HASSANA DA HUSSAINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da wurwuri Hamma sulaiman ya isa asibitin ,tunda a ranar juma’ar k’arfe sha d’aya za’a shiga da ita tiyatar ,kafin me asibitin Yakuma cika da y’anuwa da abokan arzik’i na nesa da na kusa ….Babane ya yanke shawarar cewa duk su tarkata sutafi gida suje suyiwa Hassana addu’a ,asamu ayi aikin lafiya agama lafiya ,haka suka dinga shiga d’aya bayan d’aya da kukansu suna dubata da yimata addu’a ,itakuwa murmushi ne akan fuskarta duk da ciwon da takeji Wanda bata tab’a jin makamancinsa ba ,kuma duk Wanda yashigo sai tacemasa “kayi hak’uri wane ,kayimin addu’a karkayi kuka” Usman ne k’arshen shiga,Hassana ta Shafa kansa tace”Autan Umma inasonka ,kadinga yimin addu’a kullum ,kuma ka nemar min afuwa agurin kowa da kowa ,musamman Umman mu”Usman yana kuka haka aka fitadashi .
A haka duk suka gama ganinta ,Baba yasa suka tafi gida kowa zuciya a raunane ,yace bayan anyi aikin sa dawo su ganta.
Hamma sageer da Hussaina kawai aka bari saboda basuda lafiya suma, sai Hamma sulaiman da mummy Aisha da Mamma ,sai kuma Baban ,suna zaune dukansu a d’akin da HASSANA take ana shirye shiyen shiga da ita tiyata ,Hassanar da ke kwance tadubi Hamma sageer da Hussaina da tsananin kukansu da ramar da sukayi ya sauya musu kamanni ,sai tayi musu wani irin kallo tace suzo gareta ,aka matsa suka iso gareta takama hannayensu tace musu “na rok’eku kuyi hak’uri da rayuwa a duk yadda kuka samu kanku , wannan hak’urin shine zaisa kusamu riba duniya da lahira ,kuma a kullum kudinga tuna cewa ina matuk’ar k’aunarku ” sai ta juya ta kalli mummy Aisha tace “mummy ki kula da ya Abdurrahman ,kishare masa hawayensa aduk sanda suka zuba ,kuma kicemasa NAGODE SOSAI” Mummy da ke kuka tace “zafin ciwo ne yasaki wad’annan maganganun Hassana ,insha Allahu zaki tashi ,jibi I yanzu and’aura auren Ku ” sai Hassana tayi murmushi ta girgiza kai kawai ,ta kalli Baba tace “Babana yau juma’a ko ….!?Baba yace ” hakane Hassana yau juma’a “sai ta rufe idanunta tace ” nagodewa Allah da zai azurtani da babban rana,irinta juma’a “
Minti 20ya rage ashiga da ita tiyata ciwon ciki ya murd’a ,tunda Baba yaga yanayinta ya matsa gabanta yafara nanata mata Kalmar shahada ,Hamma sageer a durk’ushe yakasa d’agowa sai had’iyar zuciya yakeyi ,yayinda Hussaina ke kwance jikin Hamma sulaiman tamkar matacciya babu inda take iya motsawa a jikinta ,Baba yanata nanatawa Hassana Kalmar har itama ta cafka ta amsa ,idanunta sukayi sama fuskarta cikeda annuri ,da murmushi akan fuskarta ta ambaci ” la ilaha illallahu muhammadur rasulillah ,sallallahu alaihi wasallam “sannan komai nata ya tsaya cak,rai yatafi ????rai bak’on duniya ????Hassana tasamu cikakkiyar shahada guda uku ????ga ciwon ciki ,ga Kalmar shahada ,ga kuma babbar rana ta juma’a???????????? .
ni Hassana D’an larabawa nake addu’ar Allah yayi mana kyautar shahada muma ????,Allah kasa ranar mutuwarmu tazama ranar farinciki agaremu???????? ,Allah kasa mucika da kyau da imani ????????,Allah kajik’an iyayenmu da kakanninmu ????????,Allah kajik’an dukkan musulmin da suka mutu tun daga kan annabi Adamu har izuwa yanzu????????,ya kamata mudinga tuna mutuwa hakan zaisa muk’ara imani a zukatanmu ,kuyi hak’uri masoyana????????,nasan yau na tab’a zukatanku ,to nima yau d’in zuciya ta ta tab’u ????,sai dai kusani mutuwa wajibi ce ga kowane mutum na duniya????????????????????
ALLAH KA JIK’ANMU BADAN HALINMU BA????????
Comments
Share
Vote
Pls
HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
TYPING????
???????? HASSANA ????????
*DA*
❣???? HUSSAINA ????❣
TAREDA ALK’ALAMIN HASSANA D’AN LARABAWA✍✍✍
page4⃣5⃣to4⃣6⃣
WATTPAD:hassana3329
® PEN : WRITERS ASSOCIATION
~only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers~
TUNASARWA????
SIRAD’I
WATA GADA CE DA TAKE SHIMFID’E AKAN WUTAR JAHANNAMA DOMIN MUMINAI SU GIFTA TA KANTA ZUWA ALJANNA ,MANZON ALLAH (S A W) YA SIFFANTA SHI DA CEWA “YAFI GASHI SIRANTA … KUMA YAFI TAKOBI KAIFI” MUSLIM NE YA RAWAITOSHI
AIKI ME FALALA????
MANZON ALLAH (S A W) YACE”WANDA YA ROK’I ALLAH MUTUWAR SHAHADA BISA GASKIYA,TO ALLAH ZAI BASHI MATSAYIN SHAHIDI KODA KUWA YA MUTU NE A BISA SHIMFID’AR SA
KULLU NAFSIN ZA’IK’ATUL MAUT
????????????????????????
Wani irin zazzafan hawaye ya zubowa Baba ,k'arfin imani da hak'uri yashiga zuciyarsa ,a fili ya furta "Alhamdulillah ,y'ata ina tayaki murna da samun rahamar ubangiji ,Allah yagama yimiki komai tunda yayimiki kyakkyawar cikawa ,muna rok'on ubangiji yabamu irin taki muma " yasa hannu ya shafi fuskarta idanunta suka rufe ,sannan yaja mayafi ya lullub'eta gabad'aya.
Ya kalli Mamma da mummy da suketa rafsa wani irin kuka da d’ora hannu aka ,ya girgiza kai yace “Dan Allah Aisha kuyi shiru …tace kar ayi mata kuka …nasan zubar hawaye dolene amma kudena wannan ihun” Baba ya nufi Hamma sageer ya d’agoshi ya tallabo fuskarsa yana kallonsa ,sai yaga Hamma sageer d’in ya zubawa gawar Hassana idanu yanata kallonta ,ya janye jikinsa daga jikin Baba yafara takawa a hankali har ya isa kusada gawar Hassana yasa hannu ya yaye mayafin da aka rufeta dashi ya tsuramata idanu ,addu ‘a yakeyi a zuciyarsa Allah ya d’auki ransa shima ya mutu a wajen ,sai yakife kansa a k’irjin Hassana hawaye na ambaliya ,da raunanniyar murya yace “na rasa mahaifina alokacin da nake buk’atarsa ,kema narasaki alokacin da nafi kowa sonki da buk’atarki ,me zan zauna nayi a duniyar da babu ke acikinta ,Allah ka d’auki raina nabi masoyiyata ….wayyo Allah zuciya ta ” wani irin tari ya sark’eshi kawai sai ya k’arasa kifewa akan k’irjinta ya sume.
Ita kam Hussaina ma batasan inda kanta yake ba awannan lokacin ,daga ita har Hamma sulaiman a daskare kawai suke ,saida Baba yabashi umarnin yataso sannan ya iya ajiye Hussaina ya jinginata da bango ya mik’e ,shi da Baba suka had’u suka d’auke Hamma sageer daga kan Hassana suka kwantar dashi a gadon Hussaina ,Baba da kansa ya kirawo doctor Wanda yake k’ok’arin shigar da Hassana tiyata ,shi kansa doctor yaji mutuwar sosai saida ya razana ,yace yajima baiji mutuwar da ta dakeshi kamar wannan ba ,shine yabawa Hamma sageer taimakon gaggawa ya farfad’o ,babu kuma yadda ba’ayi dashi ya zauna a asibitin acigaba da kula da lafiyarsu shida Hussaina ba amma yak’i ,banda hawaye babu abinda yakeyi ,yana kusada gawar Hassana yakasa matsawa daga inda take.
Baba ne yaja Hamma sulaiman gefe yace "ina wayarka ...!?Hamma sulaiman da ya zama baya gane fari balle bak'i saboda tsananin tashin hankali yasaka hannunsa a aljihu yana lalubar wayar ,yana d'akkowa ya mik'awa Baba ,Baba bai karb'a ba yace " lalubomin lambar Aminullahi "sai Hamma sulaiman yace " bazan iya ganin komai ba a wayar Baba ,idanuna dusu dusu suke gani "Baba ya girgiza kansa yana salati ,yasan shak'uwar Hassana da sulaiman me girma ce, tilas ya gigice da ganin mutuwarta.
Sai mummy ce ta karb’i wayar ta lalubo numbar tanata kuka, Mamma kuwa tana kan gawar Hassana tanai mata addu’a tanata hawaye masu zafi da k’una ,mummy tana danna kiran tafara ringin sai tamik’owa Baba ,ya karb’a a sanda Hamma Aminu ya amsa kiran, Hamma Aminu na d’aga wayar yace ” Hamma sulaiman ya jikin Hassanar …!?anshiga da ita tiyatar ne …!?Baba yayi gyaran murya yace “ba sulaiman bane ,nine Aminu ” yanayin yadda yaji muryar Baba nan da nan yasha jinin jikinsa ya rud’e ,Baba yace “matsa daga gefe zamuyi magana ” Hamma Aminu ya matsa daga cikin y’an gidansu da suke zaune jugum jugum wasu nata addu’a “Baba yace ” kanajina ko Aminu !Allah subhanahu wata’alah da yabamu Hassana ya karb’i abarsa a sanda yaso ….rok’ona agareka Aminu kasami mahaifiyarku kayi mata bayani cikin natsuwa da y’an uwanka …kar kabarsu suyi ihu da koke koke irinna jahilai …domin babu kyau ko kad’an …muma gamunan tawowa da gawar yanzunnan “tunda Baba yafara magana zuciyar Aminu take bugawa ,matsanancin tsoro ya shigeshi jikinsa Yakama karkarwa ,hawaye wani na korar wani ,kawai sai wayar ta fad’i a hannunsa ta tarwatse .
A lokacin da yafito amsa wayar Ashe Sadiya ta biyoshi tana bayansa ,wayar na fad’uwa yana juyowa yayi arba da Amsad d’insa ,ganin hawayensa yasa ta nufeshi a razane tana tambayarsa menene ya faru ,jikinsa na rawa hawaye na zuba ya fad’a k’irjin matarsa yana wani irin kuka yace ” Hassana……wayyo Sadiya Hassanar mu tarasu “da k’arfi Sadiya ta rushe da kuka tace” innalillahi wa’inna ilaihir raji’un ….Hassana ta rasu….. “Wannan magana ta Sadiya da ihun da tayi shine yajawo hankali wad’anda suke falon Umma aka firfito da gudu ,nan da nan gida ya kacame da kukan mutane ,Babangida kuwa fad’uwa yayi ya sume ,safwan ya sunkuceshi yayi d’aki dashi .