NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

Sai alokacin ta dago ta kalli jekadin jikinta duk yakuma yin sanyi ta bude baki ahankali tace”

Nagode jekadi.

Gyada Mata Kai jekadi tayi tana miqewa tace”

Ranki ya dade Zaki iya tafiya.

Miqewa tayi ta nufi kofa tana Jin gabaki daya gajiya takeji sbd sanyin da jikinta ketayi ayau din daga wannan sai wannan.

Dakin farhat ta wuce kawai sbd acan zata samu nutsuwa yanzu kawai
Tana shiga ta nufi toilet tayo alwala ta fito daidai shigowan farhat Nan suka shirya sukai sallah tare daganan tacewa farhat baccin awa biyu zasuyi kafin la’asar
Nan suka kwanta.

MAMUH

KUYI MANAGE.

ZAFAFA BIYAR????????????

Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA
Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL
Dalaal–MISS XOXO
Mabudin zuciya–HAFSAT RANO
Ubayd Maleek–MAMUH GEE

DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

08085405215

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

0903 234 5899
[10/7, 9:09 PM] Xynerv Sadeeq Aderm????: Mamuhgee 31

YERWA INCENSE & MORE*
(The scents with diff essence for YOU& your HOME)

(MASARAUTAR KAMSHI)

Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa…

YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:

Khumra kowacce Iri.
Turarukan Wuta
Mopping khumrah
Washing khumrah
Bathing khumrah
body mist
kullaccam
scented hair cream/spray
wardrobe balls

carpet spray
air-fresheners
scented pebbles
body sprays
oil perfumes
Perfumes

kabbasa
burners
coal igniter
tong
kasko
english coal
dilke&halwa set
scented body mist

kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: @yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215 / 09044191709

suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai


Mr Omar ita yafara budewa kofar mota tashige kafin ya zagaya ya budewa MALEEK yashige shima ya zagaya yashige ya tada suka bar asibitin sbd fita irin wannan Mr Omar shine yakejan MALEEK hardai idan zasuyi sirrantacciyar magana sai basa fita da drivern maleek din.

Tafiya suke Babu me magana acikin motar sai numfashinta dake fita ahankali ahankali sbd nauyin da kirjinta yayi.

Dan dagowa yayi ya kalleta ahankali tareda ajiye wayar hannunsa ya maida kallonsa kan wani envelope daya bude da muryar me kamewa yace”

Today shud be the last time.

Ajiyar zuciya ta sauke me dumi kafin ta waiwayo ahankali ta kallesa da idanuwanta dake bayyanarda halinda zuciyarta ke ciki na tsananin tarin damuwa me nauyi sbd Jin guntun zancensa.

Batareda ya kalletaba Yana cigaba da karanta takardar yace”

You deserve it.

Wannan karon cikowa idanuwanta sukai da hawayenda batasan lokacinda suka balle mataba dama kukan take buqata kozataji saukin damuwarta.

Mr Omar guri yasamu gefen hanya Mara mutane sosai da hayaniya yayi parking tareda budewa ya fita ya rufo musu kofar yana matsawa daga gurin.

Ahankali shehekar kukanta yafara fita sbd takasa daurewa kuka takeson yi.

Shiru yayi tareda dungurar da takardar sbd gabaki daya baya gane me yake karantawa ya lumshe ido ya bude ya juyo ya kalleta
Kuka takeyi hawayenta na gudu akan fuskarta ya zuba Mata idanuwansa gaba daya akaro na farko dabaisan mezaiceba.

Zaro tissue yayi ahankali ya miqa Mata cikin muryarsa me kamewa da dadin sauti yace”

Idan kinsan bazaki iya daukaba Meyasa kikaje?.
Wayace kije asibitin tun farko?

Kasa kallonsa tayi sai hawayenta dake qara gudu takasa bude bakinta.

Dauke kansa yayi Yana zaro wani Tissue din yakuma Bata ta karba tana goge hawayenta dasukaqi tsayawa
Ahankali yace”

Daga yau idan ba school ba karkije koina.

Da sauri wannan karon ta dago ta kallesa shima ita ya kalla cikin ido ya daga gira daya alamar yes abinda kikaji nace.

Wani irin mutuwar jikine kallonsa ya sakar Mata Wanda Kuma jikin nata ya nuna hakan sbd sakewa da hannunta me tissue yayi.
Dauke Kai yayi daga kallonta Dan kada sauyin dayaji daga nasa bangaren ya bayyana Kamar yanda nata ya bayyana.

Itama juyar da kanta tayi bayan ta Kuma kallonsa ya waiwayo ya kalleta saitaji Kuma kunyar kallon ta kamata ta sauke Kai tana share fuskarta.

Wayar Mr Omar yakira
Yana ganin Kiran yasan sungama ya dawo motar ya bude yashigo ya tada motar suka wuce.

Koda suka iso gida su afia sun Dade da dawowa
Koda Mr Omar ya budewa NURUn kofa ta fito maleek harya bude da kansa ya fito shiyasa kusan a jere suka shigo
Afia dake palon zaune ta dago tana kallonsu harsuka kawo maleek ya wuce Kai tsaye NURU kuwa Jin tayi nauyin afia ya kamata saidai itama Bata tsayaba sbd samun kanta tayi da rashin bawa afia wani bayanin komai tashige tana cewa”

Afia kundade da dawowa kenan.

Harta shige afia Bata iya waiwayawa ta kalletaba sbd kusan itama dai batasan tunanin mezatayiba
Itama yau dai komai ya kunce Mata daga mum dinta har dad din Kamar suna sauyawa.

Tubewa NURU tayi ta sauya Kaya zuwa free doguwar riga mara nauyi da tsayi tafada toilet tayo alwala tazo ta tayarda sallah.

Tana gamawa ta fito hankalinta kwance sbd tasamu nutsuwa ba laifi Wanda takega kila sbd tasamu tayi kukan ne.

Kitchen ta nufa ta dauko ledar crispy patato chips daya ta bude tun daga can tafara ci harta iso Palo tazauna gefen farhat da duk ta tsorata da rigimar dazu tsoron lailah yasak shigarta tana cewa”

Sweetie inzo mu kalla pj masks cartoon ko.

Kwantawa jikinta farhat tayi tana cewa”

Aunt next time idan mum LAILAH tazo daddy idan zai tafi dake kuje Dani tayita yiwa afia fada afia nata kuka inajin tsoro.

Murmushi kawai NURU tayi tana cewa”

Kidaina Jin tsoro tana sonki bazatayi Miki komaiba mum dinki ce.

Kallonsu suka fara suna zaune mum Sarah tazo zata haye samansa tana tura wringer wheel mop bucket jekadi data fito kitchen takira NURU tana waiwayowa da ido ta nuna Mata mum Sarah ta juya ta kalla mum Sarah din taga abinda yake hannunta ta sauke ajiyar zuciya ahankali tareda Miqewa tsaye tana miqawa farhat ledar crispy ‘dinda sukeci tace”

Ina zuwa sweetie.

Gurin mum Sarah ta nufa Kai tsaye tace”

Mum Sarah kawo Bari natayaki kije kawai.

Kallonta mum Sarah tayi sbd wannan shine aikinta agidan tsawon shekaru Babu Wanda aka yarda dashi akan gyaran sama sai ita ko yanzu taso cewa NURUn tabarshi Amma ganin yanzu ita Matar maleek din ce saita miqa Mata tana cewa”

Thank you” ta juya Takoma kitchen.

Afia dake zaune palon tana jinsu saita waiwayo tareda tasowa tana cewa”

Muje na tayaki sbd aikin de yawa karki gaji.

Dan wani kallo NURUn tayiwa afia na mamaki da fara shakku akan afia sbd zuciyarta na Bata kaman afia batason kusancinta da dad din sbd mum dinta idan ta tuna yanda Afia din taqi jinin a danganta dad dinta da auren wata mace ba mum dinsu ba ta sake dubanta tana cewa”

Wannan aikin bazaisa na gajiba Amma dai tunda Zaki Taya din muje.

Saman suka hau suka tsaya a palon farko NURU batareda ta kalli kofar dakin lailah ba tace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button