babu komai kallon fuskarsa kad’ai nasata nishad’i da jin dad’i a zuciyarta …..Hussaina na lura da ita …wani bak’inciki takeji tarasa me Hassana takeso a sageer …..”

    Ilai kuwa ranar Hamma sulaiman bai zauna cin tuwo ba ....yace da Umma yanada uzuri ....bayan Umma da Baba sunga motar sun  saka albarka sai kurum ya tada abarsa yakoma gidansa....domin cikawa sakeena alk'awari da bata kulawar da take buk'ata..

Washe gari da safe ringin d’in wayata ne ya tasheni …..da k’yar na mik’a hannu na d’aukota saboda magagin bacci ….tunda mukayi sallar asuba muka koma saboda asabar ce babu boko ….gashi sisina tazo ta wani mak’alk’ale a jikina ….ina duba number da ake kirana sai naga bak’uwar Numba .. …….

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page 1⃣3⃣to1⃣4⃣

WATTPAD :hassana3329

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W )YACE”WANDA YA KASANCE A ZUCIYAR SA AKWAI KWATANKWACIN KOMAYYA (ZARRA)NA GIRMAN KAI BAZAI SHIGA ALJANNA BA”

ABINDA AKE CEWA GIRMAN KAI SHINE TURE GASKIYA DA K’IN KARB’ANTA BAYAN MUTANE SUN SANTA,DA WULAK’ANTA MUTANE

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH( S A W)YACE ” DUK WANDA YACE “SUBHANALLAHIL AZEEM WABI HAMDIHI”ZA’A SHUKA MASA BISHIYAR DABINO A GIDAN ALJANNA

***Ko kad’an banyi niyyar amsa kiran ba saboda bancika d’aga kiran da ban San Numba ba ……sai dai nasamu kaina da son d’aga wayar a dai dai wannan lokaci …..bada b’ata lokaci ba kuwa na d’aga tare da karata a kunnena nayi cikakkiyar sallama ta addinin musulunci.

Daga can b’angaren aka amsamin sallamata tare da cewa “dafatan ina magana da HASSANA ne …. !? Jin muryar mace yasa nasamu nitsuwar amsawa sosai a hankali nace ” eh itace …dawa nake magana …!?

       Maman sageer ce "aka amsamin ......nayi wal da ido da girmamawa tamkar ina gabanta nace " mamma barka da Safiya ,antashi lafiya ...!?lafiya lau daughter ya mutan gida da Hussainanki da yaro me wayo ....!?ta amsa da karsashi a muryarta .

Na juya na kalli sisina da taketa sharar bacci batasan me nake ba nace “gata tana bacci …..nima wayar ce ta tadani yanzu …..kowa yana lafiya ” mamma tace “ayya sorry na tasheki a bacci ko ….!?wallahi nakasa jurewa ne dake na kwana a raina ……My daughter don Allah ina Neman alfarma a gareki gameda Muhammad sageer ……had’uwata dake da yadda komai ya wanzu akan idona jiya na tabbatar da zaki iya taimakona …kuma zaki iya taimakawa sageer yafita daga rayuwar da yasaka kansa ciki …….sageer ba haka yake ba …..sageer yaro ne nagari …..sageer yanada hankali da tunani …..ba komai yasashi a wannan hali ba illah wata k’addara da ta gifta ..Wanda kuma nice SANADIN TA …..karkiga laifin sageer akan dukkan abinda yake aikatawa ….duk da bakisan komai ba amma inason kid’ora laifin a kaina ……idan zai yuwu inason mu had’u ni dake domin nabaki labarinmu da k’addarar da tasaka sageer a wannan yanayi ……”

Hassana tana sauraren mamma kanta na d’aurewa ….tunani take a ranta wane irin laifi mamma tayiwa sageer da har yafad’a wannan halin …..!?meyasa sageer yake ganin mata ba mutanen kirki bane …!?meyasa yake gudun mahaifiyarsa kamar mutuwar sa …..!?menene acikin labarinsu ….!?duk wad’annan amsoshin suna gurin mamma itace zata warware komai ……”cikin ladabi Hassana tace “idan har kin aminta dani kibani labarinku ta Yaya ni zank’i amincewa na saurareki …..!?wallahi mamma na d’aukeki da daraja ,zan tsaya na saurari dukkan abinda zakizo dashi kodan samun maslaha …..wani Abu da baki saniba mamma tun randa nafara ganin Hamma sageer najishi a zuciyana tamakar jinina ….naji ina k’yamatar abinda yakeyi da burin ya daina …..gani d’aya nayi masa nasan mutumin kirki ne k’ila halin rayuwa ne yajefa shi a wannan halin ……mamma na amince ….ko yau kika shirya ni mai sauraronki ce ……kuma zan bada gudummawa wajen ganin komai ya dai dai ta insha Allah “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button