NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

NURU idan Banga amed mukai magana ba akwai babbar matsala wlh komai zai lalace zamu rasa komai da iyayenmu duk mutuwa zamuyi.

Zaro manyan fararen idanuwanta NURU tayi jikinta na daukar rawa tana sake padiman takasa magana tana neman yin baya ta fita a rude padima ta riqota da qarfi tana cewa”

NURU wlh dagaske nake idan bangansa munyi magana ba komai zaifaru Dan Allah kimin hanya naganshi idan nadawo zan fada Miki komai Amma wlh rayuwata na cikin hadari danasu abal ma..

Kasa fahimtarta NURU tayi sbd firgici sai rawa da jikinta keyi ganin hakan yasa padiman taja wani qaramin tsakin takaici tareda girgizata da qarfi ta jawota ta direta zaune tafara shafa bayanta tana hura Mata iska tana kiranta ahankali ahankali hartafara nutsuwa tana dawowa hayyacinta saidata rarrasheta tadawo hankalinta tsaf tukuna ta janyota ta kwantarda kanta kan cinyarta tafara Sabin hawayen samun yaddar NURUn tasake fada Mata abinda tafada Mata da farko NURUn daketa ajiyar zuciyar ta qanqame padima cikin tausaya Mata murya amatuqar sanyaye tace”

Padima idan kikaga amed din shine zesa bazaki kashe kanki ba ko?

Eh NURU bazan kashe kainaba Ni sbd ma kune nakeson ganinsa na nema mafita.

Haka ta lallaba NURU taringa marairaice Mata da kuka hartayi nasarar cika tunanin NURU da tausayinta akan alamarin shiyasa washe gari da za’aje wankan ruwan Madara saita lullube fuskarta taje amaimakon padima bayan tayi Mata hanya sunyi sauyin kaya ta fitar da ita gidan masu wankan dasuka ganta saisuka tambaya tace ai yanzu ita za’a ringawa ba padima ba dayake bayin qasane gabaki daya saisuka yarda sbd manyan bayi basa fitowa delah bare akawo musu irin wannan.

Dama Shima NURU taje ta sanar dashi padima zata fito tanason ganinsa shiyasa yaje inda suke haduwa Yana jiranta danshima a mugun qage yake da ganinta Dan wlh Shima be shirya mutuwaba tunda yasamu labarin ita aka bayar yasan qaryarsa taqare kashesa zaayi duk ranarda akaji shine yafara kwanciya da ita.

Kamar munafuka haka take tafiya tana waiwaye tana boye fuska harta iso Yana ganinta da gudu ya qaraso yakama hannunta suka nufi can nesa da gidajensu cikin wani lambu bayan bishiyar ayaba ya rungumeta Yana cewa”

Ya Allah Padima nafekushi
(Ya Allah padima Nayi kewarki sosai)

Kuka tafashe dashi tana turesa daga jikinta tace”

Amed duk mutuwa zamuyi
Banason mutuwa guduwa zanyi da qasarnan zanshiga duniya bazan tsaya akasheni ba…

Riqota yayi da sauri Shima cikin firgicin yake yace”

Padima ki nutsu musamo mafita Nima angaya Miki na shirya karban wannan hukuncin ne?
Bazan iyaba nikaina mafitar nake nema.

Zamewa tayi qasa tayi zaman dirshan tana cewa”

Amed kayi gaggawar samo mafita kokuma kawai mu gudu.

Mu gudu muje Ina padima?
Idan muka gudu burirrikanmu fa damuka Dade muna….

Cikin masifar tashin hankali ta katsesa da cewa”

Burin banza tunda Saida rayuwa zamu cika burin,
Ni kaga kawai musan abinyi wlh na cikin masifa wannan wane irin balai ne nasaka kaina aciki amed ka cuceni…

Kinga yi hakuri kidaina kukan yanxu mafitarmu dayace ajanye badake abada NURU.

Wani kallon takaici da baqin ciki tai Masa tana cewa”

Sun San da NURUn suka badani sbd tunanin ita wawuyace batada wayo Ni bansan inda zansaka kainaba zuciyata fashewa zatayi….

Da sauri ya durqusa gabanta cikin Dan samun sa’ida yace”

Muyi amfani da sanyin halinta kiyi Mata wayo ki gurbata Mata tunani da tsananin tausayinki ki Bata tsoro da rayuwar iyayenku da kanta zata bada kanta.

Dakatawa tayi da kukan datake ta dago idanuwanta dasuka gama kunbura sukai jajir ta kallesa tana qoqarin karban abinda yafada din cikin nazarin maganar tace”

Kumafa hakane..
Batada wayo zan iya sata ta bada kanta da kanta.

Zabura tayi ta miqe tsaye tana share hawayenta cikin farin ciki tace”

Meyasa banyi tunanin hakanba tun farko?
Meyasa na tsaya Bata lokacina cikin tsoro da tunanin zan mutu bayan inada NURU.

Riqosa tayi da sauri cikin tsananin farin ciki tace”

Amed kashirya komai zai tafi yanda mukeso zanji da NURU sauran aikin idan mukazo tareda ita saikayi naka.

Rungumeta yayi Yana cewa”

Karki damu tunda munada wadda zata shiga tarkon mukuma mu fita kuka yaqare sai Dadi da rayuwar delah gizah dake jiranmu.

Shafarta yashiga yi Yana lallashinta da qara Bata shawarwarin yanda zasuyi hardai suka samu suka sake biyan buqatarsu agurin Saida duhu yadan yi yarakota har bayan gidansu ta zagaya tashige yakoma cikin farin ciki.

Itama cikin farin cikin tadawo gidan ta tararda NURU a daki tana jiranta cikin firgici da tsoron rashin ganin dawowarta kan lokaci tana ganinta ta taso da sauri cikin tsoro ta rungumeta tana sauke ajiyar zuciyar ganinta tace”

Padima kinbani tsoron rashin dawowarki kan lokaci.

Murmushin jin Dadi padiman tasaki tana rungume NURUn tace”

Wallahi Bet’ami afek’irihalewi NURU.
(Wallahi Ina tsananin sonki NURU)

Ajiyar zuciya kawai NURU ta sauke suka qarasa komawa ciki suka zauna ta marairaice fuska tana Shirin fara hawaye NURU ta katseta da cewa”

Padima karkiyi kuka Dan Allah tunda kingansa kinsamo mafitar matsalarki ko?

Girgiza Mata Kai padima tayi tana tsoyayo hawaye tace”

NURU banason mutuwa,
Banason abal da ammi suma su tafi su barku dagake se meryam qilama duka tafiya zamuyi mubar DUNIYAR bansan yazanyiba duk nice na janyo shiyasa nakeson na kashe kaina nahuta kowama ya huta.

Da sauri NURU ta girgiza Mata Kai tana cewa”

Padima bazan iya Bari ki kashe kankiba gwara mu mutu gabaki dayan koma menene yafi Mana sauqi bazamu iya juran rashin ‘daya daga cikin ahalinmu ba kidaina fadar hakan muna tsananin sonki bazaki mutuba yanzu inshallah.

Jan numfashin kuka tayi murya na fita daqyar tace”

NURU kinsan menene yake faruwa ga duk negestati dinda aka Kai aka tararda batada budurci tabawa wani??

Ras Ras qirjin NURUn yayi wani mummunan bugawa harsaida jikinta ya nuna hakan sbd rawar daya Dan dauka ta kalli padima da fararen idanuwanta cikin rashin fahimta tace”

Meya kawo wannan tambayar padima?

Sunkuyar dakai tayi tana tsoyayo hawaye tace”

NURU nida amed mun…..

Wani mummunan tarine ya qware NURU idanuwanta suka firfito tafara tarin cikin azaba da tashin hankali tun tana shafa Mata baya hardai dole suka fito daidai fitowar amminsu Nan sukai kanta akaita Bata ruwa Ana fesa amata Amma sosai ta sarqu idanuwanta sunyi jajir sbd azaba cikin fada ammi tace”

Menene ya sarketa padima?

Ammi kawai zaune take saita fara tari shikenan ne kawai.

Fitowa abal yayi daukeda sabuwar madarar raqumi yabata yakuma fesa Mata take abin yafada Mata tafara fidda numfashi daqyar tana rufe idanuwanta cikin galabaituwa.

Padima ta tayata ta watsa ruwa takaita daki itama tadawo tayi wankan tazo tayi sallah saikuma takejin kunyar NURU din Amma Kuma tunda dai amfani takeson yi da ita dole zata fada Mata hakan.

Kwanciya dukkaninsu sukayi babu ko me dogon motsi sbd tunanin da kowa keyi musamman NURU dake cikin tashin hankalin jin masifar dazata samu ahalinsu.
Washe gari ma NURU ce taje wankan ruwan madaran haka zalika takasa sake tankawa padima maganar dasukai din sbd har lokacin shock din maganar Bata saketaba.

Padima ganin ankwana biyu NURU taki cewa komai gashi zuwa lokacin kowa ya shaida NURUn Bata cikin hayyacinta tana cikin tsananin tsoro da tashin hankali saidai anyi tambayar duniya taqi fada sai kuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button