HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Good bless u “thank u my daughter ” mamma ta ambata da tsananin farinciki …… Sannan taci gaba “idan babu damuwa zanzo har gidanku yau …..Dan na gaisa da ummanku …sonake mu zama d’aya ….zamuzo tare da Nafeesa ……dafatan babu wata matsala …..!?

“Babu kam ….Umma zata karb’i bak’untarki …..matsalar d’aya ina zuwa islamiyya ….ba lallai kisameni yau ba mamma “Cewar Hassana duk da akwai tantamar zuwan mamma d’in a ranta…..”

Cikin murmushi mamma tace”

“Nasan ba zai wuce da azahar kuke tafiya bako ….!?zanyi k’ok’arin zuwa kafin tym d’in …..bari na barki haka ….nagode my daughter sai nazo “

Kafin Hassana tayi magana mamma ta katse wayar ……jikin Hassana a sanyaye ta ajiye tata wayar da tunani fal a ranta …..sai yanzu tsoro ya kamata …..yanzu idan mamma tazo aka tsareta akan menene alak’arsu me zatace …..!?ko da yake Allah yaga zuciyarta zai taimaketa akan hakan ……ita bata bata gama saka ran mamma d’in zatazo bama….


Bari muji tarihin wad’annan Ahalin kafin mu d’ora

*Malam Abubakar haifaffen garin gombe ne kuma bafulatani usul ,ya taso maraya babu uwa babu Uba ,a hannun k’anin mahaifinsa ,inda yana d’an shekara takwas shima kawun nasa ya rasu ,aka rasa wanene zai d’aukeshi cikin dangi sai Aminin mahaifinsa Malam sulaiman ,Wanda akewa lak’abi da Malam dattijo saboda dattijantakarsa da iya mu’amalar sa ,kuma gashi babban malami me karantar da alk’ur’ani .

     A gurin Malam dattijo Abubakar yayi karatu har zuwa sanda ya sauke alk'ur'ani me girma ,sannan yayi cikakkiyar hadda ,yasamu tarbiyya a gun Malam dattijo sosai inda ya rik'eshi tamkar d'an da ya Haifa da cikinsa ,kasancewar Allah bai bashi haihuwar d'a namiji ba sai dai ya haifi y'ay'a mata guda biyu ,ta farin me suna fad'imatu ,sannan k'anwarta da ke binta wadda suke da tazara me yawa me suna Aisha .   Duk inda kuke tunanin mutumin kirki to Malam dattijo ya kai ,lokacin da Abubakar ya girma ya kai munzalin fara Sana'a Malam dattijo shine yabawa Abubakar jarin da ya fara saida kayan miya ,ganin cewar Abubakar d'in bashida sha'awar yin kiwo ko noma kamar sauran Fulani ,a sanda ya lura kuma ya kai minzalin aure sai ya wanke babbar d'iyarsa Fad'ima ya aura masa ita....... Abubakar yaji dad'in haka k'warai kasancewar yataso tare da Fad'ima yasan tarbiyyarta da kyawawan halayenta ,ga kyau da Allah ya zuba mata tamkar Aljana .


  Malam dattijo shine yayi komai game da auren da duk wasu hidindimu ,yayinda Abubakar yasamu Fad'ima fiye da inda baya zato wajen yimasa biyayya da bin umarninsa ....Fad'ima macece tagari meson farantawa mijinta rai .....kullum burinta tasaka mijinta walwala da annashuwa .   Bayan bikinsu babu dad'ewa ne wata rana da bazasu tab'a mantawa ba ta riskesu .....lokacin Aisha tana gidan Abubakar da Fad'ima tana hutun Makaranta da aka bayar .....da daddare aka kawo wutar nefa me tsananin k'arfi inda k'wan d'akin Malam dattijo da mahaifiyar su Fad'ima yayi bindiga ....gobara ta tashi a gidan ...komai saida ya k'one har Malam da matarsa .....saboda tsakar dare ne ba'ayi nasarar kashe wutar da wuri ba .....tashin hankalin da Abubakar da Fad'ima da Aisha suka shiga yanada yawa ....sunyi kuka matuk'a kafin su hak'ura su fawwalawa Allah komai .....sosai Abubakar yaji wannan mutuwa a jikinsa ta yadda lokaci d'aya ya zabge sai Fad'ima ce me k'arfin halin rarrashinsa .

Bayan share makoki ne dangin Malam sukaso d’aukar Aisha ,nan fa Abubakar yace bai San wannan ba babu me d’aukar Aisha ,sune suka cancanta su rik’eta ….babu wani ja’inja aka yadda aka barmusu Aisha a hannunsu yaci gaba da kulawa da Fad’ima matarsa da kuma k’anwarta Aisha .

Aisha ta kasance mace me son karatun boko, burinta tazama likita idan ta girma ,ganin yawan burinta akan haka sai Malam Abubakar yasaka d’anba da k’ok’arin ganin tasamu cikar burinta …ya tsaya mata sosai akan karatunta ….Alokacin ne Fad’ima tayi haihuwar fari… Ta haifi y’a mace …ran suna yarinya taci suna Nabeela ……murna sosai Aisha takeyi da wannan haihuwar …itace takewa Nabeela komai …..k’aunarta takeyi ba da wasa ba .

Sanda Aisha tayi candy Malam Abubakar ne yadinga cuku cukun yadda zata samu admission a jami’a …cikin ikon Allah kuwa ta samu ….karatu sosai ta duk’ufa babu wasa ….ganin hakan wani lecturer d’insu me suna sir Aliyu yake matuk’ar k’aunarta …..soyayya yakeso suyi wadda zata kaisu ga aure ….sosai Aisha take gudunsa ganin ba sa’anta bane shid’in d’an gidan masu kud’ine itakuwa talaka ce batada kowa sai yayarta da Malam Abubakar Wanda ta sauyawa suna da Baba….Alokacin Fad’ima takuma haihuwar d’anta na biyu ….kyakkyawan yaro sulaiman kenan Wanda yaci sunan Malam dattijo …..

Sir Aliyu ya matsawa Aisha da son aurenta ….tun bataso har tazo ta amince masa ta fara sonsa da gaske itama …..ya nuna yanason ayi bikinsu sai taci gaba da karatu a d’akinta …..hakan kuwa akayi nan da nan manya suka Shiga lamarin akayi komai aka gama …..dangin Aliyu basu k’yamaci Aisha ba sun nuna mata kulawa da soyayya suma….. Sanda Fad’ima ta haifi d’anta na uku Aminullah alokacin Aisha Nada cikin fari ….babu dad’ewa itama ta haifi d’anta namiji inda yaci suna Abdurrahman (shine me son Hussaina a yanzu ) daganan ne kuma suka d’an samu hutun haihuwa nawasu d’an shekaru saikuma Allah yabasu ciki lokaci guda ….dan tsiran haihuwarsu kwana ukune kacal ….Fad’ima ta kuma haifar namiji yaci suna safwan ….sai kuma Aisha ta haifi mace Halimatus Sadiya wadda takasance matar Hamma Aminu a halin yanzu (Amsad kenan) daganan nefa haihuwa ta tsayawa Aisha bata kumayi ba ….sai kawai tasaka karatunta a gaba da kulawa da mijinta da yaranta …..ita kuma Fad’ima (Umma)ta kuma haifar y’an biyu (kyautar Allah)yaran da sukazo da farinjini da albarka iri iri ….kyawawa masu shiga ran mutane …kowa k’aunarsu yakeyi …..daga Kansu ne Umma ta haifi Abubakar (Babangida)sai kuma Usman (autan Umma).

Wad’anna Ahali sun taso cikin k’aunar juna da d’orewar zaman lafiya ….Malam Abubakar sosai yake kulawa da iyalensa da taimakon Aisha ….domin tagama karatunta tasamu aiki a wani privet hospital me suna (savannah hospital)dake garin gombe …..sosai take taimakon sa akan abubuwa da dama…. Aisha itace takai Baba da Umma aikin hajji suka sauke farali .

Izuwa yanzu yaransu duk sun girma wasu sunyi aure…. Kamar Adda Nabeela da ke auren me kud’i itama Wanda ya kasance cousin d’in Aliyun Aisha …a yanzu tana gidanta da yaranta guda hud’u duk maza Auwal ,Sani ,Salisu ,Rabi’u ,…… Adda Nabeela ta kasance mai yawan fara’a da son k’annenta .

Sai Hamma sulaiman Wanda ya kasance miskili Mara yawan son magana …..mai kishin iyayensa da son ahalinsa suji dad’i….. Hamma sulaiman ya auri sakeena wadda take tsananin sonsa…. Class mate d’insa ce a school ….sakeena ita tafara furtawa sulaiman Kalmar so …..inda tayi amfani da wani hadisin manzan Allah S A W ,wani mutum ne yazo wajen Annabi yace “ya manzan Allah inason wane ….sai manzan Allah yace ” ka sanar dashi kana sonsa….. Sai wannan mutum yasamu Wanda yakeso ya sanardashi Cewar yana sonsa…..sai mutumin yayi murna yace “kaima Allah ya soka kamar yadda ka soni “……..da wannan had isin tayi amfani wajen fad’awa sulaiman tana k’aunarsa …..Hamma sulaiman ba gwanin kula y’ammata ba duk da yadda y’ammatan ke rububinsa tamkar su cinyeshi ….kuma duk cikinsu yafijin sakeena a ransa ,shiyasa ya tsayar da ita a matsayin matar aurensa,mahaifinsa sakeena me kud’ine sosai ….yanzu haka sulaiman a k’ark’ashinsa yake aiki … Kuma sosai yake bud’awa sulaiman saboda hankalinsa da gaskiya da rik’on amanarsa …..a yanzu Hamma sulaiman yanada y’ay’a guda uku tsakaninsa da sakeena ….Abubakar( sadauki) shine babba sai kuma Maryam da Zainab ..

Hamma Aminu me yawan fara’a da son kyautatawa ahalinsa , ya auri Sadiya d’iyar goggo Aisha bayan soyayya da suka tafka tamkar a cinye juna ….Aminu yana son Sadiya sosai kamar yadda itama take bala’in sonsa…..basu dad’e da aure ba domin haihuwarsu d’aya mace me suna Fad’ima (zuhuriyya).

*Sai safwan da yakusa kammala karatunsa yanzu ….yaro d’an k’walisa da son burgewa ….safwan akwai son gayu da k’yale k’yale ….shiyasa ko a school farinjini ne dashi gurin samari da y’ammata.

HASSANA da Hussaina y’ammata adon gari…. Masu kama da juna da tsananin k’aunar juna ….y’an biyu kyautar Allah ….wad’anda suka tashi cikin farinjini da kyakkyawar tarbiyya …masu sowa junansu abinda kowacce take so …..amma sun bambanta ta wajen k’aunar Abu d’aya wato SAGEER …

Sai Babangida da Usman sarakan tsokana da Sanya nishad’i a gidan …..sosai sukeson y’an uwansu da iyayensu..burinsu bai wuce su gansu tare da suba …

A yanzu Malam Abubakar yana zaune da iyalansa a unguwar Herwagana ….unguwace da ta had’a masu kud’i da masu k’aramin k’arfi ……hakanan acikin unguwar makarantar bokon su Hassana take…..wadda batada nisa da gidansu.

Wannan shine kad’an daga tarihin wannan ahalin.


Hassana zaune a tsakar gida kan kujera Y’ar tsuguno tana wanke wanke ,yayinda Hussaina ke gefenta tana d’auraye kwanukan da ta wanke d’in …..lokacin k’arfe sha biyu saura mintuna na rana ….yayinda Umma ke zaune a falonta itada Usman yana tayata gyara zogalen da zasuyi Dambu dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button