HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

 Kafin ya k'arasa ma tuni sunyi waje da gudu sun nufi d'akinsu ....ragowar ahalin gidan sunata dariya harda Baba da Umma ...safwan yana dariya yace "ai wallahi Hamma idan mutum yashiga fad'an yaran nan kunya yakeji ...k'iri k'iri sai su b'atar da kai " Babangida yace "ni zan baka labari ya safwan nida rannan nashiga fad'ansu suka kunyatani a gaban abokaina ...Usman na dariya yace " nagane ranar ya Babangida ...ranar da ka kusa kuka ko...!?wata harara Babangida ya zabgawa Usman yace "ba'asaniba ...na rantse Umma kishiga tsakanina da autanki fa ....wani kallo Hamma sulaiman yayiwa Babangida yace " kai tashi ka fita... Kaima bisu ..."yana nuna masa hanyar fita ...sum sum yamik'e yayi waje yana cin alwashin sai Usman yasha mintsini.

“Baba ne yace “ayi hak’uri sulaiman naga yau fad’a kakeji ……kar agama dasu muma agano namu laifin…!?da murmushi yake fad’in hakan ..harda duban umma dake zaune tana sauraren abinda ke faruwa amma bata tanka ba yace ” kar muma agano laifin mu ko ummansu …!?Umma tace “aikuwa dai Dan naga Asama yau yake” kunya takama Hamma sulaiman ya sunkuyar da kai yana murmushi yace”haba Baba ….!

   Aminu na dariya yace "to ai gaskiya ne Hamman mu...yau kanata fad'a waye ya tab'o mana Kaine ....!?ko da yake kana zuwa gida sakeena zata rarrasar mana kai ..." Hamma yayiwa Hamma Aminu kallon gefen ido sannan ya d'auke kansa gefe yana fad'in"yaseen bakada kunya Aminu ...ka manta agaban su Baba kake ne ...!?

Sunkuyar da kai Hamma Aminu yayi yana y’ar dariya da Shafa kai yace”Baba ayi hak’uri “Baban baice komaiba banda murmushi ,sai Umma ce tace” Allah ya shiryeka Aminullahi “itama da murmushin akan fuskarta.

 A can kuma y'an biyun suna Shiga d'akin su Hussaina takuma turb'une fuska tana wani basarwa ....sannan tadubi Hassana a d'age tace" waida nufinki zaki gayawa Hamma abinda yasa nake fushi dake ne ...!?Hassana ta langab'e kai tace "to ya zanyi sisina ...wallahi banason naga kina fushi dani..gashi naga Hamma na k'ok'arin d'aura miki laifin ...shiyasa nake k'ok'arin kareki nikuma" saida Hussaina ta k'arewa Hassana kallo sannan ta numfasa ta dafa kafad'ar Hassana tace "kinyi min laifi da yawa Rabin raina ...don Allah kifita harkar mutumin nan wallahi bana sonsa" wani Abu yasoki zuciyar Hassana sosai ta d'an runtse idanunta a hankali ta bud'e bakinta da niyyar magana sukaji an kwad'a sallama .

Kan Hassana ta Ankara wuf Hussaina tamik’e da gudunta tayi tsakar gida tana fad’in “oyoyo ya Abdulrahman d’ina” kamar ya rungumeta shima ya bud’e hannayensa cikin k’aramar muryarsa da sassanyar dariyarsa yake fad’in “oyoyo Tawan nayi missing d’inki “sai kuma Hussaina tajuya bayanta tana b’ata fuska alamar tayi fushi …da Sauri Yakuma zagayowa gabanta ya d’auko wayarsa a aljihun jeans d’in jikinsa, ya haske fuskarta saboda tsakar gidan babu wadatar haske sosai ,ganin yadda ta b’ata rai yasashi marairaicewa yanacewa” haba Y’ar rigimata …kirufamin asiri kar fushinki ya makantar da idanuna…nafison ganin murmushinki fiye da komai kinsani…ki bari kiji uzurina karki hukuntani da fushinki …”cikin rad’a rad’a yakemata magana ta yadda baza’a jiyosu ba …ita kuma sai mak’e kafad’a take tana cuno baki da kyawawan lips d’inta masu taushi…alokacin Abdulrahman jiyake da sunada aure babu abinda zai hanashi morar bakinta saboda yadda yake fizgarsa …bai iya Barin abin a zuciyarsa ba saida ya furta cewa”na rantse kidena turomin baki…kinji yadda jikina ke rawa idan na Ganshi haka kuwa…!?a hanzarce Hussaina tasa hannayenta tarufe bakinta tana dariya k’asa k’asa …shikuwa ai sai ya langab’e kansa ya zuba mata idanu yanajin sonta na k’aruwa a ruhinsa…ya kasa had’iye shauk’in saida ya bayyanar dashi a fili wajen fad’in “wallahi ina sonki Y’ar uwata …Allah yabarni dake tawan”

Fitowar su Hamma sulaiman da Aminu daga d’akin Baba yasa Abdulrahman waigawa yana Shafa kansa…cikin y’ar inda inda yace”Hamman mu Ashe kuna ciki …!?nima shigowa na kenan ta tsareni ta hanani Shiga ciki …”zaro ido Hussaina tayi jin abinda yace ,yanaso ya k’aramata laifi a gun Hamma bayan Wanda ake tuhumarta dashi yanzu …Hamma Aminu ke dariya yana cewa “mu bamu tambayeka ba Abdulrahman…tsakaninku ne wannan kunfi kusa …” Shikuwa Hamma sulaiman duk’awa yayi yana saka takalmansa sauciki a k’afafunsa ,yana d’agowa sukayi ido biyu da Hussaina sai zazzare ido takeyi …ya d’an harareta kad’an yana fad’in “bar nan ” da hanzarinta kuwa tajuya d’akinsu a zuciyarta tana fad’in”shifa Hamma wani lokacin yacika masifa …wai Aunty sakeena na fama..Allah dai ya yaye masa.

  Abdulrahman yabita da kallo yana murmushi ,yasan cewar antab'o Y'ar rigimarsa zaisha lallashi. Ya gaisa da su Hamma ,sukayi waje Dan tafiya gidajensu ,....shikuma ya nufi d'akin Baba yana fad'in "bari naje na kwashi gaisuwa gun Baba da Umma...Hamman mu Ku gaida gida da iyalan Baki d'aya.."

A wannan daran ne kuma Hassana tasamu nasarar bawa Umman su da sisinta labarin su mamma kaf…takuma nemi shawarar su akan me yakamata tayi …!?labarin ya firgita Umma sosai ,kuma tajishi a jikinta sosai ,anan take bawa Hassana shawara da k’arfafa mata gwiwa a matsayin ta na uwa agareta …akan ta yarda takuma amince akan ta taimaki sageer , tasan dabarun da zatayi wajen fitar dashi daga halinda yake ciki ta hanyar fasaha da naseeha da kuma addu’a ..ka na ta gargad’eta akan itad’in mace ce yakamata ta tsare mutuncinta da imaninta har zuwa sanda hak’ansu zai cimma ruwa …”Hassana taji dad’in maganar ummansu sosai da sosai ,tayiwa Umma addu’ar bazata bata kunya ba insha Allahu ….Hussaina kam kamar yadda Umma taji labarin ya ratsa jikinta itama taji hakan sosai …sai dai bambancin bataji tausayin sageer a ranta ba ko kad’an …illah ma bak’insa da takuma gani akan biyewa faruk da yayi harya fad’a halaka …a ganinta baiyi tawakkali da d’aukar k’addara ba …kamata yayi alokacin yarik’i addu’a sai damuwarsa ta yaye ba wai ya rik’i shaye shaye a matsayin maganin damuwar saba ….kuma har a lokacin bataji a zuciyarta zatabawa Rabin ranta goyon bayan Shiga rayuwar sageer ba .


Kwanaki sun wuce har zuwa ranar alhamis Hassana batasa sageer a idanunta ba …ko Makaranta zasuje har suje su dawo bata ganinsa …tarasa meyasa yadena zaman wannan dakalin ,sosai take tunaninsa da kewarsa a zuciyarta ,duk cikin damuwa take jinta… Ganin sageer kawai takeson yi da idanuwanta da zuciyarta ,yayinda Hussaina ta kasance cikin farincikin hakan …addu’a takeyi akan Allah yasa sageer d’inma yabar unguwar ta yadda Hassana zata dena ganinsa kwata kwata.

 Toh kuma k'arfe hud'u da y'an mintuna na yammar ranar Alhamis d'in wayarta tayi k'ara ,tana dubawa ta iske Ashe sak'one daga Aunty Nafeesa tana rok'on tazo gidanta tana nemanta yanzu ,alokacin tana zaune sisinta nayimata kitso a kanta kuma saura biyu a kammala ....saida tajira ta gama mata sannan tamik'e tana karkad'e jikinta ,sosai kitson ya zubo kafad'unta yayi mata kyau ..kasancewar gashinsu me tsawo da laushi ne irin na Fulani ....saida tashiga toilet tad'an k'ara gyara jikinta, tafito ta sauya kayan jikinta ta gyara fuskarta da kwalliya dai dai gwargwado ,sannan tazura hijabinta ta dubi sisinta da ta zura mata ido tana kallonta kurum tace "sisina Aunty Nafeesa ce ke nemana ...zanje nanemi izinin Umma naje ..ko zaki rakani please ...!?wani takaici Yakama Hussaina da k'yar tabud'e baki tace" bazani ba ...agaida nagaba "sai jikin Hassana Yakuma sanyi ..yanzu Ashe duk da labarin sageer da Hussaina taji bata sauya ra'ayinta akansa ba ...!?mik'ewar Hussaina da shigewarta toilet shine yabawa Hassana damar girgiza kanta ta nufi d'akin Umma tana murmushi .
  Umma tabata izinin zuwa ,amma da gargad'in karta dad'e ,Hassana ta buk'aci ina Usman ya rakata ,Umma tace" ya tafi ya mik'amin markad'e ..blander ta tak'iyi ina zaton k'onewa tayi "tilas haka Hassana tafice ita kad'ai ba tare da D'AN Rakiya ba .  Tana tura k'ofar get d'in gidan Aunty Nafeesan a bud'e yake.... Sanya k'afar ta ciki wani mugun k'amshin turare me dad'i ya daki hancinta..kafin tagama shak'a kuma warin sigari ya kuma Dakar ta .

Yana zaune akan farar kujera a harabar gidan …yana sanye da wata riga dark blue me gashi gashi a jikinta da jeans milk colour ,bata tab’a ganin yayi mata kyau irin ranar ba …gabansa tebur ne fari, an d’ora juice da cup a kai …sai wayoyinsa da ke kai da kuma kwalin sigari da lighter ….hannunsa kuma d’auke da wata sigarin yanasha.

K’arar bud’e get d’in ce tasashi duban gurin Dan ganin wanene yashigo …idanunsa sukayi tozali da Hassana … Ita dai Hassana gani kawai tayi ya mik’e a rikice jikinsa na mugun rawa kamar yaga abun tsoro…ya k’ura mata idanu yana wani irin dubanta…sannan yayi hanzarin mayar da hannuwansa bayansa yana b’oye tabar hannunsa wai Dan karta gani.

Yadda yake kallon ta haka take kallonsa zuciyarta na lugude….A hankali tasoma takawa gabansa tana tafiya cikin wani irin taku har tazo dab dashi …sannan taciro hannunta da yasha Jan lalle me k’ayatarwa ta mik’a masa tafin hannun da nufin yabata abinda yake b’oyewa ….sageer yabi hannun da kallo idanunsa na lumshewa ……”

Comments
Share
Vote
Pls

HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

TYPING????

???????? HASSANA ????????

       *DA*

❣???? HUSSAINA ????❣

TARE DA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍

page2⃣3⃣to2⃣4⃣

WATTPAD:hassana3329

TUNASARWA????

MANZON ALLAH (S A W )YACE”DUKKAN WANDA YA KAWAR WA MUMINI WATA MASIFA DAGA CIKIN MASIFUN DUNIYA ,TO SHIMA ALLAH ZAI KAWAR MASA DA WATA MASIFA DAGA CIKIN MASIFUN LAHIRA ,KUMA DUK WANDA YA RUFAWA WANI MUSULMI ASIRI ,TO SHIMA ALLAH ZAI RUFA MASA ASIRI DUNIYA DA LAHIRA ,ALLAH YANA TAIMAKON BAWA ,MATUK’AR BAWAN YANA TAIMAKON D’AN UWANSA

AIKI ME FALALA????

MANZON ALLAH (S A W ) YACE “DUK WANDA YAYI ALWALA KUMA YA KYAUTATA TA ,KURAKURANSA ZASU RINK’A FITA DAGA JIKINSA HAR TA K’ASAN FARATANSA

GASKIYAR MAGANA NA RAINA COMMENTS D’INKU READERS ,IDAN BAKWAYI NIMA ZAN AJIYE TYPING NA HUTA ,TA YAYA KULLUM INA K’OK’ARIN FARANTA MUKU KU KUMA D’AN COMMENTS YA GAGARE KU ,SAI TURO STICKER WADDA BATADA AMFANI A GARENI ,COMMENTS D’INKU SHI YAKE K’ARAMIN K’WARIN GWIWA HAR NAKE SAMUN DAMAR TYPING ,AMMA SAIKU KARANTA KU SHAMUK’E KUNJI DAD’I NI KUMA KO OHO ,SHIYASA BAZAN MANTA DA AMIRA ABUBAKAR DA HUSSAINA D’AN LARABAWA BA ,MASUYIN COMMENTS HARDA READ MORE,GASKIYA KU SAUYA NIMA ZANFI JIN DAD’IN FARANTA MUKU ,NAGODE

Ganin yadda jikinsa ke mazari kuma yak’i fito da hannayensa yasata juya masa baya …batason ganinsa yana shan sigarin nan shiyasa taji zuciyarta tayi rauni ,hawaye yaciko idanunta har yayi nasarar kwaranyowa kan kyakkyawar fuskarta ….hannayensa na bayansa haka ya zagayo gabanta Dan ganin yanayinta …hawayen da ya gani a fuskarta ya k’ara rud’ashi ya zaro idanu yana kallonta yana girgiza mata kansa, batasan meyasa hawayen ta yak’i tsayawa ba saima gudu da suka k’arayi …tana kallo ya runtse idanunsa yana ajiyar zuciya …a hankali kuma yafito da hannayensa ya saki sigarin a k’asa yana takewa da k’afarsa …duk da hakan batadena hawayen ba sai zuba suke shar shar….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button