NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

Bata ankara daya Dan farfado ba taci gaba da goga Masa tafin qafafun
Ya sake bude idanuwansa a wahalce yanason cewa ta daina ya kasa sbd hakan datake Yana Masa wani iri temperature dinsa tana hayewa sama Amma yakasa mgn sai kawai ya maida idonuwan ya rufe bacci ya daukesa me qarfi a wahalce.

Qarfe bakwai na safe yabude idanuwansa ahankali Yana furta sunayen Allah da adduar tashi bacci cikin zuciyarsa,
Motsawa yayi ahankali tareda yunqurawa zai tashi zaune yaji qafafuwansa a riqe ya Kai idanuwansa zuwa gabansa yaganta kwance rungume da qafafuwansa baccin wahala ya dauketa.

Kallo daya yayi Mata ya dauke idanuwansa daga gurin Yana zame qafafuwansa ya zuro qasa tareda yaye labulen makeken gadon ya fito Yana tafiya ahankali duk da garau yake Jin kansa ba damuwar ciwo ko daya Amma akwai rashin qarfin jiki ya nufi toilet yashige.

Harya fito tana baccin Bata farkaba Dan haka Kai tsaye ya shirya cikin Ash Armani’s ya fesa turarensa na imperial majesty rosalle ya saka takalmin manolo blahnik ya fice Kai tsaye Yana kunna wayarsa ya Kira mr Omar daya kwana zaune zaman jiran yazata Kaya yana ganin Kiran maleek yayi wuf ya dauki Kiran a qage yace”

Good morning MALEEK.

Ka kunna mota ganinan fitowa.

Da gudu mr Omar ya sauko ya nufi mota yashiga ya kunna da sauri tareda gyara parking yayi saiti daidai kofarda maleek din zai fito
MALEEK din nafitowa ya bude Masa yashiga ya rufe ya zagaya da sauri yashiga suka wuce.

Qarfe Tara da mintuna ta bude idanuwanta dasukai mugun nauyi sbd kukan datasha dakuma bacci
Tafara jujjuya idanuwan taga inda take a zabure ta miqe jikinta na rawa ta wuntsulo qasa tana kallon gadon taga bayanan da sauri ta fito cikin gadon har tana tuntube ta fice ko ganin gabanta batayi Takoma dakinta jikinta na rawa.

Daqyar ta nutsar da kanta Dan yin sallah tayo alwala tazo tayi sallah zuciyarta na harbawa da qarfi
Kallo daya zakai Mata kasan a firgice take takasa samun nutsuwa tana zaune a daki tana tunane tunane har kusan 12 tayi Dole ta fito Takoma dakin ta dauko wayarta sai alokacin taga misscals din Imran da text din Mr Omar na cewan sun wuce komawa Paris MALEEK zaiga likita.

Ajiyar zuciya ta sauke duk da bawai tasamu nutsuwa bane dajin hakan sbd ita yanzu qaddarorinta yawane dasu yanzu dame zata Kira qaddarar datakaita hawa gadon MALEEK na DELAH Giza Wanda ko ‘yayan sarauta bila adadin ba kowane yaga ko gurin zaman Shan iskansaba gata tsautsayi da qaddara yasata ganin makwancinsa dako ‘yayan cikinsa Basu taba ganiba Dan daga afia har Farhat Babu Wanda yataba shiga bedroom dinsa nako Ina Bare suka shimfidar kwanciyarsa.
Kiran Imran ne ya katse damuwarta da tunaninta sbd rashin daukan wayanta tun jiyan yasashi shiga damuwa Dole ta Dan sake suka hau magana sama sama qarshe dai Dole hakura yayi da wayar akan tayi bacci ta huta zai kirata zuwa anjima danma Bata fada Masa abinda yafaru ba bakuma tajin zata taba iya fadawa kowa har abada.

Wanka tayi sai alokacin yunwar dake cikinta tun ta jiyan ta taso Mata ta nufa kicin ta dumama sauran abincin dabaiciba jiyan taci Tasha orange juice Takoma daki sai alokacin takira Afia suka hau fira itama sama sama harsaida afian tagane tace”

NURU are you sure you’re okay???

Numfashi ta sauke kafin tace”

Eh kawai ciwon Kai ne ke ‘dan damuna shima sbd I didn’t sleep well last night ne.

Ok tom kiyi bacci yanzu Koda na 1 hour ne you’ll feel good inshallah.

Aje wayar sukai ta kwanta Dan tasamu tayi baccin Amma Sam takasa har lokacin zuciyarta Bata cikin Dadi qarshe jekadi ta Kira taji lafiyan iyayenta tukuna ma tasamu ta ‘dan rintsa baccin ya dauketa.
Bata farka ba sai yamma tana tashi wanka tayi tayi sallolinta ta Sanya riga da guntun wandon jeans baqi ta fito ta dafa kwai da farar noodles taci Tasha ruwa ta dauko ledar crunchy chips chops tazo ta zauna kallo tana ci saiga Kiran Afia ta dauka Nan suka hau waya yanzu cikin sakewa Dan baccin ya taimaketa sosai.

Karatunta yadau zafi sbd tafara exams din kammalawa shiyasa yanzu batada wani lokaci sosai karatu ne a kanta ko lokacin fira ta waya batadashi Dan wani lokacin wayar a kashe take yini saitazo kwanciya ta kunna da afia kawai take waya kafin takuma maidawa ta kashe ahaka ta gama exams dinta kwana uku ta qara akai ta tattaro tadawo gida ranar murna da farin cikin farhat Bata misaltuwa hakama afia datai tsananin kewan NURUn kusan daima kowa yayi kewarta shiyasa ranar gidan kaf acikin walwala suke Dan Jin suke kamar rayuwar gidan tadawo sbd AFIA ko yaushe tana library gurin karatun batada lokacin kowa na gidan
Farhat ma haka take turata daki tace taje tayi karatu itakuma NURU tana shiga cikinsu tayi aiki harma tayi Wasa da dariya dasu uwa uba idan ta biyewa farhat gurin wasan yara na guje guje ko qasa a playground na gidan Wanda ka zuba komai na wasan yara domin farhat Wanda ita kanta farhat yanzu take morewa playground din data samu abokiyar dake tayata shiriritarta shiyasa yanzu batada kaman NURUnta.

Hutun sati biyu kawai NURU tayi Mr Omar ya kammala komai na karatunsu dazasu fara yanzu na cikan burirrikansu,
NURU lawyer itakuma AFIA likitanci.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR????????????

Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA
Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL
Dalaal–MISS XOXO
Mabudin zuciya–HAFSAT RANO
Ubayd Maleek–MAMUH GEE

DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

08085405215

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

0903 234 5899Mamuhgee 15

Mg’s skincare
Hi my people????♀️
Ina gaisuwa
Toh albishirinku????ku karkade kunnuwanku kuji inamai sanarmaku cewa set dinmu ayanzu yazama available maiso yarugo aguje karya tsaya Sanya ayi babushi☺️kundaisan kayan mg’s dabanne ba karya indai tafannin gyaran jikine kunsan yanda sabulun mg’s herbal whitening black soap kemaida fata tazama Babu kuraje, pimples, acne,eczema, stretch mark, knuckles,black head,spot,dama duk wani matsala daya danganci fata duk wnd yayi anfani dashi yasan yanda yake maida jiki yazama abun burgewa abun kwatance, fata tadinga haskawa tana walwali duk inda kikashiga sai anyaba???? toh Inaga wannan zazzafan set Mai maida tsohuwa yarinya☺️Uwargida Takoma amarya???? amarya Takoma tamkar yanmata❤️yanmata Kuma sudawo Yan Sha shida fata tadinga walwali tana daukan Ido ???? wani abun ba’a magana shiru akeyi sai Wanda yajaraba shine zai karas????bama cika Baki duk wnd yagwada shine zaifadi ynd product din mg’s yake❤️Kuma munakara Fadi cewa kayanmu organic ne bana bleaching ba suna tsagwaran gyaranjiki ne fiye da tunaninku kuyi kokari kushigo Kuma adama daku Wanda bayada halin siyan set toh sabulun mg’s kadai kukarike kankat ne insha Allah????
Set dinmu yakunshi
Soap,body cream,face cream,body nd face scrub, cleanser,
Price:13k
Kaman ynd nafadi Wanda bazasu iyasiya set ba sabulun kadai zaibaku mamaki shikadai kukayi anfanidashi zaigoge duk wn prblm na skin living the skin fresh,smooth nd make the skin to glow set din kawai zaikara murje fatane buh ko soap mutum yake anfani dashi ba’a magana????
Soap price:3k

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button