UBAYD MALEEK COMPLETE

Uncle Imran yaushe kadawo?
MALEEK ya kalla cikin shiga nutsuwa da wani irin kwaijininsa daya cika idanuwansa yace”
Barka da yamma MALEEK.
Zama yayi a kujeransa da Babu me zama Yana amsawa ahankali tareda miqa Masa hannu ya miqo Masa takardun dasukai maganar zai kawo Masa gida.
Karban file din yayi tareda dakatawa daga budewa ya saurara sbd Jin wani qamshi dake fita kadan kadan daga file dinne kokuwa daga jikinsa?
MAMUH
ZAFAFA BIYAR????????????
Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA
Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL
Dalaal–MISS XOXO
Mabudin zuciya–HAFSAT RANO
Ubayd Maleek–MAMUH GEE
DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
08085405215
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
[10/7, 9:09 PM] MG 10
File din hannunsa yasake rufewa ya dan kalli bayan file din tareda yamutsa fuska ahankali cikin yanayi na kamshin zai damesa ya bude Kai tsaye yayi signing inda zaiyi ya rufe tareda miqawa Imran din batareda yace komai ba cikin girmamawa Imran ya karba Yana sake Masa bayanin sauran paparworks din dasuke pending.
Sauraronsa kawai yakeyi idanuwansa akan makekiyar TVn data kusa cike Rabin bangon palon Yana Jin dukkanin abinda Imran din yake bayani akai saidai kaman hankalinsa nason kasuwa gida biyu Dan zuwa yanzu Kam yafara tunanin sauyin qamshin dayake shaqa a hancinsa daga inda yake zaune ne kokuma daga kayan jikinsa Dan yanzu ya tabbata ba file din daya miqawa Imran bane wani abin ne dabam shidaima koma menene qamshin na damunsa sbd qamshin na kaman turaren matane sbd lailah ta taba amfani da irinsa…….
Cak ya tsaya da tunaninsa guri daya tunowa da kusan karon dasukai da mace a palon hakan na nufin suturar jikinsu ta hadu data juna Dan idan ba hakaba Babu yanda zaayi qamshin ya maqalu a kayan jikinsa.
Miqewa yayi yabar palon Yana dagawa Imran Kai alamar amsawa daga gaisuwan a huta lafiya maleek dayayi masa ya shige Palo na biyu yakamata hanyar hayewa samansa.
Daidai fitan dad din daidai shigowan Afia data baro daga dakinsu tana ganin Imran ta saki wani qayataccen murmushin farin ciki tana qarasowa ta zauna tana cewa”
Barr uncle Imran yaushe kashigo?shine ko atambayi Ina afia.
Kallonta yayi da milky idanuwansa Yana sake murmushin daya sata qara kallonsa tana sake kyakkyawar fuskarta cikin muryansa me class kaman Koda yaushe yace”
AFIA MALEEK kinyi saurin tambayane Amma kinsan bazanzo nafitaba batareda naganki ba Dan haka ma nemanki dole ne.
Hmmm that sounds like a bribe.
Dariya yaso saki ya daure Yana miqewa tsaye riqeda hannun farhat Yana cewa”
Ina sauri zantafi zan dawo zuwa weekend zamu fitama inshallah Amma dagani sai farhat.
Tsalle farhat ta buga tana murna da cewa”
Amma zamuje da my lewa?
Kallon tambaya yayi wa afia data tsuke fuska tace”
Don’t give me that look bazan fada maka wa take nufi ba tunda ku kadai zakuje kuje muma zamuje inda mukeda buqata.
Juyawa tayi zata tafiyanta yayo gurinta zai hanata tayi gaba da gudu tana cewa”
Kowa yaje da Wanda yakeso bazan fada ba.
Wata ‘kayataccitar dariya yabita dashi cikin ransa Yana cewa”
Naga wadda kike nufi kawai inason sanin wacece ita din.
Juyowa yayi gurin farhat tareda shafa kanta Yana cewa”
Sainazo weekend din ko Uncle’s princess.
Bayan tafiyansa zamanta tayi apalon tana kallon cartoon sama sama sukuma suna can daki NURU na kwance idanuwanta arufe baccin dole nason daukarta.
Har dare a kame take da kanta acikin daki hakanan idan abin yadawo Mata sai tsoro yasake shigarta sbd tasan da a delah ne hakan yafaru Allah ne kawai yasan hukuncin dazata fuskanta akan ko hada hanya da MALEEK bare kusan karo Wanda taji lokacinda jikinsu ya ‘dan shafu sbd itace me tudun qirji.
Afia taso fahimtan akwai wani abu atareda da sanyin NURUn Amma Kuma sanin halin NURUn na yau shiru gobe sakewa yasata sharewa Bata tsaya tambaya ba har sukai bacci.
Washe gari ma ko breakfast a kicin tayisa kafin suka wuce school tanaji afia na maganar dad dinta tafiya zaiyi yau itadai Bata iya cewa qala ba sbd duk lokacinda su afia da farhat suka dauko maganar dad dinsu Bata taba Koda kuskuren saka Baki ba sbd sanin matsayinta be Kai na saka Baki a zancensaba.
Weekend nayi Barr IMRAN JALALUDDEEN ‘dan babban yayan lailah dake qasar ta France shima wato babban tsohon chief minister na esthern ambassador Wanda bayan manyancinsa yakoma gida Amma shi ‘dansa IMRAN na zaune anan qasar haryanxu sbd anan yake karatu tareda aikin gamayyar wani sashen kamfanin MALEEK dake qasar yazo gidan da maraice cikin lafiyayyar motarsa white jaguar Yana sanye da designers qananun Kaya dark blue na Jimmy choo wainda suka fito da asalin kyawunsa na Dan Africa sai qamshin Mara hayaniya dayake fitarwa kallo daya afia tayi Masa kaman koyaushe data Saba tace”
Hmm Uncle u look great.
Murmushi yasaki Yana kallon NURU dake gefenta zaune kan kujera tana qoqarin hada wasu kalmomin English a iPad tana sanye da riga da wandon Palazzo me Fadi sosai rigarce kawai takeda shape itama Bata roba bace chiffon ce sai gashin kanta dake dunqule cikin Dan qaramin scarf da turkian gabaki daya hankalinta nakan abinda takeyi dan Monday zatayiwa malamarsu Mrs Edward presenting karatun shiyasa hankalinta baya kansu tunda ta Masa Ina wuni bayan shigowarsa.
Dauke kallonsa yayi daga kan NURU cikin basarwa yasaki wani boyayyan murmushi yana cewa idan sun shirya su taso suje a Kai farhat garden datakeson zuwa.
NURU bataso zuwa ba sbd karatun daya gama daddaure kanta da tunaninta Amma farhat ta takura akan ita da ita takeson aje dole badan tasoba tashiga ciki ta sauyo dankwalin kanta zuwa veil Mara datayi Rollin sai takalmi data sanyo loafers sabanin Afia datai ado bame yawaba itama kusan irin kayan NURU ne ajikinta suka fito suka wuce afian ce Agaba sai farhat da ita NURUn a baya wadda Sam ko kallon sosai bataiwa Imran ba bare ta lura da Yana Dan kallonta akai akai sbd gabaki daya ita bataso fitanba taso tsayawa tayi karatunta Dan yanzu data fara sanin kanshi da wayar karatun batada babban burin daya wuce samun ilimi me zurfi domin tsayuwa da kanta da iyayenta shiyasa yanzu kwata kwata batada lokacin batawa sbd karatu.
Duk wani yawo da tarin siyayyan da akayo a fitar basa kanta gida tamatsu su koma Dan haka harsuka gama yawon suka dawo bazatace ga takamaimai na kamannin Imran jalal ba Amma shikam yagama karanceta tsaf kaman yanda yake buqata musamman dayayi fira da farhat Sosai yagama fahimtar babban burin NURUn yanzu karatu ne sai hakan yasakashi farin ciki sbd dukkanin wannan na daya daga cikin abinda yake tsananin so ga irin matarda yake ra’ayi.
Ko kafin Monday karatunta tagama fahimatarsa sbd takuran data saka kanta ta saka afia Saida ta tayata bayani harta fahimta dakyau dakyau shiyasa Monday din harsuka je suka dawo cikin annashuwa take musamman data fara da samun yabo gurin Mrs Edward.
Imran jalal kuwa da zuciyarsa takasa hkr da rashin bawa kasa dama agurin NURU yasashi dawo da ziyarar daya Dade da daina kawowa gidan ahankali ahankali tun Bata wani bi takan sha’aninsa dasu afia harta fara sabawa dashin musamman akan karatun dayake dorata akai sosai Dan hakan sai sabo yashiga tsakaninsu duk da baitaba nuna wata alamar so atareda Shiba sbd yasan Basu Isa fara soyayyaba ayanzu tunda karatu ne agabansu sai sunshiga University Koda zasu fara bawa wata soyayya dama.