NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

Marairaicewa padima tayi itama tana rungumo NURUn cikin muryar datayi laushi ta ciwo tace”

NURU nayi tsananin kewarki wadda bantaba sanin haka nake kaunarkiba Saida Kika tafi nakasa nutsuwar zuciya,
Wlh NURU nayi kewarki fiyeda zato ga amed ya yaudareni yace yafasa aurena Amma tsoro yahani fadawasu abal Wanda hakan yasa suka tsangwameni”””kuka tasake Mara karfi sosai tana sake shigewa jikin NURUn tace”

Nidai NURU bansan ya zanyiba mutuwa kawai nakeson Yi sbd itace daidaini,
Dan Allah NURU ki yafemun abinda nayi Miki wlh nayi nadama tunda gashinan Naga ishara irin wadda bantaba tsammani ba.

Cikin mamaki NURU ta share Mata hawayenta tana cewa”

Kidaina kuka padima duk wannan yariga ya wuce Kuma shi amed kansa yayiwa sbd Allah zaibaki Wanda yafisa Inshallah idan har kin tsarkake zuciyarki.

Wasu sabbin hawaye tasaki tana satar kallon kofa tace”

NURU bazan taba daina kukaba sbd kuka yaganni.

Da tausayawa NURU tace”

Kidaina fadar hakan padima.

Padiman zatayi mgn saiga amminsu tashigo wadda takasa zama Jin sun Dade aciki tsaf hankalinsu Bai kwanta da kebewar NURU da padima ba Dan haka Bata Bari padima tasake mgn ba ta janye NURU suka fito inda ta zauna tsakiyar iyayenta suna sake zantawa Kamar kadasu tafi goben jintake Kamar tabisu kosu bita musamman Meryam wadda takeda burin dauka duk tayi aure Amma yanzu Kam ko ita Bata gama tantance matsayintaba bare harta dauko wani ya zauna a qarqashinta.

Saida jekadi taga lokacin kaita gurin maleek yayi tashigo ciki ta sanar musu tayi bankwana da iyayenta bayan anshigo da tarin kayan arziki anjere musu daga Kaleeb da Anneti sai babbar kyautar MALEEK wadda ko ciki baa shigo da itaba saidai idan sun Isa gida akai musu.

Dazata fice harda hawayenta padima ta riqo hannunta tana hawaye qasa qasa tace”

NURU ki taimakeni Banda lafiya mutuwa zanyi idan Ba’a nemamin magani ba ciwon zuciya me qarfi nake fama dashi tunda dadewa kullum bana iya bacci ki taimakeni ki tafi Dani ki nemamin magani NURU.

Kallonta NURU tayi a Dan tsorace tace”

Tun yaushe padima shine Baki fadaba idan yayi tsanani wani Abu yasameki fa?

Kallon abal tayi cikin damuwa da kulawa tace”

Abal meyasa ba’a fadamunba ko a wayane da anfadawa jekadi ta fadamun ta waya wannan ciwon ba abun Wasa bane zantambaya afia Inshallah zamu tafi da padima.

Wani mugun kallo ammi tayiwa padiman data bushe idonta ba wani alamar qarya ko yaudara atareda ita abal ya hade fuska tsaf yace”

Kije NURU Allah ya albarkaci rayuwar aurenki ya Hana duk wani Wanda beda fatan alkhairi sa’ar rabarki,
Padima bazata bikiba kowane irin ciwone zamu nema Mata magani Inshallah.

Kallon padima NURU tayi tana Bata hakuri ta ido da cewa tayi hkr Inshallah ta Mata alqawarin dawo da ita hannunta ta nema Mata lafiya idan nasu abal din baiyiba.
Da haka aka wuce da ita tabarsu suna binta da addua suka wuce ciki Babu Wanda yaceda padima dake tsaye idanuwanta sunyi jajir zuciyarta na wani irin zafi da harbawa.

Kai tsaye sashensu datake dasu afia aka maidata sbd saqon maleek daya Isa gurin jekadi ta hanyar Anneti cewar basai ankar NURU gurinsaba yau din gobe zasu koma,
Tana Isa ta tarar da Afia zaune tagama hada musu kayansu tsaf sbd suma dad ya sanar cewa gobe zasu koma dama amatse take dasu bar Nan din sukoma Kota samu kanta tayi tunanin abinda yakamata.

Tsayawa tayi daga bakin kofa tana kallon afia da duk damuwa da sanyin jiki ya bayyana atareda ita taji tausayinsu su duka ya dawo Mata sbd tafi kowa sanin burin afia akan dawo da mahaifiyarta gidan MALEEK gashi yanxu su duka qaddara ta bullo musu ta inda basa zato.

Qamshin NURUn daya cika gurin yasata dagowa sukai ido biyu kowa yakasa motsawa suka tsurawa juna ido kafin Afia ta taso ahankali ta qaraso gaban NURUn ga mamakinta saitaji afia din ta rumgumeta tana cewa”

Thank God you’re back NURU nayi kewarki.

Mamaki yasata daskarewa batareda tace komaiba ko motsawa.

Afia kuwa tarigada tasan zaman aure ko rayuwar aure tsakanin NURU da dad dinta bamai yiyuwa bane har abada Dan haka Bata sawa ranta damuwaba Dan duk duniya Babu Wadda dad dinta zaiso idan ba mum dintaba Dan haka tasan shima idan har aka koma Babu wani maganar aure dazaibi hakama NURU tana komawa Imran yadawo bazata yarda ba Imran zataso komawa Dan haka ta daure tacire damuwar komai aranta.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR????????????

Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA
Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL
Dalaal–MISS XOXO
Mabudin zuciya–HAFSAT RANO
Ubayd Maleek–MAMUH GEE

DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

08085405215

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN qNUMBER TAREDA SHEDARKU????????

0903 234 5899
[9/22, 8:52 PM] +234 703 598 9527: Mamuhgee 22
Washe gari tunda safe sakon Anneti na gayyatarsu cin abincin safe tareda ita ya iso musu suka shirya dukkaninsu itadai jekadi dama tunda safe tazo da kayanda NURU zata saka tana Palo takasa ta tsare Dan kuwa komai daya danganci NURU yanxu saiya biyo ta gurinta kafin ya isa gun NURUn.
Da kanta tashirya farhat kafin itama ta shirya cikin doguwar royal gown dinsu me adon golden stones da sequence rigar ta tafine straight shiyasa ta fidda shape din tudun qirjinta zuwa shafaffen cikin har fadin hips dinta saidai adon sequence ne ya ‘dan boye bayyanar shape din nata Sosai Sosai Amma duk da hakan yafito sai wuyan rigar dakeda Fadi sosai ta Sanya qaramar siririyar sarkar gold ta doro gyalen rigar akanta ta rufe gashinta dake daure Yana qamshin turaren hayaqin da akai Masa ta fito afia nabinta da kallon yaba kyawun datai Wanda duk be daga Mata hankaliba tunda dai duk abanxane suka fito jekadi na bayan NURU sai sauran masu Binsu suna bayansu kawunansu duk a soke kasa.

Afia ce ke kokarin janta da firar karatunsu da tun shekaran jiya yakamata su koma Amma Basu komaba itama NURUn abin sai lokacin yafado Mata musamman da tafara zuwa Court itama afian tana zuwa asibiti sama sama sbd karatun nasu.
Tun kan su qaraso aka sanarda zuwansu suna isowa suka tararda askarawan maleek kusan guda shida a sassan Anneti din afia na gani tasan dad dinsu na ciki ita Kam NURU batasaniba tunda Babu abinda tasani anan din Dan haka Babu tunanin komai dayazo Mata suna isowa aka wangale musu qofa Ana yiwa NURU gaisuwa ta musamman kafin aka juyo akaiwa AFIA da farhat suka shige.

Suna shiga palon farko duka sauran Yan rakiyarsu suka tsaya anan dagasu se jekadi suka wuce har cikin asalin palon hutawar Anneti suna shiga jekadi ta zube qasa cikin bada girma tace”

Allah yaqara MALEEK kyakkyawar zuciya data fuska,barka da fitowa.

Da hannu kawai ya amsa tareda juyowa Jin muryar AFIA na gaishesa cikin girmamawa itama.
Farhat kuwa kusadashi ta zauna tareda riqe hannunsa tana cewa”

Good morning Daddy.

Da sauri jekadi ta Raba gefen NURU data kusan sanqamewa a tsaye sbd shammatarta da abin yayi Sam ko kadan ko qamshinsa batajiba batama taba saka ran zata ganshi ananba.

Kallon afia yayi da idanuwansa masu haske cikin sautinsa na kamewa ya amsa Mata tareda cewa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button