UBAYD MALEEK COMPLETE

Kayan bacci ne ajikinta qaramin guntun wando da rigarsa Mara hannu Dan haka saita sanyo doguwar kimono akai ta riqe gaban ta fito da sauri ta bude tana cewa”
Please stop ringing the bell Ina zuwa.
Tana budewa taga mr Omar ciki mamaki take kallonsa kafin tayi mgn ya dunguro Mata inhaler din cikin gaggawa yace”
MALEEK yasamu attack na asthma kiyi sauri ki Kai Masa idan yayi nisa ki shaqa Masa please go go go fast.
Karba tayi ta juya arude sbd ita duk Mr Omar dinne ya rudata ta yanda yake maganar dukkanin jikinsa na wani irin rawa ga tsoron shiga dakin na MALEEK Yana ciki Amma haka ta Isa arikice ta bude tashige qofar na rufewa shima Mr Omar Jan qofar yayi yakoma gefen qofar shiga palon ya dasa sabon zama.
Tana shiga yana qoqarin zubewa kwance batasan lokacinda ta qarasa da sauri ba cikin tsoro da rudewa ta tarosa dayake batada kauri sosai da qarfinda zata iya taresa musamman da jikinsa yariga yasaki sai takasa suka zube kan gadonsa gabaki daya.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR????????????
Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA
Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL
Dalaal–MISS XOXO
Mabudin zuciya–HAFSAT RANO
Ubayd Maleek–MAMUH GEE
DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
08085405215
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
[10/7, 9:09 PM]: MG 11
Sai magrib ta farka ta bude idanuwanta dasukai nauyi sosai tana kallon inda take ta lumshe idanu tana sake tabbatarda tabbas ta gaji matuqa gabaki daya rayuwarta yanzu hutu takeso Dan hakan zata sassautawa kanta tunda dai karatun yanzu yazaunu a kanta.
Tashi tayi zaune tana shafa wuyanta dayayi Mata sakayau sbd yanayin yanda tayi kwanciyar.
A kasale ta miqe tayi ciki tana duba qaton agogon dake bangon palon ta shige palon ciki ta doshi hanyar bedroom dinsu tashige.
Saidayi sallah kafin tayi wanka ta Sanya doguwar riga Mara nauyi black me dogon hannun Kuma har qasa take komaima Bata sanyo akantaba ta fito ta nufi dakin farhat tana Kiran sunanta.
Zaune take tana homework NURUn ta shigo taqaraso kusa da ita ta zauna farhat din ta haye cinyarta tana cewa”
My Lewa dubamin kigani yayi daidai kuwa?
Murmushi NURU tayi tana karba tafara dubawa tana cewa”
Ni danasan farhat Dina nada kokari Babu homework da bazata iyayi daidai ba Amma dai yanzu kinajiye muje kici abinci tukuna daga baya a qarasa lokacin cin abinci yayi.
Kwantawa tayi jikin NURUn tana cewa”
Ni yau banason cin abinci cupcakes and pancakes nakeso cin zakimin ai ko my Lewa?
Kumatunta taja tana sake gyara Mata kwanciya ajikinta cikin tsananin qaunar farhat din tace”
Yes of course sweetie duk abinda kikeso shi zakici.
Ahankali ta sake lafewa jikin NURUn tana cewa”
I love you my Aunt NURU.
I love you too baby.
Tashi sukai NURU na cewa”
Muje cikin yanzu bada dadewaba chief NURU zatayiwa princess pan and cup cakes dinta duka.
Kicin suka nufa cikin murna farhat ke taya NURU aikin da surutu sbd Babu kowa yanxu acikin gidan Dan dama da angama abincin yamma tun 7 na yamma kowanne me aiki na gidan ke barin shashen sukoma sashen masu aiki musamman idan MALEEK na Nan to ita yau batamasan MALEEK din yadawoba Yana gidan.
Saidata gama hada cake din tasaka a oven tafara gasa pancakes din lokacin tuni tacewa farhat taje dining ta zauna gatanan kawowa yanzu.
Cikin farin ciki takeyin aikin daga can cikin kicin din ta Dan dago muryarta me sanyin dadin sauraro tace”
Sweetie kinajin qamshin cake din Nan kuwa daga Nan inda kike sbd I just added your favorite inib yanzu akai inason kina fara cinsa kunnuwanki suyita tsalle Suna gudu sbd Dadi.
Dariya farhat tasaki tana toshe Baki idanuwanta akan fuskan dad dinta daya Dade da samunta a dining din Dan lokacin dinner dinsa yayi.
Ahankali ya dan kallin hanyar qofan dazaikaika kitchen din saikuma ya dauke Kai tareda saka spoon akan lafiyayyan abincin dake gabansa Wanda yanzu Fana tagama serving dinsa ta fice daga sashen gabaki daya.
Kasa kasa da murya farhat tace”
Daddy ai zakaci pancakes dina sbd cakes din aunt NURU are the best
Idan kaci wannan kullum zakaso ka qara kaji Kuma tasaka inib oh oh daddy na matsu akawo.
Dan kallon farhat din yayi da fararen idanuwansa Yana iya ganin farin ciki me tarin yawa da nutsuwar rayuwa gashinan bayyane ko Ina atareda farhat din Wanda hakan yasa yaji wata nutsuwa tashigesa tabbas yaransa deserve the best life,
Yaran MALEEK guda na delah gizah sun cancanci kowane irin farin ciki na duniya dai sbd sune keda matsayinda kusan yafi na kowa a gizah sbd mahaifinsu shine asalin maleek na kujerar sarautar delah gizah Amma rashin dacen uwa Kamar Laila yabarsu da qarewa tamkar marayu gashi shikuma schedules dinsa na rayuwa sun hanashi lokacin zama tareda yaransa.
Amma koma dai menene tunda sunsamu kulawa daga wannan din hakan yamasa Dan kuwa yaransa na cikin walwala da farin ciki Kamar Basu taba shiga damuwan kewan iyayeba musamman AFIA tasamu ‘yar uwar dataketa yiwa kanta mafarki da fatan asamu hakama farhat tasamu dukkanin soyayya da kulawan datafi buqata daga iyaye sbd qarancin shekarunta.
Dauke da kyakkyawan tray ta fito kitchen din ta nufo dining room tana
Cewa”
Sweetie are you ready??
Yessss “”farhat tafada da Dan qarfi cikin Jin Dadi da qaguwa.
Ok baby I’m coming ki tabbatarda yau kin rufe qofa da windows dinda kunnuwanki zasu gudu Dan kuwa yau hmmm.
Tana shigowa cikin dining room din tace”
Tadaaa…..cak ta dauke wuta ganin dadynsu farhat din a zaune da ‘dan guntun mamakinsu akan fuskanshi sbd su biyun kawai sun cika gidan da hayaniyar datafi ta mutum goma..
Rawa qafafunta suka dauka sbd tsananin tsoro da firgicin data shiga saura kadan tasaki tray din farhat ta karba da sauri tana cewa”
Zaki zubar muyi wahalan banza fa.
Batama San me farhat ke cewa ba gabaki daya ta rude ta tsorota batasan abinyi ba sai kawai ta durqusa cikin rawar murya tace”
Barka da dawowa da fitowa.
Tsit gurin yayi sbd kallo daya yayi Mata ya dauke Kai sbd kayan dake jikinta da kanta dake bude
Itakuma tunda yau ta ritsu Babu damar wucewa batareda izininsa ba Dan hakan ta sauke Kai durqushe agurin.
Farhat ce ganin shiru shiru dad din nacin abincinsa hankali kwance yasata sauka kan dining din tazo gaban NURU ta kamo hannunta tana janta tashi tace”
Lewa Daddy ya amsa gaisuwanki kitaso muci cakes din kibani abaki na matsu nafara ci.
Dan zare hannunta tayi daga na farhat din tana sake saukar da Kai qasa Dan bada tsananin girmamawa ga zaman maleek dake gurin.
Tissue ya dauka ya goge bakinsa tareda Miqewa cikin nutsuwa da kamewarsa ya bar gurin sbd yagama cin abincin dakuma hayaniyar dazata iya basa ciwon Kai tasu.
Yana barin gurin ta zube zaune gabaki daya tareda sauke ajiyar zuciya me sanyi tana dagowa ahankali ta dan saci kallon bayansa ta sauke Kai da sauri tana dawo da kallonta kan fuskar farhat dake Jan hannunta,
Kyakkyawan hancin farhat ta zubawa ido Wanda yake tsaf tsaf na dadynta ne ta debo ta gangara da idonta kan idanuwan farhat din take kirjinta ya buga da qarfi ta dauke idonta akai tana miqewa Kamar wadda kwai yafashewa aciki.