HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Ya Abdurrahman ya tsuguna shima kusa dasu yasa hannu yanatayasu gyara salat d'in,Hassana tad'an kalleshi cikin k'aramar murya tace "ya Abdurrahman tayi shiru kuwa tadena kukan ...!?ya mik'a mata na hannunsa da ya gyara yana fad'in" tayi shiru da k'yar ..har tayi bacci ma shiyasa nafito ..."ya juya yakalli Usman yace "nifa yadda kake burgeni autan Umma ka iya aikin mata yaseen ,inajin dai gidana zaka tare kadinga taya tawan aiki ko ...!?Usman ya kyalkyale da dariya yace " hakama fa Hamma sageer d'in Adda Hassana yace wai zasu tafi dani gidansu ,kumafa Umman mu bazata bari kowa ya d'aukeni ba ...ko Hamma Aminu saida yaso nakoma gidansa Umma tak'i yarda "Abdurrahman yayi dariya yace " lallai autan Umma ,gaskiya Umma tana sonka da yawa shiyasa batason rabuwa da kai "Usman yace " nima ai inason ummata ,nifa ya Abdurrahman ko girma nayi idan zanyi aure bazan tafi nabar ummana ba ...sai dai natafi da ita gidana ko kuma nakawo matar nan gidan kawai "Hassana da Abdurrahman sukayi dariya har Umma dake ktcheen saida maganar Usman tasata dariya harma ta tofa albarkacin bakinta tace" Allah sarki autana ...shiyasa nake sonka ,nima bazan iya rabuwa dakai ba autana"

Hassana tamik’e wanke salat d’in ,Usman kuma ya fara tattara gurin ,ya kwashe dattin ,Abdurrahman kallonsa kawai yake yana kallon yadda ya iya shara kamar mace .

Umma da Abdurrahman nata hirarsu ,daman Umma bata d’auki Abdurrahman siriki ba d’a ta d’aukeshi ,yadda takejin su Hamma sulaiman haka take jinsa shima .

Har Umma tagama girkinta Hussaina nata baccin ramuwa bata farka ba ,anan Abdurrahman yaci abincin rana da Umma tagama ,sai azahar Hassana tatashi Hussaina dan tayi sallah ,da k’yar ta iya tashi tayi sallar ,abinci kuwa k’in ci tayi saida Hassana da Abdurrahman suka sata a gaba tukun ,da Kansu suka dinga bata abincin abaki ,idan Hassana tabata sai Abdurrahman ma yabata ,sunata janta da wasa da tsokana ,ahaka har tasaki jikinta sai gashi taci me yawa kuma cikin farinciki.

Umma na kallonsu sai dai ta girgiza kai kawai ,ita kanta tana tunanin rabuwar y’ay’anta ,babu Wanda yafita sanin yadda suke matuk’ar k’aunar junansu ,idan ta tuna cewar takusa rabuwa dasu sutafi gidan aure har k’walla takeyi itama .

Har yamma ya Abdurrahman yana gidan ,lokacin mummy Aisha tataso daga aiki tabiyo gidan anan ta tarar dashi ,takama baki da fad’in “yanzu Abdul tun safe daman kana nan …!?shiyasa nak’agu ayi auren nan ko zaka daina damun Umma da zarya ” Umma tayi dariya tace “haba Aisha !shida gidansu kice haka ?ni dad’ima nakeji yazo muyita hirarmu wallahi”

Mummy Aisha ta kalli Hussaina da Hassana tace “yarana menene ya ramar daku haka …!?ko duk tunanin rabuwa da gidane …!?kamar jira Hussaina takeyi tafara Matso k’walla zatayi kuka, Abdurrahman yayi hanzarin cewa ” shikenan mummy zaki kuma jangwalota wallahi ,da k’yar fa muka samu tayi shiru yanzu “ya mik’e yana jan hannun Hussaina yace ” zo muje waje tawan ,zo muje kiji wata magana “yajata suka fice daga d’akin .

Ita kuma Hassana tashige d’akin Umma ta kwanta a gadon Umma tajawo filo ta rungume ,d’aukar wayarta tayi tashiga gallery tana kallon hotunan sageer masu tsananin kyau kala kala ,batasan menene dalilin fitowar hawaye a idanunta ba ,kawai sai jitayi tana kuka ,ta rungume wayar a k’irjinta tana hawaye ,k’aunar sageer na huda zuciyarta tana zagayawa ko’ina a jikinta .

Can kuma Umma da mummy Aisha nata hirarsu ,mummy nacin abincin da Umma takawo mata take cewa ” Umma (itama haka take kiranta ,Dan ta d’auketa tamkar mahaifiyarta)tace “Umma akwai wadda tayiwa Sadiya gyaran jiki lokacin bikinta da Aminu ,to nayi magana da ita gobe zata fara yiwa yarannan gyaran am are suma, ta iya aiki sosai ,mungama magana da Nabeela zasu dinga zuwa gidanta kullum anayi musu a can ,saboda nidai Indai a gidanane Abdul sakamana ido zaiyi wallahi ,bazai bari komai yatafi daidai ba ,sannan Umma bansaki ki kashe kud’inki kisaimusu wani Abu ba ,nida Nabeela duk min gama siyan komai tun daga kan kayan ktcheen har sauran Abubuwa ,sulaiman da Aminu kuma sun d’auki nauyin furniture’s ,jiya sun sameni mun gama magana “

Umma tayiwa mummy godiya mai yawa harda hawayenta ,har saida tasa itama mummy tayi hawayen ,cikin hawayen tace “idan kinayimin godiya akan wani Abu kunya nakeji Umma ,ke da Baba kun zamemin uwa da Uba ,Kunmin komai a rayuwa ,duk wani Abu da zan muku bazan tab’a biyanku ba “

Umma tashare hawayenta tace “Hakane Aisha ,Allah yabar zumuncin mu akan tafarki na gaskiya ” mummy tayi murmushi tace”Ameen ya Allah Umman mu “.


Biki nata matsowa yayinda amaren suke ramewa kamar allura ,su Kansu angwayen duk jikinsu yayi sanyi kamar ba angwaye ba ganin yadda amaren nasu suke ramewa kamar wad’anda za’a kaisu gidan mak’iyansu ,musamman Hamma sageer da a kwanakin kullum cikin tsananin fad’uwar gaba da zazzab’i yake, wataran yana zaune sai dai kawai yaji yana hawaye bai San dalili ba .

Amare nata sintirin zuwa gidan Adda Nabeela ana gyarasu ,in kagansu ba lallai ka ganesu ba saboda wani bala’in kyau da sukayi na musamman ,idan Hamma sageer yazo gurin Hassana bashida aiki sai kallonta ,yakance ” wallahi da inada yadda zanyi na had’iyeki saboda so da tuni nayi sweety “ta D’AN zaro idanu tana murmushi tace”had’iyewa kuma Hamma sageer….!?k’walla tacika idanunsa yace ” sonki ne yayimin yawa ,kullum zuciya ta batada aiki said tunaninki da begenki “ta d’anyi tagumi tace” wannan hawayen fa Hamma sageer …!?yasa hannun ya shafosu yana tsananin kallonta yace “na soyayya ne sweety ,sun dad’e suna zuba a idanuwa na wallahi ” saita girgiza kai tana maida nata hawayen tace “toh Hamma sageer kacemusu sudena zuba Dan Allah …su jirani zuwa lokacin da zan share maka su da hannaye na kaji “.


Sati d’aya yarage saura bikin duk wani shirye shirye sun kammala,anbuga katin d’aurin aure an raba ,suma amaren sun rarrabawa k’awayensu na Makaranta tare da taimakon Zahra da k’awarsu Asma’u,Hamma sageer da ya Abdurrahman d’oki da murna har yayimusu yawa .

Randa akayiwa su Hassana sallama a islamiyya sunsha kukan rabuwa da Makaranta,Malam Huzaifa kuwa ko gun sallamar baizoba a office ya zauna ,ya kifa kansa akan tebur yana kukan rabuwa da masoyiyarsa Hassana ,har aka gama bai fito ba ,Hassana da kanta tanemeshi bayan antashi …tasameshi a office ta durk’usa agabansa kanta a sunkuye tana hawaye tace” Malam kayafemin duk abinda nayimaka tsawon zamana a makarantar nan dan Allah ….kuma kayi hak’uri da …..”sai takasa k’arasawa ta fasheda kuka .

Ya d’ago kansa ya share hawayen idanunsa yace “na yafe miki duniya har zuwa lahira ,nima ki yafemin ,sannan kisa a zuciyarki cewa na hak’ura ne kawai ,amma har yanzu ban cire rai da samunki ba ,sai randa naji an Shafa fatihar d’aurin aurenki …tashi kije nagode ” yakuma kife kansa akan tebur d’in .

Haka Hassana ta mik’e jiki a sanyaye tafito daga office d’in tana share hawayenta.

Yadda suka tsara bikin zasuyi kamu ranar alhamees ,ranar juma’a kuma zasuyi walima ,ran asabar kuma zasuyi dinner kamar yadda angwayen sukeda buk’ata ,kuma Baba da Hamma sulaiman duk sun amince ayi ,Dan shi kansa Hamma sulaiman yanzu lallab’a k’annen nasa yakeyi ,Ranar lahadi kuma za’a d’aura aure, inda za’a kai Hussaina gidanta da Abdurrahman ya gina mata me kyau da had’uwa,ita kuma Hassana bayan kwana uku da d’aura aure zasu cale Abuja .

 Ranar laraba da misalin k'arfe d'aya na rana Hassana zaune tana kwalliya saboda gidan Hamma sulaiman zasuje za'ayi musu k'unshi ,wata mak'ociyar Aunty sakeena ce takeyi ,ta iya zana lalle sosai ,kuma matar aurece mijinta baya barinta zuwa tayiwa mutane sai dai mutum yaje gidanta tayi masa ,shine Aunty sakeena tace suzo ayi musu ,tun d'azu Zahra take damunsu da waya suyi su tawo Dan ita har tarigasu isa gidan Aunty sakeenan .

Hassana ta waiwaya ta kalli Hussaina dake kwance batada niyyar tashi tace “sisina kitashi ki shirya mutafi mana …kinga fa Zahra ta dameni da waya …” Hussaina tad’an ja k’aramin tsaki tace “shiyasa fa nakashe tawa wayar dan ma karta dameni wallahi …gaba d’aya banajin dad’in jikina shiyasa banason zuwa k’unshin nan …ga wata muguwar fad’uwar gaba da nake fama da ita ….zokiji yadda k’irjina yake bugawa fa ” takamo hannun Hassana tana d’orawa a k’irjinta .

Sosai Hassana taji yadda k’irjin Hussaina ke bugawa fat fat ,sai tadubi Hussainar tace “kinyi addu’a kuwa yau….!?Hussaina ta jijjiga kai idonta na sauya kala tace” nayi “sai Hassana tace” karki damu, wani zubin mutum yanajin irin wannan yanayin daman ,bari nayimiki addu’a nima “Hannunta nakan k’irjin Hussain a ta dinga karanto mata addu’a iri iri har Hussainan tafara jin d’an dama dama.

Tilas da lallashi da komai Hassana tasaka sisinta a gaba saida ta shirya itama,kamar kullum shigarsu iri d’aya ne komai da komai ,suka d’aura nik’abi a fuskarsu ganin yadda fuskarsu ke Jan hankalin maza saboda kyawun da suka k’ara .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Leave a Reply

Back to top button