NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

MAMUH

Last free page

ZAFAFA BIYAR????????????

SAFIYYAH HUGUMA
BILLYN ABDULL
MISS XOXO
HAFSAT RANO
MAMUH GEE

DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

08085405215

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

0903 234 5899
[10/7, 9:09 PM]: Mamuhgee 6
Gyara kwanciya tayi ahankali cikin sanyin jiki da rashin kuzarin daya mamayeta na kukan datun jiya da aka kawota ta kwana tanayinsa.
Juyar dakai tayi daga kallon makeken dakin baccin ma’ana bedroom dinda take Wanda ita kaf rayuwarta da tunaninta dama irin labare labaren da padima ke fada Mata akan akwai daula da jin dadin rayuwa tareda qyale qyalin rayuwa Bata taba ayyano tunanin ganinsu Kamar hakaba abin ya shallake tunaninta musamman da tun jiyan sanyin AC ke shigarta a hankali Saida ‘dayar me aikinta data shigo dubata cikin dare taga yanda ta qudundune ta bude Mata qaton duvet me tsananin laushi da Sanya nutsuwa ta lulluba Mata batamasan lokacinda tasake shigewa cikinsaba tana gyara kwanciya sbd sanyin yayi Mata yawa ga tsoron baqunta na kwanciya daki ita daya.

Jin akaro na biyu ansake kwankwasa Mata qofa Ana sake sanar da ita anagama shirya Mata abinci yasa ta tashi zaune tareda miqewa ta nufi qofar qafafunta na rawa murya na rawa cikin sanyi tace”

Ganinan zuwa.

Bayi Takoma akaro na babu adadi tana sake kakkala ko Ina batasan Yaya zatai tayi wanka ba gabaki daya a firgice take ita yanzu ta daina kallon wasu abubuwan na masu daula amatsayin Jin dadin rayuwa sai abun tsoro.

Jin shiru da yawa yasa jekadiyar Kaleb shigowa bedroom din Kai tsaye ta duba makeken gadon Wanda yake zagaye da wani irin transparent labule fari tas taga Bata hango daga ciki kan gadon saita juya tana kallon qofar toilet ta qaraso ahankali takira sunanta.

Jin jekadi ce yasata fitowa a sanyaye tana kallon qasa ta tsaya daga bakin qofar bayin.
Kai tsaye jekadiyar ta fahimci komai dama Kuma daga yau ne za’a fara kokkoyawa NURUn komai hatta kwanciya sai ankoya Mata.

Shiga bayin tayi tana cewa”
Biyoni kigani.

Shiga sukayi bayin tafara nunnuna Mata komai daya bayan daya tareda fidda sabbin setin brush masu tsadar gaske da toothpaste Suma kala kala sai towels da aka jere Suma kusan sunfi guda biyar bangaren kayan wanka kuwa su sabulu da turaren wanka ba’ama magana Nan dai ta tayata komai har kusan wankanma ita tayi Mata Saida suka gama tafito NURUn tasake dauraye jikinta tafito daureda towel dinda yafi kowanne girma shima kusan daqyar ta daurosa kallo daya jekadi tai Mata ta dauke Kai tana sake yabawa da jinjinawa tunanin kaleeb na karbanwa UBAYD MALEEK yarinya ‘danya sharaf sa’ar ‘yarsa Kamar wannan tabbas za’aga ‘yaya masu manyan idanuwa da hanci Dan kuwa NURUn tubarkallah uwa uba UBAYD din da shikam idan shima ‘yayan zasu dauko angama magana.

Da kanta ta tsaya tana sake nunnunawa NURUn wasu abubuwan na dangane da shafa da qamshi da sauransu hardai ta shiryata cikin doguwar Bahrain gown blue wadda tasake haskota ta nada Mata gyalen take tayi fes kamar ba NURUn abal ba suka fito tana biyeda jekadi Kamar jela suka fito babban matsakaicin palonta suka nufa inda aka jere Mata abincin sai alokacin hanjinta sukai wani qugin yunwa Dan rabonta da abinci dama tun jiya da a gida ammi tai Mata dole ya Dan ci sbd cushewar ciki da damuwa.

Zama tayi Nan daya daga cikin bayinta tazo ta zuzzuba Mata komai nanma Saida jekadi ta nuna Mata amfanin kowane cokali duk da Bata iyaci dacokali ba tanada nutsuwar cin abinci tun agida kowa yasanta a natse take gudanarda komai na rayuwarta Wanda zaisa Kai tsaye bazaka gane batasan komaiba na wayayyi ko wayayyiyar rayuwa.
Ba laifi taci abincin sosai sbd tana jin matauqar yunwa gashi Kuma bazatace ta taba cin abinci irin wannan ba.
Bayan tagama cin abincin janta jekadi tayi aka sake kimtsata suka nufi gurin Kaleb Dan Kai gaisuwar safe dakuma Kai godiya da zaben dayayiwa NURUn Wanda jekadi a hanya take fada Mata yanda zatayi da yanda zatace.

Suna Isa Saida sukai tsayuwar kusan mintuna talatin kafin akai musu iso suka shiga bangaren tun daga qofar farko NURU ke kallon aljannar duniya danma ba halin bude ido sosai tayi sbd dokace babu Wanda ake Bari yakalli fuskar negestati batareda NEGES dinta yafara ganinta ba bare ita datake ta MALEEK guda shiyasa kusan fiyeda Rabin fuskarta rufe yake cikin burka(hular doguwar rigar dake jikinta)

Duk tarin qofofin Palo palon dasuka wuce akwai masu tsaronsu harsuka Kai wadda tafi kowacce zama babba da tsaro
Nanma Saida akai musu iso tukuna aka bude musu suka shiga aka rufo.

Zubewa jekadi tayi tana kwasar gaisuwa cikin tsananin girmamawa da ladabi.
A natse itama NURUn ta durqusa qasa kanta na qasa ta yaye fuskarta cikin sanyin da nutsuwarta ta gaidashi batareda tayi Masa kirarin dataji jekadi nata jerowaba sbd Bata iyaba.

Kallo ‘daya yayiwa NURUn ya tabbatarda nutsuwarta ya dauke Kai Yana amsa gaisuwarsu tareda Basu izinin miqewa.

Basu wani jimaba suka fito zuwa sashe sashe na cikin delah din Wanda wani sashen a mota suka jejje sbd nisa da girman DELAH din,
Ayau ta tabbatarda arziki ma Ashe na wani sunane Dan kuwa taga inda arziki yake magana,
Tabbas delah wani Depot ne na arziki Dan idanuwanta da tunaninta sunkasa daukar wasu abubuwan data gani ahakanma akecewa gizah ta dame delah tabbas idan mutum beyi da gaskeba a irin Nan tsaf imaninsa zai barsa sbd kwadayin dawwama acikin irin wannan daula ta mulki.

Sai magriba suka samu damar dawowa sashenta duk da haka bawai koina suka samu zuwaba Kai gaisuwa saidai duk inda sukaje babu Wanda yaga fuskarta andai tabbarmusu da sabuwar negestati ce.
Tarin tukuicin dukiyar data samu ayau din Bata bayyanuwa danma asalin tukuicin na tafe ne ranarda za’a tabbatarda budurcinta delah ta sheda.

Kallon uban dukiyar zinarai da situru tayi tana rintse idanuwanta cikin tsananin azabar gajiya Dan qafafuwanta har wani numfashin azaba sukeyi daqyar ta miqe ta daddafa tashiga toilet tayi wanka ta gasa qafafuwanta tana tsiyayar hawayen tausayin kanta da kewar iyayenta itafa shikenan yanxu haka zataita rayuwa daga ita sai bayi sai idan neges dinda take tasa ya buqaci ganinta a turakarsa.

Tunanin hakan yasa kukanta tsananta tafara kuka sosai cikin bayin tana cusa kana cikin qafafunta Dan zaune take cikin bathtub.
Da kanta ta rarrashi kanta tasake dauraye jikinta tayi alwala tafito tazo daqyar ta tsaya akan qafafunta tayi sallolin da duk basuyiba yau din tana idarwa da kanta ta sidado ta fito cin abinci da yunwama Kamar ta kusa kasheta.
Tana zama dakanta ta zuba abincin sbd duk basanan suna gurin sallah Suma Dan Suma Kam sun gaji hannu tasaka Bata tsaya saka wani cokaliba kadanma taci sbd cikinta daya qulle tasha lemun sabuwar abarba ta miqe ta nufi daki tana shiga ta kwanta kife take baccin wahala yayi gaba da ita.

Washe gari ma yini tayi daki kwance abinci kawai ke fiddo da ita Palo har dare bataga jekadi ba sai washe gari da yamma tazo bayan ta tabbatarda NURUn ta huta daga wahalar shekaran jiyan kafin suka fara gudanarda aikin dake gabansu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button