NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

Yawwa dai Ngd Sosai.

Suna Isa har kofar dazata sadasu da sassan Matar maleek ma’ana sassan NURU anan akai parking suka fito Kai tsaye suka shige hanyar suka wuce sassan NURU sukabi wata hanya sukai tafiya me tsayi datasaka padima fara waiwaye tana son yin mgna Amma tana dannewa sbd tasamu tafara riqe abinda za’a Bata din tukuna.

Sassan maleek suka nufa suka kusa can baya sosai inda wani boyayyan gurin sirrinsa yake jekadi ta waiwayo tareda kallon padima tana bude kofar tace”

Bismillah shigo daga ciki.

Ba wani tsoro padima ta qaraso tana leqawa ta shige sbd ganin kamar dakin ajiyar dukiyane ta qarasa ciki tana dube dube tanajin matsuwar abata abinda za’a Bata ta bar gurin sbd kaman tsoro da fargaban gurin na neman shigarta.

Mintuna biyar ba’ayi ba da shigarta saiga jekadi dauke da ruwa da drinks masu sanyi a tray ta qaraso tana ajiyewa kan table dake dakin tana cewa”

Bismillah.

Dagowa padima tayi ta kalli tray din kafin ta kalli jekadi tace”

Anan ne saqon yake?

Wannan karon jekadi Bata kalletaba tace”

Eh saqon ne za’a Baki idan kinyi hkr Yana isowane.

Shiru padima tayi cikin qaguwa da gagfawarta ta saqon yashigo hannunta tasaki guntun tsaki cikin ranta tareda Kai hannu ta dauki lemun takai bakinta tafara kurba ahankali tana kallon kofa tana Jin matsuwarta na qaruwa harta shanye lemun ta dauki ruwama Tasha kadan ta ajiye tareda Miqewa dagakan kujera daya tal dake dakin sai table da kayan adon daki masu kamar zaiba ta juyo tana kokarin komawa ta zauna taji wani irin gumi da zafi zafi me tsanani Yana tasowa daga cikin jikinta ta hadiye wani wahalallen yawu sbd bakinta dake gauraya da wani irin mummunan daci ta juyo da sauri tana share gumin fuskarta tana kallon jekadi da alamar tashin hankali da azaba tace”

Me Kika bani???
Me kikeson yimin???
Innalillahi wayyo Allah
Mutuwa zanyi azaba nakeji me tsanani….
Wurgi tayi da dankwalin kanta tana fige rigar jikinta cikin wata mummunar azabar dabata taba Jin makamanciyartaba arayuwarta ta zube qasa tana yagar jikinta tako Ina tana cewa”

Dan Allah ki taimakeni
Jikina cikinsa wuta ake hurawa
Dan Allah kibani ruwa
Zan mutu……

Shure Shure tafara jikinta na rikidewa jajir duk inda ta Sosa Kota fizga saiyayi wani irin kumburi kaman wuta ta koneta a gurin take ta haukace tana Shure shuren azaba tana ihun mummunan yanayi Jin takeyi kamar ruwan dalma na sirkuwa cikin jininta da bargonta..

Ihunta yasa jekadi juyawa ta fice daga dakin tareda rufewa ta waje ta cire qaton mukullin ta bar gurin Takoma can kofa daganan ta dauki hanyar zuwa gurin Anneti da akaiwa isarwada sakon zuwan jekadi.

Da murmushi Anneti ta kalli jekadi tace”

Barkan jekadi da dawowa lafiya,
Muna fatan anbaro Mana su maleek da mushransa tareda ‘yayansa lafiya?

Da murmushi akan fuskan jekadi cikeda biyayya tace”

Alhmdlh muka barosu Inshallah.

Masha Allah to Yaya bakuwar mushrah?
Da ita kuka dawo dai Ina fata?

Sauke Kai jekadi tayi tace”

Da ita muka dawo saidai tariga ta wuce delah inshallah Bata biyo ta Nanba.

Masha Allah shikenan kije kihuta kin debo gajiyar Kai baquwa da dawowa da ita Dan Haka kije ki huta na tsawon kwanaki shida bakya buqatan fitowa kawo gaisuwa nabaki daman hutawa tukuicin Kai baquwar NURU da dawo da ita.

Cikin tsananin farin ciki jekadi tace”

Allah yaqarawa Anneti tsawon Rai da lafiya tareda girma, jekadi godia take sosai da matuka.

Murmushi kawai Anneti tayi tareda gyada kai tana cewa”

Amin.

Tashi jekadi tayi ta fice tana sake miqa godiya.

Tana fita hamdala ta sauke sbd hutunta zaibata ikon rike aikin gabanta da kyau su samu su gano asalin maqiyin maleek da nahaifinsa daya rasu Wanda suka shafe shekaru suna bibiya.

Sassanta NURU ta nufa inda takeda babban Palo da daki tareda makeken toilet dinta ware musamman acikin sassan na NURU tareda makeken dakin bayin sassan dake gefen nata.

Wanka tayi ta huta taci abinci sai alokacin tasamu ta rintsa dataga tafara aikata aikin kaleeb da maleek wainda zata iya bada ranta akansu.

Washe gari da sassafe ta saci jiki Babu me gani ta nufa gurin padima daukeda abinci cikin kwando tana Isa ta saka mukulli ta bude kofar ahankali tareda shigowa ta maida ta rufe ta ajiye kwandon hannunta tana kallon padima da kamanninta suka Gama sauyawa zuwa wani irin yanayi na tsoro da firgici tana fidda wani irin azababben Nishi dake fitar Mata daqyar.

Gyaran murya jekadi tayi tana kallonta batareda taji tausayinta ko dayaba aranta.

Daqyar cikin tsananin azaba padima ta dago idanuwanta dasuka kumbura suntum dama fuskarta Baki daya
Dukkaninta tayi jajir koina jininta.

Da hannu jekadi ta nuna Mata abincin data shigo dashi tana cewa”

Ga abinci Nan kici zai taimaka Miki kadan gurin samun karfin iya daukan dose din anjima.

Wasu siraran hawayen azabane suka silalo Mata ta gefen ido ta bude bakinta daya kunbura batako iya motsashi daqyar can qasa ta iya furta”

Meyasa? Meyasa akemin Haka????

Numfashi jekadi ta sauke ahankali tareda kallon padiman tace”

Da zakiyiwa kanki adalci tun Baki lalace da yawaba da kin Fadi inda Kika samo wannan garin da kanki Amma nasan burinki da gurbataccen tunaninki bazai Bari ki zabi hanyaba.,
Wannan shine aikin da kikaje gidan ‘yar uwarki aikatawa akan mijinta kokuma nace akan MALEEK sbd qyashi da hassada sungama cinye zuciyarki gashi kin samu kanki acikin abinda tun kafin kizo duniya yake Dan haka batareda wahalarda sauran rayuwarkiba kifadamun inda wannan garin meriz din yafito yashigo hannunki.

Rintse ido tasake Yi cikin wahala wasu siraran hawayen suka sake gangaro Mata tanason fashewa da kuka batada hali sbd batada qarfin iyawa tanaji tana gani jekadi ta fice tasake rufeta cikin dakin dakeda tsananin duhu da zafi ta daga hannunta dake rawa ahankali ta wawuro abincin taga flatbread na alkama da dafaffuyar madara
Jikinta na tsananin rawa takai madarar Baki ta shanye tana Gama shanyewa tasaki cup din tana zare idanuwanta dake firfitowa kaman zasu tsinko jikinta ya tsananta rawa ta kife agurin tana ihun da baya fita ko kadan sbd dushewar murya cikin azaba Dan Ashe anxuba meriz din ciki.

Kwanan padima biyu Ana shayar da ita meriz ahankali ahankali Wanda yagama illata dukkanin jini da gangar jikinta tareda fatarta da duk tagama sabewa Takoma Kamar wadda aka tsoma cikin tafasasshen ruwa takai takawo ko motsi batayi Wanda yasa hankalin jekadi tashi ta sbd ganin Kamar padiman zata mutu saita dakata da Bata saidai dai gabaki daya padima ta sabule tashiga cikin wani irin mawuyacin hali na azaba tanajinta Amma ko motsi Bata iyayi banbancinta da matacci numfashin datakeyi ne kawai Wanda shima cikin tsananin azaba takeyinsa,
Tayi kukan zuci Dana ido Wanda baida amfani sbd dukkanin nadamarta Mara amfani ce tunda yau Bata ganin iyayenta bare ‘yar uwarta Susan halinda take ciki bare su yafe Mata ko haqqinsune yakamata yasata cikin wannan mummunan qaddarar.,
A da batada fatan datakeyiwa iyayenta da ‘yar uwarta tabasu tsoro Dan tayi amfani dasu saina Kiran mutuwa yau gata zatayi mutuwar bama ta gataba ta wulaqanci wadda taso maleek yayi gashi ace itace zatayi.
Hawaye suka gangaro gefen idonta suna sauka kan fatarta dake radadin azaba tace”

Abal Dan Allah kuyimin adduar sauki da rahamar ubangiji Ina cikin tsananin hali da gurbatan zuciya ya kawoni ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button