UBAYD MALEEK COMPLETE

Mai bukatan Kaya should chat:08062991549
Call:08064532391
To plc ur order
Munada komai available now so hurry nd grb urs before you hear sold out????
Karkubari abarku abaya ko abaku lbr domin kynm yanagyara ko fatan d Mai yabata komutum bashida komai zai iya using kayan zaisa jikin k yafidda wn kyau medaukan hnkl duk inda kikayi se ankalla,show ur skin some luv domin mata da gyara akasanmu????just gv it a try nd ur skin will definitely/forever thank you❤️
Mn Kaya kowani gari buh delivery is not free????
Team glow????♀️
Sunfara karatunsu hankali kwance saidai NURU da hidima takeson Mata yawa yanxu Dan karatun nasu duk me zafi ne Amma ita ga hidimar kula da farhat da lalurorinta gakuma na gidan Dan yanxu tasaba sosai take saka hannu a aikin kigan musamman ma abinci sbd ko su afia da farhat sunfi Jin dadin cin nata hakama dad dinsu duk da kaman canke ne sukayi kaman yafi ci sosai idan tayi din saiya kasance kobatayi kullum idan Yana gari ita keyi.
Ta bangaren Imran jalal kuwa yanzu soyayya suke gudanarwa afili cikin kwanciyar hankali musamman yanzu daya tabbatarda yagama dasa soyayyarsa a zuciyarta Dan haka yake biyeda ita kaman jela Dan kusan koyaushe Yana gurin daukota daga makaranta kokuma Yana gidan firar yamma,
Yan gidan kaf yanzu kowa yasan menene a tsakaninsa da NURU musamman daya fara kawo Mata maganar aure Dan shi Sam Jin yake kaman soyayyarsu na buqatan kiyayewan tsaro bayason wasa wani Abu ya gitta so yake kawai suyi aure tazama tashi daganan ne kawai zaijisa hankali kwance shiyasa ya takura Mata da maganar auren.
Juyowa yayi daga tuqin dayake ya ‘dan kalleta da fararen idanuwansa cikin sauti me bayyanarda Sonta dake mamaye dashi yace”
Beauty yau MALEEK zai Paris gobe da safe zanshigo zamuyi maganar wasu takardun contract dinmu idan mungama zanmasa maganar zuwa neman aurenki gaskia bazan iya cigaba da jira ba is high time ace komai namu yazama dahir ma’ana samun tabbacin zamowanki matata shine agabana komai baya gabana yanzu kamar wannan.
Tunda yayi maganar zai fadawa MALEEK zancen neman aurenta gabanta yayi mummunan faduwa ta dago da sauri ta zuba Masa manyan fararen idanuwanta tareda fadawa cikin tunani me qarfi da firgici.
Wane irin sarkakiya rayuwarta take cikine?
Menene matsayar rayuwarta gabaki daya yanzu sbd batasan menene sunan dazata alaqanta kanta dashiba adaidai yanzu.
Har suka Isa gida batasaniba sbd tunani da tsoro me qarfi da zancen Imran din ya tado Mata.
Kiran sunanta yayi Yana kallonta gabaki daya sbd tayi nisa a tunani batasan sunfi mintuna biyar zuwa shida da isowa gidanba.
Sake Kiran sunanta yayi Yana cewa”
Are you ok?
Waiwayowa tayi dukkanin jikinta a matuqar sanyaye ta kallesa ta gyada Masa Kai batareda ta iya bude Baki tayi maganaba
Zai sake mgna ta bude kofar motar ta fice daukeda handbag dinta da wayarta a hannu.
Bin bayanta yayi da kallo cikin ‘yar damuwar sauyawarta atake cikin motar.
Baishigoba sbd a yanda take dinnan bazai samu damar ta kulashiba yanda yakamata sai kawai ya tada motar ya juya ya fice daga gate din gidan ya wuce.
A palon ciki ta tararda farhat na kallon cartoon ta taso da gudu ta fado jikinta tana Mata sannu da zuwa
Qaqalo murmushi tayi ta shafa kanta tana cewa”
Sweetie Aunt NURU batajin Dadi kanta na ciwo zanje na huta ko.
O o sorry aunt.
Gyada Kai tayi tareda sake shafa fuskan farhat din tana wucewa zuwa daki sbd AFIA Bata dawoba sai zuwa yamma.
Tana zuwa daki ta zube kan kujera tareda watsarda Jakarta da wayarta kan daya kujeran tana dafe goshinta tareda rintse ido tana.
Ta Jima ahakan cikin tunani me zurfi har wani wahalallen bacci ya dauketa Bata farkaba sai yamma da Afia tashigo.
Tashi zaune tayi kanta na tsananin sarawa ta miqe tsaye ta nufi closet ta tube ta shige toilet.
Wanka tayi tareda alwala ta fito ta shirya cikin doguwar Bahrain gown mara adon komai Mara nauyima kwata kwata,ta nada mayafi ta tada sallah.
Bayan tagama sallolinta miqewa tayi ta nufi kicin Dan aikin abincin dare sbd Imran yace yau dad dinsu afia zai dawo.
Acikin sanyi takeyin komai sbd rashin walwalar datake ciki na dawo da ita tunaninta da Imran yayi Dan kuwa Dole wata Rana duk cigaban rayuwar dazata samu saita dawo inda asalin rayuwarta take tsaye wato baiwa Kuma negestati.
Meyasa ta shagala hartaso manta wacece ita?
Ta Yaya zatai aure bayan batada wannan damar ko ikon,
Shin ita ayanzu ma menene matsayinta a masarautar delah?
Menene sunanta anan gidan? Yar aiki kokuwa me Reno kokuwa me debewa ‘yan gida kewa.
Tayaya Imran zai mallaketa amatsayin matarsa bayan ita din negestatin wani ce Wanda haryanzu batamasan ko wayeba.
Ta Yaya zata Bari Imran yayi maganar aurenta gurin maleek bayan tasan hakan bame yiyuwa bane.
Kammala komai tayi ta diba nata ta jera a tray ta fice daga kicin din tabarwa Fana ta jeresu a dining.
Koda taje daki ta aje abincin tafaraci tana amsawa afia firarta sama sama
Dataga ma ba iyacin abincin zatayiba saita shanye drink din kawai ta bar abincin.
bayan sallar magriba motar data dauko MALEEK daga airport tana shigowa gidan su Kuma lokacin sun gama sallolinsu suna zaune a Palo na biyu farhat na kwance jikinta tana kallon cartoon AFIA Kuma na gefensu itama riqeda wani hardcover t book tana karantawa ita Kuma NURUn tayi nisa sosai a tunanin abinda yake damunta hankalinta gabaki daya yabar jikinta zaune kawai take.
Karan doorbell yasa AFIA kallon farhat sbd sanin Babu masu aiki ko daya yanzu a part din lokacin shigewarsu yayi sun koma part din masu aiki saikuma gobe tace”
Farhat kije ki bude kofa I think Imran ne yazo yanzu.
Sunan Imran din da AFIA ta fada yasata dawowa hankalinta ta juya a hankali ta kalli afia murya a Sanyaye tace”
Kina magana ne?
Batareda ta juyoba hankalinta na kan littafin datake karatu ita afian tace”
Eh inaga Imran Yana bakin qofane doorbell Yana qara.
Kallon hanyar fita palon zuwa palon farko NURU tayi cikin nazari saidai Kuma dama tasan zaiyi wuya Imran din yaqi dawowa yau din sbd sauyin daya gani tattareda ita dakuma nacinsa akan maganar aurensu.
Zame farhat tayi daga jikinta tareda Miqewa tsaye ta nufi daki ta doro qaramin mayafin doguwar riga akan kayan jikinta ta fito ta nufi qofa ta budu Kai tsaye tareda bude Baki zatai mgnar idanuwanta suka sauka kan Mr Omar dake Danna doorbell din gabanta yayi mummunan faduwa ta saci kallon bayansa daidai isowar MALEEK din sai Imran a bayansa Wanda da gani shima isowarsa kenen mr Omar ya juya da sauri yabar gurin ganin MALEEK ya qaraso,
Take taji qafafunta na neman Gaza daukarta tayi saurin kaucewa daga bakin qofar tana sauke kanta sbd wani irin kwarjini da cika Mata idanuwa dayayi saikuma shedan dake dawo Mata da tunanin abinda yafaru dasu a Vegas sai kunyar al’amarin na bayyanuwa atareda ita Wanda yasata dagowa ahankali ta sake kallonsa daidai kawowarsa daf da ita idanuwanta suka hadu da nasa idanuwan dasuka kusa sata zubewa agurin batasan lokacinda ta bude bakiba da siririyar muryarta tace”
Barka da dawowa.
Akaron farko daya bude Baki ya amsa Mata da”
Yawwa.
Gabaki daya Jin tayi tana neman rikicewa har batasan lokacinda ta rufe qofa da qarfiba Wanda ta daki hancin Imran daya fara shigowaba da qarfi har baisan sanda ya saki qara me qarfiba wadda tasata dawowa hayyacinta da sauri ta bude qofar cikin damuwa da kulawa tayi kansa tana cewa”