UBAYD MALEEK COMPLETE

Kamar ko yaushe ita tafara gamawa Amma sbd afia Bata gamaba Bata miqe ba Dan ganin kamar rashin girmamawa ne wa afian datake kamar shugabarta na matsayi.
Saida afia tagama suka miqe dukkaninsu sukai daki afia dakinta ta wuce ita Kuma NURU farhat ta raka dakinta ta sauyo Kayan bacci takaita tayo brush suka dawo dakinsu ta kwantar da ita gefen afia kan gado kafin itama tadawo kujera ta kwanta tana rufe idanuwanta sbd afia tuni tafara bacci Dan agajiye suke.
Washe gari dad dinsu zai dawo Dan haka gidan a natse yake anata gyara da girkin ire iren abincin da akasan su yakeci Dan shi mutum ne da bai cika cin abinci me maiqo ba ma’ana soyayyan Abu bai damesaba kodai dafaffe ko Wanda aka gasa.
Cikin farin ciki farhat take da dawowan dadynta hakama afian Dan haka da wuri tadawo school yau sbd tasan tareda dad din zasuci lunch Dan baya tafiyan dare yawanci da wuri yake dawowa idan yayi tafiya musamman irin wannan daya Dade.
Qarfe biyu da rabi da mintuna hudu jirginsa ya sauka suna zaune a babban Palo suna kallon wani film da NURU afia ce ke fassara Mata me suke cewa tana gyada Kai ahankali sbd kallonma kaman na dolene takeyi afiance ta sakata zaman dole Amma ita tafi Jin dadin zaman daki.
Sunajin diran motan isowanshi da sauri suka miqe farhat da gudu tayi kansa tana Kiran sunansa tana Isa yayi sama da ita Yana sake Mata wani irin murmushin daya kusa sumar da NURU data Dan waiwayo setin qofar idanuwanta suka sauka kanshi da sauri ta dauke kanta daga gurin tana sauke Kai tayi saurin miqewa tana barin palon tsoro na mamaye zuciyarta Dan tabbas laifine yiwa jinin sarautar delah kallon quri bareshi dayake maleek guda na delah gizah Dan haka hanyar daki ta Kama har qafafunta na Dan hardewa sbd tsoron kallon datai Masa Wanda takasa gane laifin ne ya tsoratata kokuwa.
Tana shiga daki toilet ta wuce tana shigewa ta rufo.
Afia ma riqo hannunsa tayi tareda dorawa a goshinta tace”
Dehina metahi ya abal(barka/sannu da dawowa mahaifina)
Kallonta yayi da fararen idanuwansa masu maiqo aciki wani boyayyan annurin ganinta cikin nutsuwa data samu na bayyanuwa cikin ransa ya bude Baki cikin muryarsa me Dadi da sirkin mulki da iko na Koda yaushe yace”
Da akwai wani sirrin wannan boyayyan farin cikin danake gani akan fuskan AFIA UBAYD MALEEK ne?
Wani murmushin farin ciki tasaki suna yowa cikin Palo tace”
Sirrin na farin cikin dawowan abal din afia ne.
Daddy bana dawowankane ba kawai AFIA tasamu best friend yanzu tana surutu da NURU acikin gidan Nan Amma daddy nidai NURU tawace sbd tanada girma irin na AFIA ne suke friends.
Kallon bakin farhat din yayi Yana sauketa cikin palon yace”
Hmmm farhat inaga you are the talkative anan.
Masu aikin gidan ne suka jero mum Sarah ce agaba suka rurrusana suna Masa barka da dawowa cikin tsananin girmamawa batareda kowannensu ya dago Kai ba ya daga musu Kai kawai suka juya suka bar palon Wanda idan ba aiki suka shigoba Babu me shigowa sai mum Sarah.
Har sama farhat tabishi ita Kuma afia ta ja luggage dinsa tabishi dasu iyakacinsu Palo qaida Babu me shiga master bedroom dinsa sai matarsa lailah Dan haka kosu ‘yayansa Basu taba shigaba bare Susan Yaya yake.
Suna saukowa daki afia ta nufa inda tasamu NURU zaune tana kallon window inda take hangen library din karatun su AFIA sai datazo Nan takejin tabbas Ashe ilimin boko me yawa yanada amfani tunda gashi yanxu acikinsu Takoma tamkar wani kurman dabba da magana saidai a kwatanta Mata sbd duhun rashin ilimin bokon.
Dafata AFIA tayi tana cewa”
NURU Baki zo kinyiwa dad barka da dawowaba gashi harya shige se yafito cikin abinci Kuma.
Waiwayowa tayi ta kalli afian tareda dauke kai tace”
Darajana bekai naje gabansa harna tsaya na gaishesa.
Murmushi kawai afia tayi tana nufar mirror tace”
NURU kinason dakusar da darajanki anan gidan meyasa haryanxu kinkasa sakin jiki damu ki kulamu da qaunarmu yanda muke jinki?
Farhat na Miki kallon ‘yar uwa Kamar ta jini Amma koyaushe kina Mata abubuwan dakesata tuna akwai banbanci me girma a tsakaninku,
Nayi iya duk yanda zanyi Nima ba nuna Miki irin qaunar damuke Miki mundaukeki ‘yar uwa Amma Sam kinkasa sakewa Dani Nima meyasa?
Ko bakyajin dadin zama damu ne?
Rayuwanmu be Miki bane?
Tsoro NURU taji na shigarta na maganganun afia din ta juyo ta kalleta tana girgiza Kai tace”
Wlh ko daya Babu wannan sabo ne kawai matsalata inada wuyan sabawa da waje Amma wlh inajin farhat kaman meryam Babu wani abu dabaiminba anan hasalima wani irin girmane kukedashi aguna Wanda yasa bazan iya sakewaba sbd tamkar rashin girmamawa ne.
Ahankali Afia ta dawo takama hannunta tana cewa”
Karna sakejin wannan zoki rakani gurin karatu daganan zanfara koya Miki turanci.
Binta tayi zuwa libry dinsu dakeda wani irin girma da tsari da kyau ga littafai ko wani shagon Saida shagon littafan albarka.
Zama sukayi akan wasu kujeru masu kyau da taushi AFIA ta dauko wani littafi tana ajiyewa gaban NURU tace”
Kiyi kallon zanen dake cikin wannan littafin kafin nagama karanta wani abu cikin wannan littafin na hannuna idan nagama zanfara koya miki.
Karba tayi boyayyan murmushi na bayyana kan fuskarta Jin Wai tayi kallon Zane tsabar toshewar kanta kenan kaman wata yarinya kamansu meryam.
Budewa tafarayi tana kallo aikuwa zanen ne aciki na dabbobi da sunayensu irin su biri,doki,Kare,mage,zomo hardasu bera abin saiyaso Bata dariya ta murmusa harsaida haqoranta suka bayyana AFIA na lure da ita itama sai yanayin NURUn yasata boyayyar dariya.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR????????????
Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA
Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL
Dalaal–MISS XOXO
Mabudin zuciya–HAFSAT RANO
Ubayd Maleek–MAMUH GEE
DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
08085405215
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
[10/7, 9:09 PM] Mamuhgee 9
Sun Dade a can Saida afia taduba agogo taga lokacin fitowan dad dinsu yayi yasata aje karatun tana kallon NURU data dage tana kallon dabbobin duniya wainda wasu batama taba sanin akwaiba bare ganinsu sai take kallon abin cikeda mamaki da burgewa fuskarta ma ta nuna hakan
Afia ta dafa littafin tana cewa”
Ma’am Muje saikuma gobe mudawo ki Dora daga inda Kika tsaya.
Murmushi NURU tasake tana cewa”
Inason sanin sunayensu duka.
Karki damu ko farhat zata koya wannan yanxu dai muje inajin yunwa.
Fitowa sukayi NURU nasake wanyewa da qaton gidan sbd saiyau tun zuwanta ta fito ta zagaya cikinsa AFIA kuwa sai sake Mata bayanin komai takeyi tana nunnuna Mata.
Suna shigowa MALEEK UBAYD na gab da shigewa dining room tareda farhat dake gefensa cikin sauri AFIA tace”
Dad NURU na gaidasheka.
Jin haka yasa NURU saurin durqusawa muryarta na rawa tace”
Barka da fitowa cikin yarensu sbd a rikice take batasanma wane kalar yare shi yakejiba ko yake amfani dashi.
Batareda ya juyoba ko ya tsaya ya daga Kai tareda qarasa shigewa yana fiddo hannuwansa dake zube cikin alhijun qananan kayan dake jikinsa na Stuart weitzman dark blue dasuka fiddo hasken fatarsa da asalinsa.