UBAYD MALEEK COMPLETE

Palo tadawo ta tsaya idanuwanta na cikowa da hawaye tarasa abinyi sai kawai ta zauna kan kujera tareda fashewa da kuka ahankali tana cewa”
Yaya zanyi Ni?
Mum Sarah ce da itama take cikin tashin hankalin tace”
Ki Kira IMRAN kifada Masa saiya Kira MALEEK yafada Masa.
Dago idanuwanta dasukai ja sbd kuka tayi ta kalli mum Sarah cikin sake shiga damuwa me qarfi tace”
Bayan afia Dana kasa samu IMRAN ne na biyun danayita Kira Amma shima wayarsa Bata zuwa.
Ki rubuta Masa text zaigani inshallah.
Hawayen cikin idanuwanta suka gangaro batareda ta damu da shafewaba ta daga wayarta tahau rubuta Masa massage tana turawa ta miqe jiki amatuqar sanyaye ta rurrufe ko Ina Takoma daki gurin farhat din.
Zama tayi bakin gadon tareda zubawa yarinyar idanuwanta dasukai luhu luhu sbd kukan tausayin farhat data zabge cikin yini daya sbd azabar ciwo.
Cikin kuka Mara sauti tace”
Farhat Allah yabaki lafiya
Bazan iya cigaba da ganinki hakaba.
Kuka takeyi sosai kafin daqyar ta iya miqewa ta rage kayan jikinta sbd zafin da dakin ya dauka yayi Mata yawa ita ta Sanya riga da wandon bacci qananu rigar Mara hannu ce sai wandon gajere ne iya cinya ta hau gadon tareda rungumo farhat ajikinta ta lullubesu bayan tayi musu addua har lokacin tsiyayar hawaye takeyi ahaka bacci ya dauketa tana qanqame da farhat din.
IMRAN lokacinda text din NURU yashigo wayarsa ya duba agogo qarfe dayan dare da minti arbain da uku sai hankalinsa yayi mummunan tashi sbd yasan ciwon farhat din zabura yayi ya miqe tsaye Amma Kuma bazai iya zuwa gidanba yanzu Amma Kuma tsoronsa idan har lokacin ciwon bai lafaba kumaba,
Numbern MALEEK ya lalubo a rikice ya Danna Masa Kira
Amma kaman yanda yayi tunani bai dagaba Kuma yasan ba dagawan zaiyiba sai kawai ya rubuta Masa massage cewan farhat na cikin mawuyacin hali tasamu attack na asthman datake dashi Yana turawa yakoma ya zauna Yana dafe kansa cikin rashin nutsuwa Dan yasan NURU ma nacan cikin mawuyacin halin damuwa da firgicin ganin farhat acikin halina ciwo.
Kwance yake idanuwansa ne kawai a rufe ba bacci yakeba sbd yanayin sanyi da ake yau me tsanani dashima yakeson Dan dago Masa da ciwonsa sai qaramin ciwon Kai dake damunsa na rashin bacci shiyasa yau ko fitowa baiyiba ruwan energy drink na powerhorse kawai yakesha sai yaga wayarsa na haske alamar shigowar Kira batareda ya dubaba ya share wayar Dan ba dauka zaiyiba.
Ganin anata Kira yasashi dauka Dan kashe wayar duka saiga text din Imran jalal yashigo bai budeba ta gaban lockscreen din yafara ganin abinda ke rubuce cikin massage din ya tashi zaune ahankali Yana qarasa karantawa ya ajiye wayar tareda Miqewa tsaye cikin nutsuwa ya sauko gadon tareda zura slippers din Berluti masu tsananin tsada da rashin nauyi yafito zuwa qasan sanye cikin sleep wears na prada black colour ya sauko direct bayan wasu shekaru yau ya nufi dakin farhat Kai tsaye.
Murda qofar dakin yayi ya tura wani dumi da qamshin English rosalle oud ya daki fuskansa zuwa cikin hancinsa ya sauke boyayyan numfashi ahankali sbd best mist dinsa kenan na daki ya shigo dakin tareda tura qofa sbd akwai Dan duhu a dakin cikin takunsa na nutsuwa da kamewa ya isa bakin gadon farhat din ya zauna tareda kallon ‘yar qaramar fuskarta data fada lokacin daya wani irin tausayin ‘yarsa da qaunarta me qarfi na ratsashi yakai hannunsa akan fuskarta ya shafa yanajin kaman yakasa amatsayinsa na mahaifi yakasa Basu rayuwarda suke buqata ta kulawan uwa da uba.
Bedside light ya kunna ‘dan haske ya bayyana yasake Kai hannu kan wuyanta zai taba yaji temperature dinta hannunsa ya sauka kan hannun NURU dake rungume da ita kaman zata maidata ciki sai alokacin ya lurada NURUn wadda gabaki daya jikinta ke bayyane farar fatarta dake tas wani irin qyalli takeyi musamman dogayen cinyoyinta dake wani haskawa afili ya dauke kansa Yana Dan yamutsa fuska ya zuwa fuskarta da idanuwanta suka bayyanarda kumburinsu na alaman kukan datasha sai sauke ajiyar zuciyar kukan datai takeyi akai akai cikin baccin ya gangaro da kallonsa kan irin rungumar dataiwa farhat cikeda qauna da alamun dake nuna Jin take kaman ciwon yadawo jikinta.
Ya rintse idanu Yana jinginar dakansa jikin kan gadon hannunsa har lokacin nakan nata batareda yatuna ya daukeba sbd tausayinsu duk su duka wato itada ‘yayansa daya shigesa.
Rufe idanuwansa yayi ahakan yanajin numfashin farhat me dumin zafi na sauka ajikinsa itakuma Kuma dumin zafin jikinta na zazzabin wuya daya fara shigarta na shiga ahankali nasa jikin ta hannunsu dasuka hadu.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR????????????
Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA
Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL
Dalaal–MISS XOXO
Mabudin zuciya–HAFSAT RANO
Ubayd Maleek–MAMUH GEE
DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
08085405215
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
[10/7, 9:09 PM] Mamuhgee 12
Qarfe shida da wasu mintuna ya bude idanuwansa dasukai nauyin baccin daya daukesa daga Nan jinginen kan gadon.
Tashi zaune yayi ahankali yana kallonsu sbd har lokacin bacci sukeyi sosai musamman da alamu ya nuna farhat din ta samu sauki sauki sbd numfashinta daya ‘dan daidaita.
Hannunsa dake sarqe cikin na NURU data qanqame ya kalla ahankali tareda dago manyan fararen idanuwansa da bacci ya Dan sauyasu ya zubawa fuskarta datake Kama data ‘yan babies kaman farhat dinsa saiya maida kallonsa kan farhat da itama innocent face dinta tayi haske ya saka dayan hannunsa yakama hannunta ya zare hannunsa Yana kallon fararen yatsun hannunta dasuke farare fes kaman Bata aikin komai dasu ya miqe yaja bargo ya rufe musu jikinsu musamman NURUn da cinyoyinta suka gama Shan sanyi duk da Babu wani sanyi ko kadan a dakin shiyasa ma shima baccin yadan daukesa.
Ficewa yayi dakin ya rufo musu qofa yayi samansa Dan yin sallah da yau yayi latti.
Bayan fitarsa ba jimawa NURU ta farka ta tashi jikinta amatuqar mace da Dan nauyin jiki da sauran ciwon kan dabai gama sakinta ba ta zauna tareda kallon farhat tana tabata tareda duddubata ta tabbatarda tasamu sauqin dannewan numfashin saitaji hankalinta yadan kwanta ta sauko gadon ta nufi toilet din dakin tashiga tayi duk abinda zatayi tazo alwala tana Kai ruwa bakinta zatayi shaqar hanci taji wani irin qamshi a tafin hannunta ta Kai hannun hancinta ta sake shaqa taji wani irin qamshi dayaso kashe Mata jiki Amma Kuma takasa tuna na menene tunda tasan last abinda ta taba kafin baccin was kayan baccin data Sanya ta kwanta.
Cigaba tayi da alwalarta tagama tafito Takoma dakinsu acan tayi sallar tana idarwa tadawo ta duba taga farhat Bata farkaba har lokacin bacci takeyi ta gyra Mata lullubinta tareda gyara Mata kanta Takoma daki ta cire kayan baccin ta Sanya dogon wando da rigar sanyi da hula ta nufi kicin Dan hadawa farhat din pancakes da tea din sabuwar Madara datasan farhat na tsananin so ko zata samu taci Dan duk jiyan bata iyacin komaiba sbd tsanani da azabar ciwo.