NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

Bayan fitowarsa shiryawa yayi cikin wasu fararen Armani kaftan dasukai matuqar daukan fatarsa dake glowing fuskarsa a kame yafito Yana kunna wayoyinsa Kai tsaye ya nufi palonsa na farko daya ganawa da Mr Omar Yana Isa Mr Omar na palon tsaye Yana waya da commissioner daya tabbatar musu da ankama yakoob Wanda yaqi fadar komai sai cewa komai duk azabar da ake bada.

Kashe wayar Mr Omar yayi ya waiwayo yayiwa MALEEK kallo daya ya Dan sauke kansa cikin ‘yar sakewar murya yace”

Barka da fitowa MALEEK.

Zama yayi Yana amsawa tsananin kwarjininsa da qamshinsa na cika palon da idanuwan Mr Omar din
Ya matso ya zuba Masa lemon tea me zafi ya ajiye gabansa Yana Dan fara Masa wasu bayanin sama sama shikuma Yana sauraronsa batareda yace komaiba.

Shigowar jekadi ne daukeda tray na silver me Dan girma daukeda dafaffiyar Nonon raqumi da wani ruwan madaran na musamman sai Dan breakfast Mara nauyi
Sai wata kyakkyawar qaramar jaka dake hannunta na akayan NURUn dake ciki wainda ayau din akai odarsu aka kawosu
Cikin girmamawa tace”

Allah ya qarawa maleek lafiya da walwala
Barka da tashi.

Da Kai ya amsa Yana daukan wayarsa dake ringing ta sudada ta wuce cikin palonsa na gaba ta ajiye komai akan dining ta koma palondasu maleek din suke shima ta zuba Masa breakfast kadan yafara ci Mr Omar naci gaba da koro Masa bayanai.

Sai Sha biyu ta farka ta bude idanuwanta dasukai mugun nauyi fuskarta harta Dan kumbura kadan ta dafa ta tashi zaune tana sauke ajiyar zuciya ahankali tareda rufe ido ta bude tana zuro qafafunta qasa saidai abinda takeji batajin zata iya tashi tsaye.

Shiru tayi agurin zaune tana kokarin miqewa cikin dauriya taji anbude kofar dakin
Bata buqatar dagowa sbd tasan shine yashigo
Jin shiru yasata dagowa daidai isowarsa dab da ita ya rankwafo baice komaiba ya dauketa gaba daya
Tayi qasa da Kai tana rufe idanuwanta yakaita har cikin toilet ya kwantar cikin ruwan dumi ya kalleta tareda shafa gefen fuskarta ya matso da tashi fuskar yakai bakinsa kunnenta ahankali ya furta”

Sorry.

Zamewa tayi ta kallesa ya sake shafa fuskarta ya juya ya fice yabarta da mamakinsa Bata fito daga mamakinba sai ganin jekadi tayi cikin toilet din da sauri ta zame cikin ruwan tana shigarda jikinta ruwan tana rufe ido
Kenan shine yake cewa tayi hkr.

Cikin nutsuwa jekadi ta qaraso gurinta tana cewa”

Ni tamkar uwace karki ji komai magani kawai zanbaki wannan sirrinkine da mijinki Nima sbd baisan yazaiyi mikin bane kisamu kyakkyawar kulawa.

Ruwan zafi ta kunna ruwan da NURUn take ciki suka dauki zafi Sosai
Ta bude wata babbar kwalba cikin kayan data shigo dasu ta zuba cikin ruwan take toilet din yadauki wani qamshi NURU kuwa tanajin ruwan na shigarta ta koina jikinta yafara Dan sakewa Yana Mata wani iri
Jekadi taqara zuba Mata wani abun daban kafin ta dibi ruwan zafin ta zuba cikin wata roba tayi hade hadenta ta ajiye Mata tace”

idan kingama wankan kiyi tsarki da wannan.

Juyawa tayi ta fice sbd tausayin NURUn takeji sbd alamun dasuka nuna tana cikin mawuyacin hali.

Wanka tayi sosai taji dadin jikinta tayi tsarki da ruwan da jekadin ta jiye Mata tun alokacin taji wani irin sauyi Sosai agurin ta Gama tafito ahankali daureda towel ta nufi gaban mirror dinsa ta shafa mansa tareda spray ta dauki kayan data gani an ajiye Mata Wanda da Alama jekadi takawo ta daga kayan tana kallo dukkaninsu Babu me nauyi duk na Shan iska ne
Bata wani damuba sbd jirin datake gani ta saka wata doguwar qaramar riga Mara nauyi tayi drying gashinta daqyar ta ‘daure da sabon band fito palon tana tafiya ahankali jekadi dake tsaye dining tana jiranta tai Mata sannu tareda ja Mata kujera ta zauna tana gabatar Mata da abubuwan dazata fara Sha kafin komai.
Daqyar ta daure Tasha duka ko abincin Bata iya tsayawa taci ba Takoma daki ta kwanta
Jekadi ta tattare kayan ta fice dasu
tana fita Mr Omar ya sulale yabi bayanta Dan bawa maleek lokacin hutawa
Ya miqe ya koma ciki Yana duba lokacin sallah da yayi.

MAMUH#Mamuhgee 47

Bacci takeyi har lokacinda ya Shigo din,ya kalleta tareda sauke boyayyar ajiyar zuciya ya juya ya nufi toilet yayo alwala yazo ya fice batareda ya tada ita ba Dan baccin Yana Bata nutsuwa da damar yanayinda takeji.

Yana fita bada jimawaba ta farka ahankali ta tashi zaune itama tayo alwala tazo tayi sallar Takoma ta kwanta tanajin zazzabin datake ji na qara shigarta ta lumshe ido tana sake shigewa bargo idanuwanta a rufe.

Qarfe goma aka Isa da lailah airport acikin wata sirrantacciyar mota
Lokacin afia tafi mintuna ashirin agurin tana jiran isowarsu Dan Haka tana ganinsu ta fiddo doguwar jallabiya da Dan qaramin mayafi da goggles datazowa da mum din Tata dashi ta nufi motarsu itama tata fuskar Bata bayyanataba yanda za’a gane itace ta bude motarsu ta shiga baya inda mum dinta ke zaune tana kakkama jikinta tayi wani duhu cikin kwana biyu ga wani irin tsamin dauda da wahala na tashi ajikinta
Cikin tsananin baqin cikin ganinta Haka da kaunar mahaifiyarta me qarfi afia ta rungumeta gabaki daya tana cewa”

Mum.

Zarewa Lailah tayi ta kurawa afia ido idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin baqin ciki da dumuwa tarema da tsoron halinda rayuwarta tashiga kokuma ma Wanda tariga tashiga,
Ahankali ta bude Bakinta dake rawa wani tsamin Baki ya feso yacika motar Amma afia ita Sam batama jisa sbd Babu abinda uwarta zata zama ta gujeta da rawar murya tana hawaye tace”

Afia,afia my baby,afia my little princess I’m sorry baby ki yafewa mum dinki Amma ki yarda Dani bantaba aikata kisa ba Kuma bazan taba aikatawaba…ban aikata ba…bazan taba iya aikatawaba…ban aikataba…banyiba…

Riqota afia keyi tana cewa”

Mum mum na yarda Baki aikataba
Mum na yarda
Na yarda mum”.ganin mum din takasa daina fadar Bata aikataba cikin firgici Kamar lokacin abin ke faruwa yasa afia rikicewa tana korarin kwantar Mata da hankali cikin kulawa hankalinta na neman tashi sbd ganin alamun kaman mum din har lokacin tana cikin shock saidai Kuma….
Imran ne cikin hali na damuwa daya shiga akan lailan tun lokacinda Mr Omar yayi Masa bayanin komai gameda Dan tabuwa da kan lailan yayi sbd Shiga hali na shock lafiya zata ringa komai Kamar yanda take sai dai idan ta tuno abindaya faru na kisan abin zai dawo Mata zata fara fizgewa tana fadar ba ita tayiba cikin tsananin tsoro da firgici,
Shi kansa bazaiso afia tasaniba sbd hankalinta zai tashi yakoma kan kula da neman lafiyar mum dinta bazata taba maida hankali kan karatuntaba Kuma Dan Haka shima ya shirya kula da al’amarin bazai Bari tasaniba yanzu sai tagama kammala karatunta tsaf yanama fatan zuwa lokacin lailan tasamu lafiya Dan Haka shima ya yanke shawaran komawa Vegas gabaki daya zai zauna da lailah Dan nema Mata lafiya ta dawo daidai ta gyara rayuwarta ta ingantata yanzu kan tunani da hanyar dazata bullar da ita sbd Lailah tamkar uwa ya dauketa Dan kuwa itace wadda tafi sonsa aduniya bayan iyayensa sbd itanema yake Paris baibi iyayensaba Koda tabar maleek dasu afia Basu rabu ba shida ita Kuma sbd itane yake tareda maleek Yana aiki a qarqashinsa farko sbd ya kula dasu farhat dasuka shaqu.

Ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda fitowa ya zagayo yashigo bayan ya zauna dayan gefen lailan suka sanyata tsakiyansu ya dago ya kalli afia data fara shiga firgici cikin kulawa da kwantar Mata da hankali yace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button