NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

08085405215

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

0903 234 5899Mamuhgee 13
Las Vegas
Sabuwar rayuwarsa NURU Bata taba koda mafarkin samun yiba Koda kwatance itace take gudanarwa a Vegas sbd wani yalwataccen ‘yanci da gata datake samu ta bangare biyu wato Imran da Kuma su afia da mahaifinsu Wanda shine ya dauki nauyin komai nata sbd ‘yayansa.
Wata irin tsadaddiyar rayuwa takeyi a Vegas acikin lafiyayyan qaramin flat din maleek dake cikin wani babban building na masu Vegas da kanta.

2 bedrooms ne manya sosai agidan kowanne da toilet dinsa shima babba sai Palo ‘daya da kitchen sai dining area shikenan,
Komai na gidan farine sai Yan abubuwa qalilan daba farare ba Dan kasancewar gidan Dan kuf kuf yasa bayada wani kadaici ko tsoron zama Kai daya saidai uban zallar dukiya da aka narka gurin gyaran gidan.

Tunda tazo bus takebi Bata taba amfani da motar da aka Bari Dan fitarsuba Dan tuqinta bai wani gama riqewaba Amma dai tsarin tuqin ne anan Bata ra’ayi tafison idan Takoma gida.

A school tunda tafara zuwa Bata samu matsalar karatun da mutanen makarantarba ko daya Dan haka saita maida hankali kawai tana karatun saikuma gyara jiki da harkan fashion da sabuwar qawarta ‘yar Morocco take janta suna Dan fadawa ahankali ahankali.
Karatunta yayi nisa tagama gane kan farin Vegas Dan haka saita saje Takoma tamkar wata baturiyar qasar danma banbancin ita haryanxu kusan fiyeda Rabin suturarta sunanan jallabiyane saidai mafi yawanci na Turkish da Kuwait ne tafisonsu sbd mayafansu daurawa takeyi kaman scarf bata yafawa sai jeans da riguna masu har qasa Amma masu tsaga Suma da scarf take sanyasu sai handbags takarmanta Kuma mafi yawansu loafers ne masu tsada saidai Kuma yanxu tana Sanya heels musamman idan tasaka Kuwait gown.

Yau a gajiye tadawo gida tana waya da Afia taqarasa shiga cikin palon tareda rufo qofa ta wuce bedroom dinda yake nasu Dan dayan ko key dinsa Babu a gidan sbd ba’a shigarsa shiyasa ko bakin gurin qofar Bata taba zuwaba.

Ajiye Jakarta tayi tareda waya ta tube tafada toilet tayi wanka da ruwa me zafi Sosai jikinta ya saki ta fito tanajin wata irin yunwa Kuma.
Neutrogena oil kawai tashafa ajikinta sai body mist ta Sanya straight English riga Mara nauyi wadda ta zaune daidai fadin jikinta daga sama har qasa ta Sanya qaramar hula bayan tayi sallolinda bataiba tana gamawa ta miqe tareda zaran wayarta ta fito Palo ta aje wayar kan kujera ta nufi fridge Dan dauko drink da biscuits koshi tafara ci kafin ta Dan dafa ko noodles taci Dan batada qarfi ko kadan tana buqatan qarfin dahuwar noodles din Dan tun safe bataci komaiba.

A kujera tazo ta zauna tareda daukan remote ta kunna tv ta Nemo tashar cwtv Ana wani American series the arrow.
Tana fara ci tagyara zama kenan taji doorbell din yayi ringing ta fara kallon agogo kafin ta kalla qofar ta ajiye cup din hannunta tareda Miqewa ta nufi qofar tana tauna sauran biscuit din dake bakinta ta bude qofar Kai tsaye.

Mr Omar ne a tsaye riqeda wata qaramar brief case da wata luggage qarama
Cikeda mamaki ta saki murmushin farin cikin ganinsa Dan bayan Imran Babu Wanda yataba kawo Mata ziyara daga gida cikin muryarta me Dadi da sakewa tace”

Mr Omar you…….Bata qarasaba qamshin da zuwa yanzu tagama sani da tabbarwa Kona wanene taji ya doshi hancinta Yana shiga take ta hadiye sauran maganar tana kallon bayan Mr Omar.

MALEEK ne sanye cikin Louis Vuitton suits dark blue as usual,
Sai waya dake kunnensa Wanda alamu ya nuna da mahaifiyarsa yake mgn sbd yare dayakeyi Wanda sautin muryarsa daya kusa sumar da ita sbd tsoro da nutsuwar dake cikin muryar tareda wata irin kamewa Dan yaune Rana ta farko datake Jin muryarsa Kai tsaye Yana magana.

Daburcewa tayi tareda tsorata tashiga hankalinta sosai tareda rabewa gefe tana kame jikinta musamman kayan dake jikinta hakama kanta duk rabi a bayyane.
Mr Omar yariga yasan wacece ita ma’ana matsayinta na negestatin MALEEK Dan haka ko gangancin dagowa yayi Mata ko kallo daya baiyiba Dan sanin babban laifin aikata hakan musamman a irin yanayin datake damashi ko acan gida baya iya dagowa ya kalleta sbd sanin laifine hakan su sauran tunda Basu saniba nasu me sauqine.

Kai tsaye MALEEK yashigo har lokacin waya yakeyi Dan haka ko lura da ita baiyiba bare yaji gaisuwarta ya wuce ciki Kai tsaye har lokacin itadai kanta na qasa kirjinta na dokawa da qarfi qarfi
Mr Omar ne yamiqa Mata waya batareda ya kalletaba kansa a qasa Yana cewa”

Jekadi ce akan wayar.

Karba tayi jikinta amatuqar sanyaye ta Dora wayan a kunnenta tareda miqawa jekadi da gaisuwar”

Barka da yau jekadi.

Barkanki da yau Allah yaqara Miki lafiya da kyau da Nisan kwana NURULHUDA.

Tsit tayi tana sauraron jekadin sbd zuwa yanzu kusan tasaba da kirari da irin gaishe gaishen da jekadi ke Mata Wanda ta dauka hakan amatsayin ‘dan wani girma daya shafeta na ‘yayan MALEEK su AFIA datake taredasu musamman dayake itama da sunan ake Mata amfani a makaranta wanda da farko ko a makaranta aka Kira sunan tsoro kamata yakeyi hartazo tadan saba Amma duk da hakan har yau har gobe idan aka kirata da NURU MALEEK sai gabanta ya Fadi.

MALEEK yazo wani mahimman taron dare da zasuyi da wasu abokanan huldansa masu mahimmanci Dan haka kinsa Babu masu hidimarsa anan kece zakiji da komai musamman yanzu da dakinsa ke buqatan gyara kasancewan yadan Kwana biyu bai ziyarci farin ba Dan haka ki gyara komai atsarin yanda yakeson komai kada kiyi kuskure ki kiyaye.

Bakinta yayi nauyinda bazata iya magana ba saidai Kai kawai ta daga tareda miqawa Mr Omar wayarsa ta juya ya biyota abaya ya ajiye kayan hannunsa ya juya ya fice bayan yace Mata idan MALEEK ya nemesa Yana can qasa a mota ya ciro key card na bude master bedroom din maleek yaja qofar ya fice.

MALEEK na balcony din dayake fes fes tsare dawasu lallausan kujeru guda biyu da table a tsakiya sai glass door din dayake Hana iska shigowa ya damesu kullum acan take karatu itama Dan haka gurin agidan ma kaman yafi samun gyara sbd ko Imran yazo anan suke fira harya tafi nada gidan.

Ganin Yana can ta dauki jakukunanda mr Omar ya ajiye ta nufi dakin da sai yanxu ta fahimci nasa ne ta Dora card din budewa akan qofar dakin ta bude.

Ahankali ta tura zuciyarta da qafafunta tareda hannuwanta Babu Wanda baya rawa sbd daburcen datake.
Girman dakin da makeken royal bed din dake ciki me wata irin transparent labule fari tas data zagaye gadon tayanda bazaka baccinsa ba saidai inuwarsa idan Yana ciki.

Mirror dinsa tamaida ido akai girmansa yasata juyowa gaba daya tana kallon kanta aciki ta yanda take firgice.
Komai na dakin fari ne shima Kuma komai tsaf tsaf yake ba wata qura sbd ba gurin shigowarta kamar dai akwai mutum aciki kullum.
Qamshinsa ne dai wadda tafara haddacewa sbd tsoro shine yake tashi takowane lungu da saqo na dakin.

Cikin sauri da gaggawa tahau aikin daya shigo da ita take ta gyare komai tsaf tareda wanke toilet ta goge ta kunna AC da turaren daki dake fita ahankali sbd Bata budeshi duka ba kadan ta bude ta yanda kamshin zaifi bada nutsuwa sbd kadan kadan yake fita Kuma saiya Jima kafin ya feso kadan din.
Gadonsa ne kawai batayi gangancin ko tabawa ba sbd sanin hukuncin laifin hakan Dan ko yau da a delah ne ko gizah Allah ne kawai yasani idan zataga safiyar gobe sbd mugun babban laifine ganin makwancin asalin jinin DELAH bare MALEEK guda matuqar ba negestatinsu ba ko matayensu Suma sbd sune abokanan kwanciyar tasu Dan haka kallo daya tayiwa gefen gadon Bata kumaba harta gama ta fice dakin zuciyarta na sake shiga rudu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button