HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Barcinta baiyi wani nisaba suka sauka a babban birnin tarayya Abuja ,da misalin k’arfe 12 na ranar juma’a ,bayan jirgin ya tsaya sai yarasa yadda zaiyi ya tasheta daga jikinsa da alamun baccin yanai mata dad’i tunda bawani bacci take samuba sai yawan tunani da kuka,yana ganin mutane nafita ammashi yana zaune duk tawani danneshi sai ajiyar zuciyar kuka take sauke masa a k’irjinsa ,yad’an d’ago jikinsa da niyyar tada ita yana k’ok’arin tallafe bayanta ,tad’an motsa tana bud’e idanunta a hankali sai kuma tak’ara lumshesu tatafi luuuu zatakoma k’irjinsa tacigaba da bacci da alamun baccin bai isheta ba kuma ta manta jikin wa take,da wani irin hanzari ya cafki kafad’unta da hannuwa biyu ya rik’e yad’an girgizata yace “kehhhhhhhh” saita fara bud’e idanunta a hankali harta sauke ganinta akan fuskarsa ….tsigar jikinsa tayi bala’in tashi saboda yadda idanunta sukayi wani irin shanyewa cikeda bacci gashi sun kad’a sunyi wani irin ja ,yace “ki hak’ura da barcinnan haka min iso Abuja …ko haka zamuyita zama acikin jirgi kowa yafita ya barmu …..!?duk kinwani sakarmin nauyinki kin danneni kina bacci ” mtswww ,yaja k’aramin tsaki yana sakin kafad’unta yad’an tureta daga jikinsa yamik’e tsaye,tuni ta wartsake idanunta na k’ok’arin cikowa da hawaye ,haushin kanta yakamata Dan batasan lokacin da tayi barcin a jikinsa ba ma,tilas haka tamik’e tana k’ok’arin binsa a baya har suma suka sakko daga cikin flight d’in …..

Bayan yagamayi musu komai sun d’ebi kayansu ,sai yazaro phone d’insa yakira number hotel d’in da zasu sauka yanaso aturo da driver yazo ya d’aukesu ,tana tsugune gaban jakunkunan su takife kanta akai saboda juyawar da kanta yakeyi ga wani amai dayake tasomata ,da wani irin hanzari tamik’e tasa hannu ta danne bakinta tana duru duru saboda aman dab yake da zubowa ,juyowa yayi yazuba mata kyawawan idanunsa yad’an d’age girarsa yana yamutsa fuska yace “kewai lafiyarki kuwa kiketa wani zabure zabure ….” Idanunta a warwaje tabud’e bakinta tace “a…..am……..amaiiiiiiiii……zanyiiiiiiiiii…..” Tana rufe baki aman na yunk’urowa da k’arfinsa ,cikin zafin nama ta tsugune k’asa daga gefe tafara kelayashi tamkar zata amayar da kayan cikinta gabad’aya numfashinta har wani d’aukewa yakeyi hawaye na kwarara a idanunta .

Tsugune shima yake agabanta yana kallon uban aman da take shek’awa ,jikinsa rawa yakeyi saboda tsoratar da yayi ,yarasa taimakon da zai bata illah kallonta da yakeyi kawai har ta kammala ,jikinta duk yasaki babu k’wari ,saita fara k’ok’arin zamewa agurin zata kwanta …….da sauri ya rik’ota yana zaro idanu yace “kehhhhhhh ,mezakiyi hakane ” ta langab’e kanta idanunta na lumlumshewa da k’yar ta fizgo magana cikin haki tace”jiriiiiii….jiriii nakeji ,kwanciya nakeson yi …”hannunsa na rik’eda nata yabud’e baki zaiyi magana sai yaji wata murya tayi sallama akansu ,a hankali yad’ago kansa yana duban………….!

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍


TYPING????

???????? HASSANA ????????

            *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page5⃣7⃣to5⃣8⃣

WATTPAD:hassana3329

® PEN : WRITERS ASSOCIATION


~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

TUNASARWA????

WUTA

KAFIRAI ZASU SHIGETA TARE DA WASU MASU LAIFI CIKIN MUMINAI ,ACIKIN MUTUM DUBU MUTUM 999 NE ZASU SHIGA,TANADA K’OFOFI BAKWAI ,TAFI WUTAR DUNIYA SAU SABA’IN KAFIRAI ZASU K’ARA GIRMA ACIKINTA DOMIN SU D’AND’ANI AZABA ,HAK’ORANSU KUMA KAMAR DUTSEN UHUDU ,ZA’A KAURARA FATARSU AKUMA DINGA CANJA TA DOMIN SU D’AND’ANI AZABA.ABIN SHANSU RUWAN ZAFINE MAI ZAFI YANA TSINKA HANJI,ABINCINSU KUMA ZAKKUM NE DA GISLIN DA MUGUNYA,WANDA YAFISU SAUK’I KUMA SHINE WANDA ZA’A SA GARWASHI A K’ASAN DIGADIGANSA K’WAK’WALWARSA TA DINGA TAFASA,FATARSA TA NARKE TA RUB’E TA SALUB’E ,RAMINTA ZURFI NE DASHI ,DA ZA’A JEFA MUTUM CIKI ZAI KAI SHEKARA SABA’IN BAI KAIBA ,KAFIRAI DA DUWATSU SUNE MAKAMASHINTA ,ISKARTA MAI ZAFICE INUWARTA MA ME ZAFICE ,,TUFAFIN CIKINTA MA NA WUTA NE ,TANA CIN KOMAI BATA BARIN KOMAI ,TANA HAD’IYAR FUSHI TANA K’ARAJI TANA CIMMA K’ASUSUWA DA ZUKATA

ALLAH UBANGIJI KA KAREMU KA TSAREMU DAGA AZABAR WUTA IDAN MUN KOMA GAREKA YA ALLAH ????????????

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W) YACE “NIDA WANDA YAKE D’AUKAR D’AWAINIYAR MARAYA KAMAR HAKA MUKE ,YA HAD’A YATSUNSA GUDA BIYU MANUNIYA DA KUMA D’AN TSAKIYA (WATO YA HAD’ASU GURI GUDA

Innalillahi wa”‘inna ilaihirraji’un ,feedyn bash inai miki ta’aziyya abisa rasuwar kakar ki ,Allah ya jik’anta yayi mata Rahama????????????

BARKANMU DA JUMA’A SISTERS ,ALLAH YABAMU ALBARKACIN WANNAN RANA ME ALBARKA????????????

***D’agowa yayi yana duban inda yaji sallama ,sai yaga wata mace tsaye akansu fuskarta da fara’a tana dubansu hannunta d’auke da robar ruwa ta swan water ,murmushi takuma yimasa sannan tace” sannu ,hala batada lafiya ne …..!?ya kalli Hussaina tanata faman lumshe idanu sannan yadubi matar yace “tun tahowarmu amai yake damunta …so sai yanzun tasamu ya zubo …” Ta D’an tsuguna tana mik’a masa ruwan hannunta tace “ayya amshi ka wanke mata bakinta tun acikin jirgi nalura cewa kamar batajin dad’i… Ina ganin abinda yasata aman ko laulayi takeyi …!?yad’an tsurawa matar idanu yana juya idanu da kai ,to aishi baima san menene laulayin da ta ambata ba ,shiyasa yace ” laulayi kuma …!?menene laulayi ….!?matar tayi dariya tace “ba matarka bace …!?ya d’anyi shiru saboda shi har yanzun bai San awane matsayi Hussainan take ba ,da taga yayi shiru sai tace” ina nufin ko ciki ne da ita shine yasata laulayi har take amai …!?

    Ba Hamma Sageer ba Hatta Hussaina saida maganar matar taso bata dariya musamman ganin yadda Sageer d'in yayi wuk'i wuk'i da idanu ,suna had'a idanu da Hussaina ya galla mata harara yana k'ok'arin bud'e murfin robar ruwan hannunsa ,matar ta mik'e tana cewa "toh sai anjimanku Allah yak'ara sauk'i ya raba lafiya ....duk da ban sanku ba hakanan naji kun burgeni" tana gama fad'in haka tayi gaba tana murmushi .

Da kansa ya d’auraye mata bakinta ,adai dai lokacin da motar hotel d’in ta k’araso inda suke, drivern yafito yana gaida Hamma Sageer ,sannan yafara kwasar jakunkunan su yana sawa acikin Boot d’in motar, Hamma Sageer yabud’e motar da niyyar shiga ya waiwayo yana kallon Hussaina dake durk’ushe batada niyyar tashi ,ya D’an tsuke fuska yace “malama mutafi mu barki anan ne …!?naga bakida niyyar tashi …” Da k’yar ta yunk’ura ta mik’e tsaye tanajin kanta na juyawa hajijiya na kwasarta ,tafara nufar motar tana tangad’i tamkar takifa ,da hanzari yayi niyyar tareta cikin wata irin murya me kama da fad’a yacemata “na rantse in kika fad’i ke kika jiyo ….ba ruwana ni ..”tilas haka ya rik’e hannunta yasata cikin motar sannan shima yashiga ciki ,driver yaja motar suka tafi .

TRANSCOP HILTON HOTEL suka isa,babban hotel ne me tsada da sai y’ay’an masu kud’i da y’an siyasa ne ke sauka saboda kyawunsa da tsadarsa ,tuni daman kafin su iso Mamma tayi musu booking saboda intazo abuja anan take sauka daman ,yana fitowa daga motar itama tafito tanata cukuikuye hijabinta ajikinta saboda zazzab’in da yakeson kamata ,wani sanyi sanyi takeji yana shiga jikinta idanuwanta duk sun sauya kala ,a hankali takebin bayansa cikin Jan k’afafu har suka isa reception d’in hotel d’in ,anan ya karb’i mukullin d’akin da suka kama ,ma’aikatan hotel d’in guda biyu aka sa suka d’ebo musu kayansu a boot ,suna gaba Hamma Sageer na binsu abaya shida Hussaina har zuwa d’akin ,ma’aikaci d’aya ya karb’i key d’in yabud’e d’akin suka shiga da kayan ,Hamma Sageer yabisu abaya har ciki yana shiga wani sanyi da k’amshi suka doki hancinsa ya lumshe idanu yanajin inama tare da sweetyn sa yake, suka ajiye kayan sukai masa sallama da tambayar ko akwai abinda suke buk’ata ,yace babu amma inyana buk’atar wani Abu zaiyi magana ,fitowa sukayi daga d’akin suka sauka k’asan benen .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button