HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

K’arfe 11 na safiya jirginsu zai tashi daga GOMBE INTERNATIONAL AIRPORT zuwa filin jirgin babban birnin tarayya Abuja ,tafiyar ba me tsawo bace tunda ajirgi ne ,baifi suyi minti 45 zuwa one hour ba .

Tun bayan sallar Asuba babu Wanda yakoma barci agidan ,Babangida da kansa ya dafawa Hussaina ruwan wanka ya kai mata toilet ,wankan ma kusan ummace tayi mata saboda jikinta babu k’arfi ,ga azababben ciwon kai da zazzab’i da take fama dashi ,kafin su fito har Babangida ya d’akko mata kayan sawa da kayan shafe shafe ya ajiye mata ya fita ,sanda yadawo d’akin har Umma ta temakamata wajen samata kaya da D’an mulka lotion da body spray sai humra me tsananin k’amshi da ratsa jiki,tana zaune gefen katifa babu kwalliyar komai a fuskarta idanu duk ajeme ,tayi rama matuk’a kamar wadda ta had’iyi allura ,ayanzunma wani kukan takeson yi amma Umma nata tausarta da bata baki,Babangida yaje gabanta ya tsuguna yace “sister yanaga bakiyi kwalliya ba …!?haka zaki tafi abujan fuska a kod’e …!?ta d’an rausayar da kanta idanunta nacikowa tace ” kwalliyar lafiya Babangida ….nidai banaso kabarni haka kawai ….”ya girgiza kai yace “ah ah sister ,ai ko D’an kwalli da janbaki sai kin saka …barima kigani nizam miki kwalliyar da kaina ” ya mik’e yaje ya tarkato kayan kwalliyar yazube gabanta ,yana k’ok’arin bud’e powder ta rik’o hannunsa tana girgiza kai tace “don Allah Babangida kabari banaso ” sai Usman yamatso ya jingina da jikinta yace “kibari yayimiki Adda Hussaina ,Yaya Babangida inka Shafa mata powder da kwalli nikuma zan Shafa mata janbaki kaji….” Kafin ma tayi wani yunk’uri tuni Babangida yafara shafe mata fuska da powder ,tanaji tana gani haka ya gyara mata fuska tsaf harda gyaran gira tamkar wani mace,shikuma Usman yashafa mata jambaki lips d’inta suka d’auki shek’i da walwali ,nan da nan fuskarta tayi kyau sai d’an kumburi na kukan da takesha ,Dan ko alokacin ma hawayene ke k’ok’arin zubowa .

Gabanta ba k'aramin fad'uwa yayiba jin muryar Hamma Sageer shida ya safwan da Ya Abdurrahman suna sallama a k'ofar d'akin ,sunzo fita da kayayyakinta domin sawa a mota ,Hamma sageer cikin shigar shadda Ash colour me maik'o da walwali anmata aiki da wani bak'in zare irin d'inkin matasan samari masuji da kyau da had'uwa ,hular kansa tayi matching da kayansa ,sai glass a idanunsu shida Ya Abdurrahman saboda sub'oye asiran idanunsu ,yayi masifar kyawu sai k'amshi yake zubawa .

Suna shigowa Usman yamik’e yayi gun Hamma Sageer yanaimasa oyoyo ,sannan ya zarce da fad’in “Hamma Sageer kaga yadda mukayiwa amaryanka kwalliya nida Yaya Babangida ,kalleta kagani tayi kyau ko …!?kallo d’aya sageer yayimata ya kautar da kansa k’irjinsa na bugawa ,wannan yarinyar bazata barshi yahuta ba saboda fuskarta tana tuno masa da sweetyn sa, sai ya Shafa kan Usman a hankali yace “tayi kyau k’anina ” Usman yayi tsalle yace “yeeee ,ya safwan kawo wayarka muyi selfy da Adda Hussaina ” safwan yace “wayata na d’aki na jonata a chargy ….” Sai Usman ya kalli Abdurrahman dake k’ok’arin zama kan kujera yace “Ya Abdurrahman bamu taka wayar Na d’auki Adda Hussaina hoto …” Abdurrahman yad’anyi murmushi ya kanne idanu yace “ayya usmanu nabarta agida garin Sauri,kawai karb’i ta Sageer kayimata jiya yasayi sabuwar waya me kyau ma kuwa ” Hamma Sageer ya harari Abdurrahman saboda yasan tarko ya had’amasa shiyasa yace yabada wayarsa ,badan yasoba ya zaro wayar yabawa usman saboda kar Usman d’in yaga ya hanashi .

Da gudu Usman yanufi Babangida yana mik’amasa wayar yace “yaya Babangida gashi kad’aukemu hoto ..” Babangida ya karb’a Usman yayi sauri yaje ya lafe jikin Hussaina Babangida ya d’aukesu ,sunyi kyau duk da hawayen da Hussainar takeyi ,Babangida ma yabawa safwan wayar yazauna aka d’aukesu shida Usman da Hussaina, shima safwan d’in ya zauna Babangida ya d’aukesu ,Ya Abdurrahman yak’i zuwa ayi dashi yace shi baya hoto dame kuka ,tunda kuka takeyi bazaiyi hoto da itaba ,sannan yace “Ango dai yakamata yashiga ayimusu shida amaryansa ,ko ba hakaba Usman ….!?Usman yayi dariya yana kama hannun Sageer yace ” hakane Ya Abdurrahman ,Hamma Sageer taso ayimuku kaida Adda Hussaina,” wani haushin Abdul Yakama Sageer ,haka kawai sai b’allo masa ruwa yakeyi ,mazewa yayi ya kalli Usman yana D’an murmushi yace “banayin hoto Usman ” sai Usman d’in yace “Ayya Hamma Sageer da fa ina ganin hotonka a wayar Adda Hassana ” ambatar sunan marigayiya sweetynsa yasashi lumshe idanu zuciyarsa na bugawa ,ya sauke ajiyar zuciya zaiyi magana aka d’aga labulen d’akin da sallama aka shigo ,Hamma Sulaiman da Hamma Aminu suka bayyana cikin shigar manyan kaya da suka fito da kyawun zatinsu ,Hussaina kamar jira takeyi tamik’e dagudu tafad’a k’irjin sulaiman tafashe da wani gigitaccen kuka ,ya tarbeta ya rungumeta ,yad’ago kanta yana share mata hawaye yace “idan kina kuka zaki samu a tashin hankali ,zaki tafi kibarmu cikin zullumi da tunani ,kuma zanta tuhumar kaina akan nakasa rik’e amanar da aka dank’amin ” tak’ara kwantar da kanta a kafad’arsa adai dai lokacin da Baba yashigo yana fad’in “me kuka tsaya yine ?kufito Ku wuce filin jirgin karku makara …yanzunfa goma takusa cika ….” Tanajin haka takuma rushewa da kuka ta fizge jikinta daga jikin Hamma Sulaiman tayi d’akin Umma da gudu ,tana zuwa tafad’a kan ummansu tanata kuka,itama Umman dauriya kawai takeyi ,haka ta rungume d’iyarta tarad’a mata akunnenta cewa”duk abinda zan fad’amiki nagayamiki shi tun jiya da daddare,abinda zan maimaita mini shine ,kiyi biyayyar aure,kuma karki manta da Hassanarki cikin dukkan addu’o’inki ,tashi kutafi Allah yatsare hanya …Allah yayimiki albarka “Umma takamota tafito da ita ta dank’ata a hannun Hamma Sulaiman da suka firfito tsakar gida ,Babangida yad’auko hijab d’inta yasamata ajikinta ,yanata daurewa amma baisan lokacin da kukan ya kufce masaba ya rungumeta yafashe da kuka ,Usman ma Yakama kuka shida safwan ,Abdurrahman da Aminu hawaye yacika idanunsu ,Hamma Sulaiman ya runtse idanuwansa yana dafe Kansa,dukkansu Hassana suke tunawa ,mutuwa tadawo musu d’anya shakaf sukaita kuka suna zubda hawaye ????,Hussaina na k’wala kiran Hassanarta kamar tayi hauka ????,ta tada hankalin kowa musamman Sageer da ya durk’ushe k’asa yana tsiyayar hawaye???? yanajin zuciyarsa tamkar tafad’o k’asa ,Baba ne yashare k’wallarsa sannan yayita rarrashinsu da nasiha iri iri ,yaje yad’ago Sageer ya rik’e hannunsa yace ” Kaine babba agareta ,kadena yawan kuka hakan zaisa itama tarage NATA kukan ,amma muddin hawayenka zai dinga zuba to itama Natan ba zai tsaya ba Sageer …Ku wuce muje kukan ya isa haka ,Hassana addu’a take so ba kuka ba ,kuma nasan tana farinciki daku tunda kuncika mata burinta ,Abu d’aya yarage ga junanku shine kuyi hak’uri Ku zauna da junanku lafiya Ku tallafi junanku ,duk Wanda ya cutar da wani acikinku to Allah yana ganinku …kuma akwai hisabi tsakani mata da miji ranar lahira ….”yana gama fad’in haka yaja Hannun Sageer yayi gaba ,yace da Hamma Sulaiman ya fitoda Hussaina,Aminu da Abdul da safwan suka d’akko jakunkunan suka biyosu dasu,aka bar Babangida da Usman jikin Umma sunata kuka ,yayinda Hussaina ke d’aga musu hannu tanai musu by by tana kallon mahaifiyar ta tanajin tamkar bazata sake ganinta ba …….tanaji tana gani aka fitarda ita daga gidan mahaifinta zuwa Sabon gurin da zata sake rayuwa ….wata bahaguwar rayuwa wadda babu Hassanarta a cikinta ….kewa da rauni suka mamaye zuciyarta ,kamar ta suma haka ta rik’e Wuyan Hamma Sulaiman kanta na langab’ewa a k’irjinsa ???? …….!

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button