NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

A bangare makaranta kuwa karatu tuni yadau hanyar nisa Dan kuwa yanzu tana farkon shiga aji uku ita kuwa Afia tana shirye shiryen zuwa Las Vegas karatun shekara daya kafin tadawo tashiga University anan Paris dan haka sai suka Dan shiga damuwa sbd sunrigada sunyi wata irin shaquwa yanzu wadda Sam basa iya ko yini batareda junaba gashi zasuyi rabuwan shekara daya duk da zata ringa zuwa hutu.

Ranar dazata wuce tareda dad dinsu zata tafi Dan haka rakiyar NURU iyakacinta palon ciki Bata fito babban ba har suka wuce cikeda kewar juna.

Bayan tafiyan AFIA sai Kamar wani babban nauyi yahau kan NURU sbd yanzu itace shugabar gidan ita ke bada umarnin komai ta bangare daya ga karatunta ga kula da farhat wadda itama kewar afia ta tabata Amma kasancewar yanzu tamkar ma uwa take ganin NURU sai Bata wani jimaba cikin damuwan tafiyan AFIA din takomawarta Kiriniyarta.

Yau Kam amatuqar gajiye take sbd Suma sunfara shirye shiryen fara midterm exams Dan haka karatu take Babu sauqi ta Dan hakan tana dawowa daga school wanka tayi bayan ta tabbatarda farhat tayi baccin Rana sai itama Takoma daki tayi Mata wankan ta Sanya riga fara mara nauyi da dogon pencil jeans Wanda yakama siraran cinyoyinta tareda bayyana fadin hips dinta ta sanyo hular dabata rufe kanta dukaba ta fito taje kicin tasamu fresh milk me sanyi sosai Tasha tareda lumshe fararen idanuwanta dasuka gama galabaituwa da gajiya ta fito riqeda sauran madaran tazo Palo ta zauna tana daukan wayan afia data kirata suka fara waya tun tana sawa har bacci me Dadi yafara Dan fizgarta Dole sukabar wayar ko motsawa batai daga gurinba bacci me nauyi yayi gaba da ita a palon.

Farhat data tashi nata baccin tana fitowa palon taga NURU tayi bacci kan kujera ta kalla kyakkyawar fuskarta datai fresh sbd samun hutu da gyara saita saki murmushi tareda qarasowa zata gyara Mata kwanciya ganin kaman zata fado tana Dora hannunta akanta taji dirin motocin dad dinta yadawo cikeda farin ciki ta miqe ta nufo qofa da sauri ko ta bude tareda rumgumesa cikin qasa qasa da murya tace”

Welcome dady.

Kallonta yayi cikin kulawa da mamakin meya samu muryanta take magana ahankali
Duk da qarancin shekarunta ta dade da sanin dad dinsu ba komai yake budewa Baki yayi magana ba da kallo ma kawai suna gane maganarsa Dan haka ta fahimci mamakinsa tasakeyin qasa da murya cikin rada tace”

Dady Lewa na Palo and she’s sleeping tagaji sosai da yawa koyaushe batada time din hutawa yanzu tasamu tayi bacci please dady kadamu tasheta.

Kallonta yayi suna qarasowa tsakiyar palon dan dama yasan tsawon shekarun Nan farhat Bata mgnar daya biyu saita lewa,my Lewa,my beauty kunnuwansa harsun gaji dajin sunan abakin farhat.

Dan juyi tayi daga kwancen ta sulmoyi zata fado da sauri farhat tayi kanta ta tareta Amma sbd NURUn tafita girma da nauyi saita kasa tareda saima danneta da NURUn tayi batasaniba sbd baccin yayi Mata nauyi sosai Dan tajima Bata baccin kirki Koda daddare.

Da sauri farhat ta kalli inda yake tsaye cak Yana kallon qanqanuwar yarinyar dabatafi AFIA shekaru da girman jiki da komaima.
Cikin wuya farhat tace”

Dady hannuna zai karye aunt NURU nada nauyi sosai.

Cikin wani irin taku da izzar data gama kame jininsa ya iso gurin batareda ya kalli NURUn ba ya Dan ranqwafo yakai dogayen hannuwansa masu siffar qarfi tareda tsananin taushi ya zura qarqashin bayan NURUn farhat tasamu damar janye hannunta tana yarfewa tayi dakinta da gudu tana cewa hannuna zai kumbura Bari nashafa ointment da sauri kada ya kumbura aunt NURU nada nauyi sosai.

Idanuwansa dake raunana kuzarin Wanda duk ya zubawa su ya waiwayo ya zubawa fuskar NURU wadda take wani glowing na zallar asalin kyawun da Allah yayi Mata.
Gangarowa yayi da kallonsa kadan zuwa jikinta a qirjinta ya dakatar da kallon tareda dauke fuska Yana zare hannuwansa daga qarqashinta yabar gurin sai ayau yasan babban shirmen da Kaleb ya tafka da jekadi kenan tsarar ‘yar cikinsa suka kawo Masa amatsayin negestati,
Ta Yaya suke tunanin wannan yarinyar tsarar afia zai iya hada shimfida da ita?Tama Yaya zata iya daukan nauyinsa ko ciki baya tunanin kwsmkesonta zai iya dauka bare haihuwa… unbelievable” yafada cikin zuciyarsa a ‘dan takaice sbd tunano ‘yarsa afia dake tsararta baya tunanin ko Nanda shekara biyar zai aurar da ita Dan ganin kaman tayi mugun qanqanta amma shi ba saurayiba ko ‘dan samari akawo Masa wannan.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR????????????

Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA
Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL
Dalaal–MISS XOXO
Mabudin zuciya–HAFSAT RANO
Ubayd Maleek–MAMUH GEE

DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

08085405215

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

0903 234 5899[10/7, 9:09 PM] Xynerv Sadeeq Aderm????: Mamuhgee 13
Las Vegas
Sabuwar rayuwarsa NURU Bata taba koda mafarkin samun yiba Koda kwatance itace take gudanarwa a Vegas sbd wani yalwataccen ‘yanci da gata datake samu ta bangare biyu wato Imran da Kuma su afia da mahaifinsu Wanda shine ya dauki nauyin komai nata sbd ‘yayansa.
Wata irin tsadaddiyar rayuwa takeyi a Vegas acikin lafiyayyan qaramin flat din maleek dake cikin wani babban building na masu Vegas da kanta.

2 bedrooms ne manya sosai agidan kowanne da toilet dinsa shima babba sai Palo ‘daya da kitchen sai dining area shikenan,
Komai na gidan farine sai Yan abubuwa qalilan daba farare ba Dan kasancewar gidan Dan kuf kuf yasa bayada wani kadaici ko tsoron zama Kai daya saidai uban zallar dukiya da aka narka gurin gyaran gidan.

Tunda tazo bus takebi Bata taba amfani da motar da aka Bari Dan fitarsuba Dan tuqinta bai wani gama riqewaba Amma dai tsarin tuqin ne anan Bata ra’ayi tafison idan Takoma gida.

A school tunda tafara zuwa Bata samu matsalar karatun da mutanen makarantarba ko daya Dan haka saita maida hankali kawai tana karatun saikuma gyara jiki da harkan fashion da sabuwar qawarta ‘yar Morocco take janta suna Dan fadawa ahankali ahankali.
Karatunta yayi nisa tagama gane kan farin Vegas Dan haka saita saje Takoma tamkar wata baturiyar qasar danma banbancin ita haryanxu kusan fiyeda Rabin suturarta sunanan jallabiyane saidai mafi yawanci na Turkish da Kuwait ne tafisonsu sbd mayafansu daurawa takeyi kaman scarf bata yafawa sai jeans da riguna masu har qasa Amma masu tsaga Suma da scarf take sanyasu sai handbags takarmanta Kuma mafi yawansu loafers ne masu tsada saidai Kuma yanxu tana Sanya heels musamman idan tasaka Kuwait gown.

Yau a gajiye tadawo gida tana waya da Afia taqarasa shiga cikin palon tareda rufo qofa ta wuce bedroom dinda yake nasu Dan dayan ko key dinsa Babu a gidan sbd ba’a shigarsa shiyasa ko bakin gurin qofar Bata taba zuwaba.

Ajiye Jakarta tayi tareda waya ta tube tafada toilet tayi wanka da ruwa me zafi Sosai jikinta ya saki ta fito tanajin wata irin yunwa Kuma.
Neutrogena oil kawai tashafa ajikinta sai body mist ta Sanya straight English riga Mara nauyi wadda ta zaune daidai fadin jikinta daga sama har qasa ta Sanya qaramar hula bayan tayi sallolinda bataiba tana gamawa ta miqe tareda zaran wayarta ta fito Palo ta aje wayar kan kujera ta nufi fridge Dan dauko drink da biscuits koshi tafara ci kafin ta Dan dafa ko noodles taci Dan batada qarfi ko kadan tana buqatan qarfin dahuwar noodles din Dan tun safe bataci komaiba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button